Ouummey 044
Page 4️⃣4️⃣
____________________Yau fa a ke yin ta!.
Washegari da safe ina farkawa na ganni in a different environment, the first thing that came to my mind was my children, cikin tashin hankali na shiga neman su, se ga su na gani a gefe na covered with a very soft duvet, na yayime su a cikin cover din na makale su q kirji na, na shiga bin dakin da kallo ina zarar ido.Ina a haka ya bude kofar ya shigo, na daga kai na dube shi, duba na sosai da sosai, se kuma na sunkuyar da kai na hawaye na flowing out zuwa kan kunci na.
Se yanzu na gane, ya dawo da ni gida ne, amma kuma ai nan ba daki na bane, jin shiru be dago ba se na kalle shi a kaikaice, yana tsaye ya tokare kofa da bayan sa hannayen sa zube a aljihun sa yana kallo na, se na sake sa hannu na rungume yara na, na sani zuwa yayi ya fada min baya son su, may be ma yace ze kwace ya je ya yar, tun da da nace bana san haihuwa da shi shima yanzu tun da baya so na na san zuwa ze yi ya yar min fa yara.
Yin wannan tunanin se na sake kankame se har se da cutie ta motsa tana yin kuka, na kalle ta da sauri dan in akwai abinda na tsana a duniya to kukan su ya biyo bayan shi a yanzu dai, se na dan sassauta tare da dagowa na kafe shi da ido, se lokacin kuma ya shiga takowa zuwa gare mu, wanda duk takun nake jin sa a cikin raina yake kuma tafiya tare da bugun zuciya ta.
Da ya tsaya a bakin gadon kuwa se na ja baya da sauri ina makalewa jikin headrest na bed din idanu na a zare cikin tsoro, se ya zauna a hankali a bakin bed din, kamar ina jira kuwa ni kuma na sauka da sauri na matsa na makale jikin bango, bugun da kirji nake yi kuwa na san har shi ya gani dan be buya ba.
"Calm down Aimah, am not here to harm you, not our children".
Duk da ya fadi haka ban zauna din ba, dan ban yarda da shi ba, na san yadda ya dena so na, na kuma san yadda dole zece se ya rama abinda na masa, duk da a yanzu ban dauki komai da yayi min matsayin ramuwa ba, sedai fushi kamar yadda Abba yace, da kuma so na da ya daina yanzu.
"Wallahi na rantse miki da girman Allah ba cutar da ku zan yi ba".
Ko a halin hauka nake ba depression ba naji wannan kalaman daga gare shi zan yarda balle yanzu, ku san wani abu, na fa san Ya Masdooq irin sani da fahimtar da ban da Ya Farooq bana jin akwai wanda ya san shi ya fahimce shi kamar ni, na san waye shi akan rantsuwa, dan be cika yin ta ba ma, in kuma yayi to be meant it.
Se na gyada kai alamar na yadda, ajiyar zuciyar da ya saki kuwa se da naji ta, ya bubbuga min gefen sa tare da cewa
"Seat, please seat let's talk".
Na kalli wajen da ya nuna na kalle shi, se kamar me tafiya kan ruwa na shiga takawa a hankali naje can nesa da inda ya nuna na zauna, abin dariya har lokacin yaran na hannu na na hade su a cakude na rungume kamar wasu kayan wanki, Sarkin hakuri handsome shiru abin sa duk da na san matsar da nayi masa na takura shi, amma cutie kuka take yi ƙasa ƙasa har lokacin.
"Saurare ta, ki rage tsaurin rikon da kika musu, shi ke sa ta kuka".
Kamar doluwa se na kalle ta, na kuma sassauta rikon da na mata, se kuwa tayi shiru tana yamutsa karamar fuskar ta, abin ya bani sha'awa se nima nayi tare da taba kuncin ta na murmusa, murmushin da ya bayyana hakora na.
Irin yadda ya kura mana ido yasa na ji kallon shi a jiki na, na dago a darare na kalle shi, se na samu kuwa idanun nasa na kan mu kamar yadda nayi zato, se na maza na ja showel din cutie na rufe mata fuska ni kuma na bata tawa fuskar.
Se ya dan yi murmushi kadan sannan yace
"Na sa musu suna".
"Suna?".
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...