PAGE THIRTY FOUR

401 21 11
                                    

Ouummey 034

Page 3️⃣4️⃣

____________________Zazzabi me zafi ya rufe ni har jiki na na rawa, ga ni ba ko paracetamol a daki, ni kadai kamar mayya haka nake fama babu wanda ya san halin da nake ciki, a haka na wuni har magrib kafin na ji saukin sa, na tashi nayi wanka da ruwan zafi da kyar dan jiki na ba karfi, ga yunwa dan bayan tea babu abinda ke ciki na wuni guda.

Da dafa bango na fito daga toilet din na zauna bakin bed ina maida nunfashi, tsayin lokaci kafin na ja jiki zuwa gaban wardrobe ba ciro wata bubu din na saka, na fesa turare cikin karfin hali dan se na ji dakin gaba daya kamar yana tashi tashi.

Ban iya yin sallah ba se da na dafa indomie biyar na dora mata kwai hudu soyayye na cinye ta tas da zafin ta tana tururi, se da na jira ta fada min sannan na tashi nayi sallah.

Ban koma bed ba se da na yi Isha, duk da haka na cigaba da zama na dan na san ko na hau bed ba bacci zan iya yi ba, tunqnin shago na yau nake yi da ya kusan shekara a rufe, dan tun rigimar aure na da Habeeb na garkame shi ban kuma waiwayar sa ba, ma'aikatan sun yi zarya gidan mu har sun gaji nace se daga baya tukuna zan neme su, suma da suka lura ba ni da niyyar budewa se ba su sake nema na ba.

Na sani da abubuwa ba su sake rikicewa ba da tuni yanzu ba wannan maganar ake ba, na sani da shago na ya shiga cikin manyan shagunan kwalliya da ake ji da fadin su a garin nan.

Yau ma se after subh na samu bacci, ina farkawa na karya se zazzaɓi ya dawo, ban samu sauki ba se after magrib, daga ranar kuma se abin ya zama daily routine, in dai har zan karya shikenan zazzaɓi ze taho, ba ze tafi ba se bayan magrib.

Ban taba fadawa kowa ba, duk da ma bani da kowan da zan fadawa din, haka na cigaba da rayuwa, ga zazzabi ga ciwon kai, ga kuma wataran in ji kirji na yayi min nauyi, se gaba daya tsoro ya rufe ni, na dinga tunanin mutuwa zan yi, ba wai mutuwar nake tsoro ba a'a in mutu ban haife baby na ba, ina son ko da zan mutu ya zama baby na yazo Duniya, ta yadda zan tafi hankali kwance da sanin na bar me min addu'a.

Wannan tsoron se ya sake haddasa min damuwa, ya zama kullum cikin kuka da tunani na ke, ciwon kai kuwa ba ya taba bari na, safe rana da dare cikin sa nake ga kuma ƙarin zazzabi, duk se na fige na lalace na rame se katon ciki a gaba, dama ba wani aikin kirki nayi ba, ci ne ya buda ni.

Sati biyu kamar yadda yace yayi ya dawo, kafin nan kuwa yaron office din su ya kawo min irin siyayyar da yake min, ya bayar me gadi ya kawo falo Hindi kuma ta kawo min.

Hajiya Sa'adah na nan na abin da ta ga dama, rowar abinci tana nan tana yin shi se dai ko a jiki na wai an tsikari kakkausa, shi kam Masdooq har yanzu be mata maganar horan yunwar da tayi min ba a baya, ya zuba mata ido yana fahimtar ta, irin fahimtar da be yi mata ba a baya.

Sedai ya sanar da ita kar ko da wasa ya sake ganin kafar ta a daki na, haka kumq duk abinda ze min babu ruwan ta a acikin be shafe ta ba, that's in tana san cigaba da samun farin ciki da kwanciyar hankali daga gare shi.

Abin da ya kawo maganar shine bayan mun dawo daga hospital yaje yayi min siyayyar nan se ta tare shi da kissar me yasa ze min wata siyayya daban bayan muna da komai a gida, se yace mata kawai dan baya san fitina na, se kuwa tace ita dai bata ji dadi ba sai hakan kamar yana neman nuna fifiko ne tsakanin mu, wai dama ai ita ta san har yanzu yana so na waye waye, shine fa ya bude mata wuta.

Gaba daya se ta tashi hankalin ta lokacin, ita a son ranta kar ya kula ni, kar ya damu da ni da duk wani abu da ya shafe ni, sedai abin da bata sani ba shine ba wai so bane yasa yake min duk abinda yake min, kawai bin umarnin Allah da son sauke hakki ne, amma maganar so a lokacin ai babu ita, da dai shekara biyar baya ne wannan ba zan musa ba.

Ko da ya dawo ban gan shi ba ranar dan dawowar dare yayi, so na bar shi as gajiya ne ya hana shi shigowa, tun da asuba nayi ta zuba idon ganin sa, ba wai dan na san ze kula ni ko kuma zan samu wani abu daga gare shi ba, se dan kewar sa da kewar motsin sa da nayi.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now