Ouummey 054
Page 5️⃣4️⃣
_______________________Jiya muka sauka a Nigeria, mun baro mutanen Ethiopia cike da kewa da begen juna, Dr Bee'at kuwa mun sha kuka ni da ita kamar ba za'a sake haduwa ba washegarin zuwan su Hajiya Yayah na kira ta na sanar mata da komai, se kuwa gata har da Maman ta, muka bar su tare su manyan bayan ta gaishe su, mu kuma muka kule daka ni da ita da Aunty Luba, Aunty Luba ce ta sake maimaita mata labarin mu har zuwa jiya, se gashi kamar an dade da juna, ita da Aunty Luba kamar da ma can sun saba, sune har da musayen number waya.
Lokacin da muka fito dan raka ni makarantar islamiyya in musu sallama ne su kuma mazan suka shigo, suma duk suka gaisa ina introducing din ta, itama ina fada mata wannan ne Ya wane, har aka zo kan Ya Ahmad, irin kallon da yake bin Dr yasa ni da Aunty Luba kallon juna cikin mamaki dan Ya Ahmad ba ruwan sa da mata, ko aiki be fiya so ya hada shi da mace ba, se gashi ya shagala da kallon Dr har ma be iya jin gaisuwar da ta masa ba se da na maimaita masa, cikin borin kunya ya amsa tare da wucewa da sauri, se hakan ya bamu dariya muka shiga kyakyatawa kuwa.
Ko bayan mun dawo daga islamiyya an zauna cik abincin rana haka ya dinga satar kallon ta har se da itama ta gane, se gashi an koma yar satar kallon juna, mu dai muna daga gefe ni da Aunty Luba muna kallon ikon Allah.
Cikin hukuncin Ubangiji a ranar da zamu taho Ya Ahmad yayi proposing soyayyar sa wa Dr, bata wani ja ba tayi accepting, aikuwa ba karamin faranta min hakan yayi ba, babu wanda ya kai ni murna dan Ya Ahmad na auro ta shikenan mun sake hadewa abin mu.
A gidan Hajiya Yayah na sauka haka ma Mama, nan suka sake neman yafiya ta har abin na bani kunya, basu dena ba se da na fashe musu da kuka ina tabbatar musu su iyaye ne gare ni Ni ban rike su ba.
Gida na daban Ya Masdooq yasa aka gyara min a cikin gidajen sa, dake tun ainahi he's not the polygamous type, duka gidajen sa tsarin zaman mace daye ne da su, se gashi Allah ya jarrabe shi da auren mata biyu.
Tun kan muzo gidan an gama gyarawa amma dai Hajiya Yayah tace na sauka gidan ta na kara hutawa kafin na shiga.
Washegarin dawowar mu ni da Aunty Luba tazo muka tafi wajen gyaran jiki, gyara ne aka min me suna gyara in and out duk da cewa ina gyara na a can amma wannan daban ne, a wuni guda se gashi na canja matuka, hatta gashi na da bana wasa da gyara shi yau gyaran da yasha na daban ne, kamshi kuwa kamar an ciro ni daga cikin turare, kayan gyaran jiki tun ina can Nene ta dinga bani, a lokacin ban gane ba cewa take dauri ne saboda yara na, se da dazu kafin fitowar mu Hajiya Yayah ta min hadin gumba sannan na gane wato Nene rufe ni tai baibai, amma ko ba komai dai na gode.
Aunty Luba tace ta aje min wasu amma ba yanzu ba , tafi so in zan yi amfani da su ya zama su kadai ne zan yi dan in gane ingancin su da kyan su, k da muka koma gida Hajiya Yayah se yaba wa take, ita dai Mama bata magana se murmushi da bina da kallo, duk wani shiri da ya kamata ayi an yi, kaya na na hade waje daya tsaf, har na gidan Mama Aunty Luba taje sun hado min ita da mama ladi, sun kuma kai gidana sun jera min, Baba uba nagari me so da kauna ta shi yayi min kayan daki, tun daga kan furnitures har zuwa kan kujeru, kayan gado set uku adadin bedrooms dake gidan, daya a kasa biyu a sama se falo biyu, sama da kasa, se kuma kitchen din girki dake kasa da kuma mini kitchen da ba'a girki a sama.
Komai da aka zuba a gidan nan unique ne, sam babu gama garin kaya, duk da ban je na gani ba amma a hoto kadai da Aunty Luba ta nuna min se da na kasa cewa komai.
Ado blue-black aka yi da milk, karshen haduwa gidan ya hadu, abin da ya kara dadada min har da garden da nake masifar so, kai gida fa yayi iya yi.
Ranar da zamu tare ni da shi kadai muka tafi ban da yara, Hajiya Yayah tace mu bar su a wajen su tukuna suma su saba da su, bayan mun sha nasiha me ratsa jini da jiki a wajen Baba da Hajiya Yayah, Mama kam albarka kadai ta saka mana, muka shiga gidan mu bisa rakiyar yayye na gaba daya da yar uwa daya tamkar da dubu Aunty Luba, godiya kam har na rasa kalar wadda xan mata dan ita tayi tsaye kan duk wani abu da za'a siya a sa min a gidan, da kuma tsarin da aka yi jeren, bata zauna ba se da ta ga komai da komai yayi yadda ya kamata.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
Genel KurguSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...