Ouummey 037
Page 3️⃣7️⃣
___________________Suna nan tsaye cikin tashin hankali, lokacin kuwa da za'a auna jinin Masdooq ya dade da hawa, hawan ma irin na wuce hankalin nan, zuciyar sa kuwa bugun da take ya zarce ka'ida, ya dunkule hannayen sa cikin juna amma duk da haka rawar da suke yi bata buya ba, ga zufa da ta jika shi sharkaf kamar wanda aka kwarawa ruwa.
Awa day shiru, biyu shiru ba'a fito ba, wannan ya kuma dugunzuma hankalin su, izuwa yanzu jiri yake ji, kamar gurin na juya masa, yace cikin shakakkiyar murya,
"Rike ni Luba".
Aunty Luba da itama ke cikin tashin hankali ta ji maganar sa kamar daga sama, ta juyo da sauri ta kalle shi se ta ga idanun sa a kulle haka kuma kamar yana tangadi, se ta rike shi da sauri ta taimaka masa zuwa seats a bayan su ta zaunar da shi itama ta zauna.
Yau ita ta karbi girman ta dinga lallashin sa da kalaman karfafa gwiwa, tana fada masa all will be fine, Aimah zata haihu lafiya insha Allah.
A nan suke cigaba da zama har another thirty minutes kafin red light dake blinking a kofar theatre room din ya koma green, indicating an gama komai, se duk suka mike cike da zulumin labarin da za'a basu, a lokacin nurse ta fito rike da baby cikin showel, dake tun da zasu shiga da ita nemi kayan haihuwa Aunty Luba tace babu amma in akwai wajen siyarwa cikin asibitin se a siyo, se nurse din ta mata kwatancen wani mini supermarket nan gefen su, shine fa ta fita ta siyo aka basu.
Cikin fara'a nurse din ta kara so gare su ganin yadda duk suka yi tsaye kamar wasu gumaka, tace cikin fara'a
"Congratulations Mr Masdooq".
Be iya amsawa ba se Aunty Luba ce ta karbi Babyn da ake mika masa tana amsawa da
"Thanks Madam".
Nurse din ta gyada kai ta wuce, bata iya bude Babyn ba saboda tambayar da Masdooq yayi mata
"What about NU'AIMAH?, How's she?".
Aunty Luba ta juya da sauri dan tambayar nurse din sedai cikin rashin Sa'a tayi wani wajen, se ta kalle shi cikin rashin abin cewa, daidai lokacin da another nurse ta fito itama rike da another baby cikin showel, shi be ma lura ba dan hankalin sa na kan doctor din dake tahowa, Aunty Luba kuwa Babyn da ake mikawa ne idanun ta ke kai, tunanin ta na bata abinda take kokarin karyatawa, se kuma Muryar doctor ya gasgata mata shi
"Congratulations Mr Masdooq, the theatre was a successful one, an samu nasarar cirowa matar ka twins, a baby boy and a girl, congratulations 🎉".
Ai daga ita har shi se suka daskare a tsaye, hannun Aunty Luba dake rike da baby ya shiga rawa, ga maza ta kankame showel din ranta nayin fari tass, zuciyar ta na kara gudun garin ciki.
Cikin rawar baki tace
"Doctor...w..whi..ch".Se kuma ta kasa hada sentence din saboda joy, gane abinda take son tambaya yasa doctor saukaka mata ya bata amsa da nuna mata na hannun ta
"The baby boy din ne babba, and the baby girl kuma karama"."Wai dagaske kake doctor?, Ta haihu? Kuma lafiyar ta kalau? Kuma yara biyu?, Haka kace?".
Doctor yayi nodding kai in affirmation, shima fuskar sa dauke da fara'a me nuni da farin cikin sa
"An yi mata aiki successfully, an ciro mata baby boy and a girl, abin farin cikin kuma duk suka cikin koshin lafiya a yanzu, ana gyara ta ne kafin a kai ta dakin Hutu".
Se kawai gani suka yi Masdooq ya zube a floor din wajen, not minding the dirt and everything ya yi sujudus shukur, kana ya dago idanun sa kaca kaca da Hawayen farin ciki, Aunty Luba na taya shi da nata Hawayen, ta kankame Boy din a kirjin ta,
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...