Ouummey 015
Page 1️⃣5️⃣
__________________har parking space Ryhan ta rako mu, ta so karbar number ta na sanar mata bani da waya an sace, se ta bani Tata wai in kira ta duk sanda nayi waya dan muyi zumunci, da murmushin da na kakalo na amsa ta da insha Allah, muka rabu cikin mutunta juna.
A baya na zauna saboda Dr da yace ina bukatar wajen da zan mike sosai, na sani yayi haka ne dan abinda yake ciki na, a zahiri kuma se yace saboda ciki da kirji na ne, hakan muka tafi motar shiru kamar ba masu rai Banda numfashin mu dake tashi.
Tun fa muka fita daga hospital din naji duk zuciya ta babu dadi sanin ina ne zan koma, yanzu da nake da ciki na kuma san zama da yunwa ze illata abin ciki na se na ke tunanin yaya zan yi a gidan da har abinci ana hana min in aka so azabtar da ni?.
Sedai har muka kai ban samu wani solution ba ko yaya, jiki a sanyaye na fito daga motar, ya fito da sauri yana tambaya ta zan iya?, Da kai na amsa masa wanda haka nake masa duk zaman da mukai a asibiti, bayan gaiuwa duk wata magana da ze yi da kai nake amsa masa.
A nurse cikin kiyayewa nan shiga gidan, ko ina shiru har nan shige daki na ba motsin kowa, ban kai ga zama ba shima yayi sallama ya shigo ya tsaya daga bakin kofa ni kuma na kai zaune kan sofa.
Gyaran murya yayi
"Likita yace kin fama da ulcer, kuma kina a second to the last stage, so ba'a san kina zama da yunwa, dan haka na saka miki duk wani emergency abu da zaki iya ci kafin a gama abinci, komai yan cikin fridge , some kuma wardrobe din ki, and in sun yi kasa ko kina bukatar wani abun kya iya sanar da ni, Allah ya kara lafiya".
Daga haka ya juya ya fita daga dakin, ni kuma na tashi zuwa bedroom, a can na tadda sabuwar fridge babba an girke min, ban yi mamaki ba dan tun da yace an saka min abubuwan ci to fridge din ma daga gare shi ne, se na fita na duba madaidaicin da yake rumfa, cike yake da ruwan roba kusan kayan daya da rabi, se juices kala uku.
Da na koma bedroom se na bude wannan, shi kuma cike yake da su fresh milk, yoghurts, snacks, fruits, custard, cerelac, kayan gwangwani da dai duk wani nau'in emergency feed.
Gefe daya da fridge din ƙatuwar kettle ce da cups, se kuma plate da electric cooker, kwalin indomie da kuma bottle din palm oil.
Na zauna tare da zuba wa kayan ido sosai cikin nazari, in har tunani na ya bani daidai Masdooq be san horon yunwar da matar sa ke min ba se yanzu, da ya gane kuma shine yayi min wannan siyayyar saboda baze iya mqta magana ba, ko kuwa yayi tace ba zata dinga girki da ni ba, to koma dai menene ni dai na gode, dan ban yi zaton haka, na ji dadi dan na san insha Allah batun ulcer yayi affecting baby na kuma babu shi yanzu.
Wanka nayi duk da ban dade da yi ba a hospital, Dan dakin a gyare yake daga falo zuwa bedroom da toilet din, na sani hindu ya saka ta gyara, dan in ba ita ba babu me yi.
Ina fitowa na gabatar da azahar da ta riske mu a hanya, kana na matsa jikin fridge na dauko can din kifin gwangwani da lemo rani, na hada da bread na ci na tashi, na kuma ji ni daidai alhamdulillah, se kuma na kwanta bacci abina bayan na sha magani na.
Tun daga lokacin se Allah ya yanke min izayar Sa'adah na abinci, so da yawa kafin ta gama gabtalin ta ta aiko abincin ni na riga na cika tumbina, wannan yasa wannan muguwar ramar ta ragu, sedai ban maida jiki na ba saboda laulayi kuma da ya sako ni gaba, sauƙin abin ma ba inda nake fita ko falo, wannan yasa ba wanda ya san halin da nake ciki.
Har yanzu kuma Ya Masdooq be fasa zuwa daki na ya kwanta ba tun ranar girki na, sauƙin da aka samu shine yanzu ya kan leko da asuba kafin ya fita, ko da kuwa ba'a daki na yake ba se ya shigo da asuba, daga nan kuma se wata asubar.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...