Ouummey 004
Page 4️⃣
_________________Bata kuma ce masa komai ba ta haɗa masa ruwan wanka kana ta dawo bakin gado in da ta zaunar da shi ta shiga cire masa kayan jikin sa, da undies ta bar shi tare da tura shi cikin toilet ta rufe kofar.
Kayan bacci ta fitar masa tare da feshe su da turare ta aje masa kan bed din tare da fita ta shigo masa da abinci.
Ko da ya fito kayan ya saka tare da zaman cin abinci yana yi yana satar kallon sa da ta zuba masa ido har ya gama.
Tana dawowa daga kai kayan kitchen ta kamo hannun sa daga zaunen da yake kan carpet ta kai shi kan bed tare da fadin
"Muyi bacci, Allah ya tashe mu lafiya".
Kwanciya itama tayi tare da jan duvet sedai inaaa, baze iya ba, baze iya wannan wasan nata ba, shi ba haka yayi tunani ba, ba kuma haka ya zata ba, ba kuma ze yarda da silent punishment din nan ba, kawai Gara ta tashi ayi ta ta kare dan haka ya yaye duvet din
"Tashi muyi magana Aadah".
Ɗan bude ido tayi daga kwancen
"Ka gaji kana bukatar Hutu, mu bari zuwa gobe ko?".
Hannu kawai ya sa ya dago ta ya zaunar tare da kamo hannayen ta duka biyun ya rike cikin nasa, sedai ya rasa ma me zece, ta ina ze fara ko taya ze fara, hakan yasa yayi shiru tsayin mintuna.
Sa'adah dake kallon sa cikin tausayawa dan kam ta san mijin ta, ta kuma fahimci situation din sa se ta zame hannun ta daya ta maida kan nasa, cikin sooting voice tace
"Ba se kace min komai ba Hubby, na sani na kuma fahimce ka, na sani ba zaka yi duk abinda ka san ze sani cikin damuwa ko tashin hankali ba, ba zan rufe ka ba at first hankali na ya tashi, na rude na kuma firgice dan ban haɗaka da komai, dole in shiga damuwa jin na gaza maka har ka kawo min wata ka haɗa mu tare, sedai da Aunty Luba ta zauna ta fahimtar da ni se na gane baka da laifi, iko da isar hajiya Yayah ne yasa ta kawo wata tsakanin mu saboda ganin dacewar hakan, mu kuma a matsayin mu na ya'ya masu biyayya ne ga iko da umarnin su dan haka ina me farin cikin sanar da kai yanzu babu digo na jin haushi ko fushi da kai a raina, haka ma Hajiya Yayah dan mahaifiya ce gare ni, yadda ba zan yi fushi da ikon Ummu a kaina ba haka itama.
Nidai bukatata daya ce a wajen ka, ko kuma ma ince alfarma daya nake nema daga gare ka, na sani kaso Aimah ta yarda har ka samu ciwon zuciya akan ta, na sani itace farin cikin ka kuma kwanciyar hankalin ka kuma zaka iya komai a kan ta ciki har da bayar da rayuwar ka domin tata, Ina so dan Allah ka dinga tunawa cewa na so ka kuma ina son ka da dukkan rayuwa ta, kaina farin ciki na kuma kwanciyar hankali na, kamar yadda zaka iya mutuwa domin ta ka dinga tuna ni zan yi abinda yafi mutuwa a kan ka in har akwai shi, ina rokon alfarmar dan Allah kayi adalci tsakanin mu, ban ce dole ka so ni yadda kake son ta ba dan na san ita din rayuwar ka ce, sedai ko yaya ne kar ka gwada min bana da gurbi ko muhimmanci ga rayuwa da zuciyar ka , in har hakan ya faru ban san ya rayuwa ta zata kasance ba, ban san me ze faru da Ni ba, na dai san zan iya hadiyar zuciya na mutu wallahi Hubby.
Ka sani ina da kishi a kan ka, ina da matukar kishi musamman kuma akan AIMAH, ban zauna da ita da kai ba amma ina kishin ta fiye da duk wata mace da zata rabe ka a duniya, dan Allah kar kayi abinda ze sa kishi na akan ta ya halakar da ni, ina son ka Masdooq, tsananin son da ban san iyakar sa da iyakar abinda zan iya yi domin ka ba, dan Allah ka taimaka ka min wannan alfarmar dan.....".Da sauri yasa hannu ya rufe mata baki zuciyar sa na karyewa da wani irin rauni da tausayin ta, ya sani Sa'adah na son shi, son da wata ya mace baya taɓa gwada masa ba, shi waye a cikin butulu da ze fifita wace mace a kan ta?, Macen ma kuma AIMAH for Allah's sake!!!.
Ya sani ya so Aimah da dukkan rayuwar sa, ya kaunace ta da dukkan zuciyar sa, ya sadaukar da farin cikin sa wa so da kaunar ta, ya yi tolerating din ta fiye da duk yadda yake tunani, haka kuma yaso rayuwa da ita har a aljanna, sedai bayan duk yadda abubuwa suka kasance baya jin yanzu akwai wadda ya tsana ko da ganin inuwar ta kamar ta, tuni ya ƙera wata iriyar akwata da karfen kwangir wanda hausawa suka ce yanke shi se makerin asali ya zuba duk wani so da kauna da yake zuciyar sa a kan ta, ya sa mukulli ya rufe tare da jefar da key din cikin kogin da dadai duniya babu ke iya samo shi balle har a bude, dan haka so da kaunar Aimah a ran sa shuɗaɗɗan al'amari ne haka kuma dawowar shi mafarki ne da baze taba tabbata ba.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...