Ouummey 022
Page 2️⃣2️⃣
__________________Shiru yayi yana saurare na har na gaji da yan koke koke na nayi shiru, jin bai da niyyar magana yasa na dan ja numfashi na kira shi cikin tantamar ko ya katse kiran ne, se kuma naga he's still on the line da na duba screen din, se na maida wayar kunne na
"Sweet tooth".
Se lokacin naji ya ja doguwar ajiyar zuciya, daga zaunen da yake ji yake kamar ana hajijiya da shi, idanun sa dake rufe ya fara budewa a hankali har ya ware su, sun canja color zuwa wani irin blue blue dan tashin hankali.
He never knew Ina da saurayi, for once ba wanda ya taba fada masa, not su Ya Salman and not even iyayen mu, nima kuma ban taba masa maganar ba se yau, me yasa rayuwa zata zo masa a haka.
Sake kiran sunan shi da nayi da sweetheart yasa ya sake sakin deep breath, kafin ya fara magana da Muryar sa da ta dishe a take kamar wanda ya yi sati yana fama da zazzafar mura
"Nu'aimahhhhh".
Yadda ya kira real ssuna na haka kuma cikin wani irin tone me bayyana zafin da zuciyar sa ke masa haka kuma a shake yasa na ji gaba daya jiki na ya mutu, na kankame pillow na amsa masa da
"Uhmmm".
Se ya sake yin shiru dan ya rasa ma me zece, gaba daya ya nemi malamai a bakin sa ya rasa, haka muka yi shiru muna sauraren shiga da fitar numfashin juna na tsayin lokaci, zuwa sannan ya samu ya dan yi controlling kan sa se ya fara magana da sanyayyar muryar sa me sama min nutsuwa,
"Is okay, na fahimce ki, ki daina kuka kin ji hakan is not good for your health, wannan maganar ba ta waya bace, kiyi hakuri ki kwanta ki yi bacci, zan zo gobe kin ji, we'll find a solution, a very good one kin ji Barbie?".
Yadda sooting voice din sa ke ratsa ni yasa na shiga gyada kai a hankali kamar yana gaba na, se kuma cikin shagwaba na da ya zame min jinin jiki na autanci nace
"Amma bana jin bacci, kai na ma ni ciwo yake yi, kuma zuciya ta ma ba dadi".
Yanzu ma naji saukar ajiyar zuciyar sa, kana cikin lallami yace
"Ki dauki Alkur'ani kiyi karatu, insha Allah zaki ji saukin komai, ki kwantar da hankalin ki and know one thing, what ever Allah planned to be must be, duk kuma abinda kika ga baki samu ba dama ba baki bane, put this at the end of your mind, what's planned to be yours must surely be, and what's not yours would never be, just pray and leave the rest to Allah, ze kawo Miki mafita Bi'iznihi".
Cuno baki nayi gaba, ni duk cikin maganganun sa ba daya da ya shige ni, ai na sani Ibrahim and I are destined to be, to kuma Meye na wani magana, bayan kawai Abba ke neman kawo matsala ga lamarin, jin nayi shiru yasa yace "kin ji?".
"Nace maka fa kai na na ciwo, ba zan iya karatun ba".
"Then ki kwanta and put the phone earphone, I'll be reading it ke kuma ki saurara".
Ban so haka ba, amma ba zan iya masa musu ba, haka na jawo headphon na saka na koma na kwanta tare da jan blanket na lullube jiki na, a hankali cikin nutsuwa, da wannan sassanyan muryan nasa, very deep and low yayi basmala ya fara karatun sa cikin suratul Noor, kira'ar sa me matukar dadi da sanya nutsuwa ta sa na gyara kwanciya ta tare da rungume pillow a kirji na, idanu na a lumshe nake saurar sa yana karatun cikin fitar da tsantsar tajweed, a hankali nake jin nutsuwa da salama na sauka cikin raina, zuciya ta ta shiga yin sanyi kamar wadda ake kwarara ruwan kankara, nunfashi na ya shiga fita a hankali, ina ta sauraren sa cikin wani irin shauki har ban san sanda bacci ya dauke ni ba.
Daga can bangaren sa karatun yake yi cikin son samawa kan sa da kuma ita nutsuwa, idanun sa a lumshe ya ke zubo haddar sa da ka, haka kuma yake fitar da kowane baki yadda ya dace ya kuma kamata, a haka ya sauke Suratul Noor ya sake basmala ya shiga Suratul Yusuf, ba wai a jere yake yi ba, a'a, favorite surahs din sa yake karantawa yana jin sanyi da Salama na saukar masa, ya shiga sauke ajiyar zuciya a kai a kai, yana jin samun daidaituwar numfashin sa da a daxun ya ƙara gudu kakar me cutar asthma, seda ya kai karshe har yayi basmala ze fara suratul Mumin se kuka ya saurara ya gyara zaman Bluetooth din da ya makala a kunnen sa, a sannu yake jin fitar numfashin ta alamun tayi bacci, ya sauke deep breath kana ya zare Bluetooth din ya aje ya kuma kashe kiran sannan ya cigaba da karatun sa.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...