PAGE FOURTEEN

304 13 1
                                    

Ouummey 014

Page 1️⃣4️⃣

___________________mun dade a haka kafin kamar wanda aka matsi bakin da yace

"Sannu, ya jikin?".

Kamar ba zan amsa ba dan bana san magana, musamman da Dr ya shaida min ban mutu ba, wanda takaicin hakan ya cika min rai, se kuma na amsa can kasa a hankali idanuna har lokacin a rufe

"Da sauki".

"Allahu yashfeek".

Kin amsawa nayi dan ni ba addu'ar samun lafiya nake so ba, addu'ar mutuwa nake bukata.

Daga haka muka ja baki muka yi shiru, ni idanu a rufe ina fadawa zuciya ta shi ya kawo ni asibitin, dan in ba shi ɗin ba babu me shiga inda nake balle a san halin da nake ciki.

Shi kuma ta bangaren sa ban san me yake tunani ba, tsayin lokaci muna a haka kafin ya mike

"Dare yayi zan je gida, akwai nurse da zata kwana da ke, kina bukatar wani abu ne daga gida in zan taho gobe?".

Girgiza masa kai nayi kaina a kasa, ganin haka ya yi min sai da safe ya juya batare da ya jira amsawa ta ba da ni ma ba amsawar zan yi ba ko ya tsaya.

Be dade da fita ba nurse Ryhan ta shigo, ta min sannu tare da zama tana daddanna waya, sa'i da lokaci kuma tana min hira wanda iyaka ta murmushi, gyada kai ko girgiza wa, daga karshe ma na rufe idanu kamar na yi bacci dan bana san hirar, itama da tai magana daya biyu ta ji shiru se ta juyo, ganin idanu na a rufe se tayi tunanin na yi bacci, dan haka ta gyara zaman ta ta cigaba da chatting din ta.

A hankali baccin gaske yayi gaba da ni, dan alamu sun nuna allurar bacci aka yi a ruwan da aka sa min.

Ban farka ba se biyar na asuba, na juya daya gadon dake gefe in da nurse Ryhan ke kwance, a hankali kuma na yunkura na mike zaune, na dan jima a zaunen se kuma na sauka ina takawa a hankali zuwa toilet.

Fitsari nayi na daura alwala na fita, se kuma na tsaya tunanin me zan saka in yi sallah, gadon da nurse Ryhan ke kwance naje na shiga tashin ta a hankali, ko da ta farka se ta buɗe ido sosai gani na a tsaye, tambaya ta tayi lafiya na sanar da ita abinda nake bukata.

Cikin dan shakku take kallo na se kuma ta tambaya wai zan iya kuwa, Murmushi nayi mata tare da gyada kai cikin tabbatarwa, se ta tashi ta fita zuwa wajen su, bata dade ba ta dawo rike da hijab da pray mat ta shimfida min ina ta godiya kana ta koma ta kwanta, ni kuma na saka hija din na tada sallah.

Ko da na idar na so biya. Bashin sallolin da na rasa amma ban san kwana nawa nayi a kwance ba, so se kawai nayi adadin da nayi na bar shi, na zauna na shiga karatun Alkur'ani da hadda ta, sabida damuwa yasa har hadda ta se da ta tabu, ina bukatar Kur'ani ko dan tilawa amma ban san yadda zan samu ba.

Karfe bakwai na tashi daga kan pray mat din na koma kan bed na kwanta, a hankali nake jan nunfashi saboda kirji na dake neman tashi saboda ruku'u da sujjud da nayi, nayi lamo ina tunanin shin ni haka rayuwa ta zata kare cikin wahala, tun da mutuwar taki tazo ta dauke ni?.

Ban san awannin da na dauka ina tunani ba, ban san adadin awannin da na bata ba se da naji hannun Ryhan kan kafada ta, na bude ido na kalle ta,

"Lafiya kike kuwa? Ana ta magana amma shiru bakya ji?".

Nunfashi na sauke na sa hannu na dafa gefe da gefe dan tashi zaune, se ta sa hannu ta taya ni na zauna

"Ba komai sister, bacci ne ya fara dauka ta".

"Ga mijin ki nan yana ta Miki sannu, ya dan jima a nan amma baki ji ba".

Seda gabana ya fadi jin tace wai mijina, kamar kuma ban san wanda take nufi ba na bi inda hannun take nunawa, na sauke duba na kan shi shima idanun sa a kan mu, da sauri na kau da kai.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now