PAGE FIFTY THREE

358 13 0
                                    

Ouummey 053

Page 5️⃣3️⃣

_______________________"Shawara kike so ko kuma goyon baya kike so?".

Na dubi Dr da mamaki, in ba shawara nake so ba har na zauna na bude nata ciki na haka?

"In har shawara kike so to ni dai cewa zan yi ki koma gidan mijin ki, in kuma goyon baya kike so se in yi backing din ki".

"Dr kar ki bata min rai pls, in ba shawara nake nema ba ai se in yi gaban kai na kawai ko?".

"Shine nace in dai ita kike nema to ki komawa mijin ki".

Hararar ta nayi ina kokarin mikewa dan da gaske na fara jin haushin wannan wulakancin da ta tsiro yau, ta maza ta riko ni tana dariya

"Dalla ina zaki?, Allah se kin zauna kin saurare ni tun da nima na saurare ki da farko".

Zama nayi ina tura baki gaba, na kau da kai gefe na ki yarda na kalle ta, itama baya damu ba ta shiga cewa

"Akwai dalilai da dama da ze sa ace ki komawa Masdooq, ba kuma iya ni zan fada miki haka ba, duk wanda ya san ku haka ze fada miki, kema kuma kin san wasu, one of which is yaran ku. Kin san dai ko da kuke jini daya Masdooq ba za bar miki yaran sa ba alhalin kin ki shi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba?, Ze karbe su ne yaje ya kai wa matar sa me son sa, wannan dai da ta azabtar dake uwar su, to ina ha su kuma.
Na biyu, shin kina tunanin in kika rabu da Masdooq zumunci zaku cigaba da yi kamar yadda wautar ki ta gwada miki?, Bayan yana yi miki so me girma? Ko kina tunanin ba ze yi kishin ki ba? To bari kiji, daga lokacin da kika rabu da Masdooq kin raba zumunci tsakanin ku, ba da shi kadai ba har da iyayen sa da ma wasu cikin yan uwan sa, kin ga kuwa kin bata goma daya bata gyaru ba.
Na uku, Aimah kina tunanin zaki samu namijin da ze so ki ya kaunace ki a rayuwa kamar baban twins?, Bana jin zaki samu nan kusa, ban ce Miki babu ba amma wallahi wahala suke, namijin da ze so ki y kaunace ki a karan kan ki da dukkan flaws din ki, alhalin yawancin maza yanzu material love suke yi, a so ki dan kyan ki, surar ki ko kudin gidan ku, wanda wannan komai me iya karewa ne, amma namijin da ze so ki a ke kan ki shine namiji, wanda soyayyar sa is unconditional, dama ba dan wani abu ya so ki ba balle in ya kare ya bar ki, kalle ni dai, me na rasa? Ina da kyau, ina da ilimi haka gwargwado familyn mu na da rufin asiri, amma aure har yau ya gagara as my age of twenty eight, saboda me?, Duk mazan da ke zuwa waje na wani abu na tare da ni suka yi biyu ba ni karan kai na ba, ke kin samu kina neman yi wa kan ki sakiyar da ba ruwa Aimah?.
And lastly, in kin rabu da shi yaya zaki yi da soyayyar sa da kaunar sa da kike yi, ko an ce Miki kuna rabuwa zaki dena jin komai ne?, In haka kika dauka to maza ki aje, ko kun rabu da Masdooq ba zaki taba dena son sa ba, kuma duk namijin da kika aura da son wani a ran ki kin cuce shi dan ba zaki taba sauke hakkin sa yadda ya kamata ba, musamman dake ga zuri'a a tsakanin ku da dole se kun dinga haduwa, balle kuma ga zumunci, ina tabbatar Miki zaki jefa kan ki da kan ki halaka, kina auren wani namiji kina kaunar wani.
Kin ga wannan bayanin, bana tunanin duk inda kike je za'a fada miki akasin sa dan iya gaskiya na fada miki a matsayin kanwa ta kuma kawata".

"Hmmm". Na sauke numfashi, tun bayan tafiyar Dr ta bar ni da aikin tunani, se dai har yanzu da ake kiran sallar magrib na kasa gano nakasun shawarar ta, da farko ban aminta ba se da nayi consulting Aunty A'i, ba wai dan ban yadda ba se dan ina son jin ita kuma me zata ce, menene view din ta a kai, kamar kuwa hadin baki se ga shi ta maimaita maganganun Dr, har na ta kara akai, hakan ya sa jiki na yin sanyi na ji na aminta da shawarar su, sedai amma ina kara yin tunani ne dan jin ko zan hango wata baraka a shawarar na su.

Na sak sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi na mike zuwa daki, alwala nayi na gabatar da sallar magrib di ta, ina idarwa na yi tasbih din da na saba, se kuma na tashi zuwa dakin Nene, wunin yau ban gane mata ba, duk muka hada ido se in ga tana yi min kallon zan yi maganin ki, ko kuma zaki gane kuren ki, dan haka gwara naje muyi ta ta kare ni da ita, ba zan iya ba, ta bar ni naji da damuwar da ke damuna mana.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now