PAGE TWENTY NINE

346 17 1
                                    

Ouummey 029

Page 2️⃣9️⃣

___________________Sosai Hajiya Yayah ke kula da ni, komai ina zaune ake min, bana komai da kai na ban da shiga toilet da cin abinci, Baba ma kullum se ya shigo duba ni so uku a rana, haka kuma se ya tambaye ni me nake so, duk abinda na fada haka za'a kawo min, ko ma ban fada ba se ya siyo wani abu da ya san ina so ya kawo.

Iya gata Baba yana gwada min, shiyasa nake kokonton canjin sa a kai na yanzu.

Ya Masdooq kuwa tun korar da Hajiya Yayah ta masa be sake shigo min daki ba, one among the amazing and beautiful facts about him kenan, biyayya, yana da matuƙar biyayya ga iyayen sa har ma dasu Mama, da wuya, kai zan ce ban ma taba jin ya maida wa daya daga cikin iyayen mu magana ba, komai suka ce sedai yace to.

Kwana uku da dawowar mu na fara taka kafata, a kwana na biyar kuwa na warke sumul, ranar a na i gobe tariyar da Abba yace, sedai abinda basu sani ba shine sedai wata amaryar ta tare ba Aimah ba.

Daren washegarin da zan tare zaune nayi na ki bacci, duk da haka kuma na saka alarm kar ma bacci ya sadado ya cuce ni, aikuwa haka aka yi, bacci ya dauke ni ban sani ba, amma dan albarkan alarm dina ya tashe ni, dake kuma na saka abin a raina kadawa biyu yayi na farka.

Nan da nan na tashi na dauko karamar handbag dina da na zuba duk wani abu da na san zan bukata, ATMs dina kudi, ID card da wayoyi na, a hankali na gama karewa dakin kallo ina tabbatar na dauki komai da na tsara tafiya da shi, se na fito cikin sanda, a irin wannan lokacin ne na san su Ya Masdooq da Baba ke fita Masallaci, Hajiya Yayah kuma se an yi kiran biyu take tashi ta tashe ni, dan haka na san yanzu tana bacci, Baba kuma da su suna masallaci, me gadi kuwa Sarkin bacci ne na san zan iya ficewa yana can yana baccin sa kamar gawa.

A sadade na sauko daga stairs, na karewa falo kallo to make sure ba me gani na sannan na fita zuwa compound, aikuwa kamar yadda na zata ina zuwa bakin gate babu kowa, megadi yana can bacci a daki with assurance din ai ya sa sakata, ajiyar zuciya na sauke cikin jin dadi da farin cikin komai ya tafi daidai.

Na saka hannu na zare sakatan da ya saka, duk da girman ta amma ba me kara ba ce sosai, so na zare ba wani dar, kana cikin kwarin gwiwa na ja karamar kofar jikin gate din zan fita, se kuwa idanu na cikin nasa.

Ya shiga bina da kallo cikin mamaki dan ya ma kasa magana, ni kuma gaba daya fuska ta ta hade cikin takaici da bacin ran yadda se da na zo gabar hango farin ciki sannan plan di na ze ruguje, cikin kokonto ya kira sunana

"Honeybun?".

Ya fada kamar dai be yadda ni din ce tsaye a gaban sa ba, se na dago cike da tsiwa na batare shi tare da murguda masa baki

"Nu'aimah ne sunana ni ehe".

Se ya kuma daskarewa a tsaye, ganin haka na raba ta gefen sa da tunanin kawai na fice se na fyalla da gudu abu na, faffaɗan hannun sa yasa ya riko damtsen hannu na kam, na dago cike da rashin kunya sedai ganin yadda fuskar sa ke hade yasa na hadiye yawu mukut, na kasa cewa komai se dukar da kai da nayi, yana ganin haka ya shiga jan hannu na zuwa cikin gida, dama yana sani ya hade rai dan ya san in ya zauna yin lakwa lakwa zamu bata lokaci ne kawai dan ba lallashi zan ji ba.

Daga masallaci ya taso ya taho bayan ya katse nafilar da yake yi jin cikin sa na juya meaning yana bukatar ziyartar toilet, ashe rabon ba zasu wahala neman ta da sunan ta gudu bane, se gashi ya ci karo da ita.

Ganin muna komawa ciki yasa idanu na cika da kwalla, bana san auren nan na fada, na nuna a aikace , me yasa ba zasu bar ni ba?, Me yasa ba zasu kyale ni ba? Ana dole ne eye!.

Be tsaya ba se da ya kai ni har bedroom dina, ya sake min hannu bayan mun shiga, kana ya dube ni a kausashe, idanun sa jawur na bacin rai, cikin Muryar da ban taba jin shi da ita ba, dan ko yana da ita be taba amfani da ita a kai na ba yace

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now