PAGE FIFTY

474 23 0
                                    

Ouummey 050

Page 5️⃣0️⃣

_____________________Zancen ya shigi Nene sosai amma se ta danne bata nuna ba, se ma ta dauko Radio din ta ta Murda ta canja tasha tana sauraren wakokin garin su na da da ake yi, Masdooq ya zuba mata ido, wato dai itama ta iya kafiya da taurin kai, Allah ma yasa ba ita daga Mama har Aimah suka gado ba.

Haka suka cigaba da zama , shi yana wasa da ƴaƴan sa ita kuma tana jin radio din ta, ni kuwa ina daga bedroom kan bed ina karatun littafi na abi na.

Ban ji kiran sallah ba saboda speaker din masallacin kusa da mu ya lalace, se kawai ji nayi an fisge min waya ta, na zabura na mike zaune daga kwance da nake, na dube shi yana rike da wayar yana duba abinda ke kan screen din, se ya dago ta kalle ni

"Kema kina bata lokacin ki wajen karanta wadannan karairayin kenan?".

"Ba na karanta karairayi se litattafan da suke da ma'ana masu ilmantar wa".

"A tashi haka lokacin sallah yayi".

Na karbi wayar daga hannun shi na aje, ya riga ni shiga toilet din dan haka na zauna jiran shi ya fito, yana fitowa na shiga nayi alwala na fito se na tadda shi kan sallaya, da hannu yayi min nuni da muyi jam'i, ban ki ba ya ja mu sallah.

Muna idar wa na yi azkhars dina da tasbih kana na gaida shi, abinda ya zame min dabi'a kenan duk in na yi sallah.

Tashi nayi zan koma kan bed ya riko hannu na ya dawo dani gaban sa ya zaunar, na zuba masa ido dan jin dalilin hakan, se yayi gyaran murya yana kallan fuska ta

"After duk abubuwan da suka faru months back na zo baki hakuri Aimah, duk da wasu abubuwan babu laifi na a ciki amma na dauki komai da komai, so batare da wani bude zance ba ko maganganu ina me baki hakuri tare da neman alfarmar ki yafe min duk wani bacin rai da damuwar da na saka ki, with or without my consent kin ji ".

Na dan kai da kai gefe ina hadiye yawu tuno wahalhalun da na sha watannin baya, sedai kamar yadda na fada muku na riga na yafe mishi na kuma masa uzuri, in yana da laifi a abinda ya faru be fi kashi 10 cikin dari ba, dan haka basu kai in ce zan rike shi da su ba.

"Na dade da yafe maka Yaya, ban rike ka ba tun farko dan na yi wa Abba alkawarin yi maka uzuri da kuma yafiya gare ka akan laifin da zaka min tun kafin kayi, so komai ya wuce a gare ni insha Allah".

Jawo ni yayi ya rungume kam kam yana fadi kasa kasa

"Na gode sosai wify, na gode my wife Allah ya miki albarka".

"Ameen ". Nace ina zame wa, se ya kada baki yace

"And again, ina nemawa Sa'adah alfarma, ki yi hakuri itama ki yafe mata, ba halin ta bane wallahi, zuga ce da sharrin shaidan kuma ta tuba, Please ki yafe mata".

Na tsare shi da ido ina masa wani kallo me kaifi, tsayin lokaci ban janye ido na ba har se da ya tsargu, ganin yadda ya shiga kame kame se kawai nayi murmushi na haye bed ban amsa shi ba.

Taya ka, taya ma ze yi wannan tunanin?, Yafiyar ma shi ze nema mata?, Duk abinda tayi min ta fi karfin kira ko ko dan iska text ta nemi gafara se shi ze nema mata?, Bayan tana cikin yan gaba gaba wajen jefa ni halin da na samu kai na a baya, ko da yake hakan ba komai bane, ai inda soyayya ba abinda ba za'a yi ba.

Gaba daya se naji karatun ma na daina ganewa bana kuma fahimta, raina ya daina min dadi, se kawai na kashe wayar na kwanta sosai tare da rufe ido na.

Bude kofa aka yi, na zata ma shine ta fita se naji Muryar Nene na fadin

"Wai kana nufin q gidan nan zaka kwana ba hotel ba?".

"Wane irin hotel kuma ana zaune kalau Nene, ga ni da gidan kaka da kuma dakin mata, haba dai".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now