PAGE TWELVE

260 9 0
                                    

Ouummey 012

Page 1️⃣2️⃣

____________________Irin azabar da nake ji ya tabbatar min da kyar in ba rayuwa tace ta zo karshe ba, ga mamaki na maimakon naji firgici se naji har zuciya ta ina son mutuwar, gwara na mutu ko na huta da wannan azabar rayuwar da nake ciki, gwara na mutu kila rabo na na kiyama ne ba duniya ba, fatana kawai Allah ya sa na cika da imani.

Yin wannan tunanin yasa duk zafi da radadin da nake ji ban kira wayyo ba, ambaton Allah da kalmar shahada ne kan harshe na, a yunkuri na na in na tashi mutuwa na dace da rahmar Allah.

Haka na kwana cikin wannan ciwo da azabar, na wayi gari cikin sa na kuma wuni kana na sake kwana, lokacin kuwa tuni na fara ficewa daga hayyaci na, dan idanuna na ma bana iya budewa, numfashi na ma baya suka ciki na, daga can saman kirji naa yake tsayawa.

Da sanyin asubar washegari gaba daya nayi loosing, tun ina kokarin fisgo numfashin har hakan ya gagara ni nayi passing out!.

*********

Ba ya san shiga hakki haka kuma yana kokarin kiyayewa da wanzar da adalci tsakanin su, shiyasa rannan da yake a matse ba ze iya hakurin jure har kwana ɗaya ba kafin yaje ga Sa'adah, ya kau da komai ya rarrashi zuciyar sa yaje gare ta, sedai yayi mamakin samun ya cikin duhu dan basa shiri ko kadan, ko a da da kyar yayi yaki da ita kan kwana cikin haske kafin ta daina, be sha madarar mamaki ba se da ya kunna fitila ya same ta manure a gado, ba hakan ne ya bashi mamaki ba dan may be taji shigowar sa ne yasa ta makure, mamakin na irin ramar da ya gani a jikin ta ne.

Rama me asalini muni da rashin kyau, gaba daya ta canja kamar ba Aimah ba ta koma wata a ba can, a lokacin yana cikin gigicewar matsuwar da yayi, dan haka ya ture komai yayi abinda ya kawo shi.

Duk da be bita a hankali ba, haka babu wani lamari me nuna shauki balle motsa ta amma ba hakan ya sa ya kasa gamsuwa ba, 100% ya ji shi zam zam, ko da ya gama ya dago dan taimaka mata ta gyara jikin ta se kawai incident din wancan lokacin ya fado masa.

Baze taba manta wannan ranar ba dan tana cikin ranakun farin ciki na rayuwar sa, duk kuwa da cewa ba da san ranta komai ya faru ba, haka kuma akasin yanzu lokacin she fought him ba hakan ya hana shi enjoying moment din ba.

Base manta yadda ya dinga lallashin ta da kalamai masu nuna tsantsar soyayyar ta ba gare shi amma ta sa hannu ta tankwabe, instead ma se ta shiga kira masa sunan wani katon gardi akan gadon auren sa, me ya kai wannan takaici da ɓacin rai, ace ka kasance da matar ka ta sunna amma ta na kukan da ta san haka ze faru da ta bawa wani kanta a waje dan kar ka samu abinda yake rightfully yours? Addini ya mallaka maka iyaye suka shaida?, Babu!.

Awajen sa da ma wajen duk sauran maza kamar sa masu kishin abinda suke so babu abinda ya kai wannan ɓacin rai, takaici, bakin ciki da tashin hankali.

Gama wannan tunanin gaba daya se ran sa ya ɓaci, zuciyar sa ta dugunzuma, ji yake kamar lokacin ne abin ke faruwa, wannan yasa ya tsallake ya bar ta a wajen bayan ya ja dogon tsaki.

Sedai ko bayan wasu kwanaki ramar da tayi na fado masa lokaci zuwa lokaci, yana jin kamar ya damu da hakan, har wani bangaren na zuciyar sa na jin haushin kan sa da kan sa na damuwa da wadda bata damu da shi ba.

Karfi da yaji ya saka kwanji ya kori tunani da damuwa kan ramar ta, ya maida kan sa very busy dan ma kar ya tuna ta, yana dawowa gida kuma Sa'adah na jiran sa da tarin salo salo na kaunar ta, wannan ya taimaka kwarai wajen mantar da shi halin da take ciki.

Yau ma girkin ta ne, haka kuma baya jin sa daidai, duk yadda yaso ya daure kuma ya kasa, hakan ya sa ya aje pen din da yake rubutu ya tashi, suit din sa da ya cire ya dauka a hannun sa ya fita daga office din, ko kula tambayar da secretary din sa ke masa na ko lafiya be yi ba, dan be saba tashi a lokaci irin haka ba, shiyasa secretary din ya damu yake tambayar lafiya, amma Masdooq be iya ya amsa masa ba, se fadi da yake a rufe masa office.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now