PAGE NINE

220 11 4
                                    

Ouummey 009

Page 9️⃣

________________Abincin rana a kawo ba'a kawo ba shiru har after four, lokacin kam na kai karshen dauriya dan haka na mike ina rangaji na nufi kitchen din.

Cikin Sa'a babu kowa a ciki, jiki na rawa na shiga kokarin daga indomie, tsurar ruwa kawai na dora na zuba mai da yajin indomie din na zauna jiran ya tafasa na watsa indomie din dan bani da karfin yi mata kowane iri hadi.

Ganin ba zan iya itama zamana tafasar ba na bude fridge na dauki fresh milk na fasa na shiga sha a yunwa ce kai kace ban taba shan fresh milk ba.

Ina sauke kwalin fresh milk din daga baki na Sa'adah ta shigo, ban dube ta ba na jefa empty container din a dustbin kana na koma gaban gas.

Da mamaki take kallo na kafin kuma ta sha kunu ta matso jikin freezer ta harde hannun irin na matan gida

"Wa ya baki izinin shigo min kitchen balle ki taba min kaya?".

"Yunwar ciki na ce, na gaji da jiran yunwar da kike min ne yasa na fito dan i can't take it anymore".

"Okay shiyasa kika shigo min kitchen kike min gaban kan ki?".

Ban lalle ta ba ina bare indomie ina sawa a ruwan dake tafasa na bata amsa

"Kina magana kamar gidan ki ne na ke Miki abinda ba ki so, ko kuwa kin manta kitchen din na mijin mu ne?".

"In kitchen din na sa ne kayan kitchen din fa?".

"Eh kitchen da kayan abinci na sa ne, kayan kitchen kuma naki ne, and am sorry for taba miki kaya batare da izinin ki ba".

"Oh ai na zata su ma din zaki ce na sa ne, da na sanar da ke wannan kayan iyaye na ne suka siya min cikin alfahari da irin diyar da suka haifa kuma suka aurar cikin girma da daraja batare da tayi abinda ya zubar masu da kima ba, ko kuma ya sa aka ga basu iya tarbiyya ba".

Wani kallo na juyo nayi mata, sedai ban tanka ba na juya ina juya indomie din cikin tausar zuciya ta da ta fara harzuka, duk abinda za'a min in a karan Kai na ne zan iya hakura amma ban da a sako iyaye na, tun da haka nake kuma har yanzu ban canja ba, shiyasa yanzu naki yanka wa Sa'adah dan kar ta cigaba in yi loosing control, karshe in zo in Yi abinda zan yi nadama.

Na zata ai tun da ban kula ta ba shikenan zata hakura ta bar zancen, sedai ina se ta gyara tsayuwa ta cigaba

"Shi dai dan da ya raina iyaye be yi ba dan haihuwar sa ma asarar ce, gwara ace tun yana ciki aka yi barin sa aka huta, Allah ka raba mu da haihuwar asara, wasu iyayen kam sun yi asarar haihuwa tun da har suka gaza tarbiyyantar da ya'ya ".

A wannan kadamin ne na kasa hakuri, duk kuwa da yadda na so yin na gaza har na juyo idanu jajir ina duba Sa'adah, nuna ta nake da spoon din da nake juya indomie kana cikin kausasa harshe na ce

"Duk abinda zaki yi min kiyi be zama lallai na kula ki ba dan zan iya hakuri na jure, amma ko da wasa, ko a cikin mafarki kar ki sake ki shigar da iyaye na shirin shirme da haukan ki dan zan iya gwada miki haukan da ya fi baki, na fada miki ".

Da alama dama haka take so dan kuwa murmushi ta sake,

"Ni ce mahaukaciya kenan, ko da yake a wajen ta gida na koya kin san itace shugabar mahau...."!

Ban bar ta ta karasa kalaman ta ba se da saukan marin da ni kaina na san ze yi zafi a kuncin ta, dama kuma da niyyar yayi zafin na daga hannu na, da sauri ta ja baya tana zaro ido dafe da kuncin ta

"Ni kika mara?".

"Na mare ki, kuma zan kara marin ki in har kika cigaba da kokarin gwada min dabban ci da akuyanci".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now