PAGE THIRTY SIX

497 27 10
                                    

Ouummey 036

Page 3️⃣6️⃣

___________________ciwo ne da tun da uwata ya haife ni ban taba jin irin shi ba, ga wani irin ruwa da yake bin jiki na wanda na fara ganin shi tun shekaranjiya, sedai ban bashi wani muhimmanci ba, ji nake kamar zan mutu, ga ba mataimaki a kusa, nishi kawai nake cikin zafin ciwo, idanu na a warwaje saboda azaba.

****Aunty Luba***

Yau da farin ciki ta tashi, jiya da dare ta samu tayi convincing Ya Salman, da kuka da magiya da komai kafin ya amince mata taje gidan Aimah, ya fada mata Yes ya san sun yi kuskure sedai kunya fa nauyin Aimah yake ji shiyasa suka kasa neman ta all this while, amma taje, da daddare ze tattaro sauran duk su zo a zauna ayi magana su kuma nemi yafiyar ta komai ya wuce.

Da wannan farin cikin Aunty Luba ta kwana, ta kuma tabbatar wa Ya Salman dan kuwa ta shayar da shi soyayya me matukar tsayawa a rai.

Ko da ta gama shirya wa se ta dauko tsarabar da take son kaiwa Aimah, tsaraba ce ta kayan gyara, kayan kankara mutunci fa kima a idanun megida, kamar kowace mace Aunty Luba ma na siyan kayan mata, na kara niima da kuma na gyaran jiki, sedai ba kowane kara zube take siya ba, a waje ɗaya take yin siyayyar ta, wajen SURAYYA, shima dan ta yadda da ingancin komai ne, ta gwada ta samu kyakkyawan result shiyasa ta rike ta hannu bibbiyu.

Bata manta yadda aka yi ta santa, makociyar ta Maman Ilham ta haihu ta shiga yi mata Barka, a nan ta samu yan uwan Maman Ilham din, da ke sun san juna sosai aka gaggaisa aka shiga hira, a nan ne suka zo kan hirar kishiya, Aunty Salma yayar Maman Ilham na bada labarin kishiyar ta, ana ta raha se aka zo batun kayan mata da take amfani da su dan gyara da yasa me gidan ta har lokacin itama yake yayinta

"Ai Maman Mimi duk macen da ta zauna tsura yanzu ita taso, mazan nan namu na yanzu se da gyara wallahi, to kana gyaran ma ya ka cika balle ka zauna ka saki baki, shiyasa kin ganni nan bana sanya wajen kula da kai na, ba wai nace mata ku haukace ne wajen shaye shayen magungunan da baku san da me aka hada su ba, kuje ku dinga karbo abinda ze cutar fa lafiyar ku ba, no, komai akwai na gargajiya me kyau da da kan ki zaki duba ingredients din sa ki ga yadda aka hada shi wanda in kina so kema zaki iya yi da kan ki sedai dan wasu abubuwan da zasu yi wuyar samuwa, atoh kin ganni nan nan tikee fruits hannu bibbiyu haka kuma kayan wajen SURAYYA, shiyasa wani wulakancin ko an so kawo maka shi dole a fasa".

Aunty Luba ta gyada kai tace

"Haka ne Aunty Salma, Ni ina taso in samu wajen siyan ire iren kayan gyaran nan duk da nima ina amfani da fruit daily, sedai tsoron irin hannun da zaka fada ya hana ni wallahi".

Aunty Salma ta gyara zama

"To kuwa ki kwantar da hankalin ki, i recommend SURAYYA HALIN YAU for you, in dai kayan gyara sadidan kike nema kin samu, tana dafa kazar amarya, Saiwowin dahuwar kaza, Saiwowin sanyi daga Chad, Saiwowin tsumi, Saiwowin matsi maganin niima, Original gadalin mata, Ƴaƴan gadali na asali, Original gumba, Tsumin Saiwowi, Tsumin kwakwa da Dabino, Igiyar alkairi, Zumar goran tula, Hakkin daka na musamman na asali, da sauransu duka zaki samu a wajen ta, kayan ta masu inganci ne, babu cutar wa ko kadan a cikin su and at very affordable price, ga number ta, 08032773332 chat her up ko ki kira ta, Allah Maman Mimi se kin gode min daga baya".

"Aikuwa yanzu ma zan kira ta, Allah dai yasa a garin nan take?".

"A garin Kano take, sedai tana pickup and nationwide delivery, ko a ina kake za'a iya tura maka, na fada miki zafa ki gode min, just ki tanadi kyautar da zaki min bayan kin yi amfani da kayan".

Aunty Salma ta karashe da tsokana tana dariya, Maman Ilham na mutmushi tace wa Aunty Luba

"A dai bi a hankali kar a ruda min dan uwa da yawa, bana san na ga ya zama mijin Hajiya atoh".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now