PAGE ELEVEN

226 11 2
                                    

Ouummey 011

Page 1️⃣1️⃣

________________Se kawai na kwanta ringine ina kallon ceiling din dakin, zuciya ta na kuna idanu na sun yi jajir sedai alkawari nayi ba zan kuma kuka akan komai da ya shafi auren nan ba, ba zan kuma kuka akan komai ma da ya shafi rayuwa ta ba, na sallama kowa kamar yadda suka sallama ni, ba ni da kowa, shi kuwa Ya Masdooq na aje shi a can wani gefe na zuciya ta, na bashi matsayin wanda ya bani wajen zama yake kuma taimaka min da abinci, ban da haka babu komai, babu komai, babu komai!!!, Na maimaita wa kaina.

Tun daga ranar ban kuma fita falo ba, komai na rayuwa ta a dakin nan nake yin sa, bana komai ban da gyaran daki, wanka sallah da cin dan abincin da aka sammin, tunani kuwa yace Bismillah.

Duk na zauna bani da abin yi se tunani, tun daga farkon rayuwa ta da nayi wayo har zuwa yanzu da komai ya lalace.

Sa'adah kuwa baya fasa min izayar abinci ba, yanzu da ta karo sabon salo ma se ta hanani abincin in ta ga dama, ta shigo ta kare min rashin mutunci ita kadai, wataran ma har da gayyar kawayen ta ko dangin baban ta, ban taba daga kai na kalle su ba, kar kari suyi su gama su gaji su fita.

A haka aka dawo da princess daga gidan Aunty Luba, shima daga kwancen da nake naji dawowar ta tare da babanta, suna ta farin ciki abin su, a very happy family, wannan yasa na sake killace kai na kar na bata musu farin cikin nasu tun da ni ai annoba ce.

Sannu a hankali lokaci na tafiya rama ta na karuwa, damuwa da tashin hankali sun min yawa, ga kuma horon yunwa agefe, na rame sosai ta yadda kayana se an saka mu mu biyu a ciki, fuska ta duk tayi zuru zuru, babu hadin wannan sabuwar Aimah din da tsohuwa ban da na suna.

Kafa ta da na fadi a kan ta tun kwanaki na min ciwo sa'i da lokaci, ya zamana ma duk sanda zan yi sujjud se da dabara, ba wanda ya san halin da nake ciki haka nima ban sanar da kowa ba, to wa zan sanarwar Bayan bani da kowa?!.

Wannan yasa na cigaba da gasata da ruwan zafi kawai, se kuma ta rage zafi amma kamar kashin gwiwar tawa ya rabu biyu, ba kamar da da yake daya ba, aka zo ma ta daina zafin gaba daya, se in na bige ko na taka kafar da karfi.

Wata uku bayan incident din na shiga fama da wani irin ciwon kirji me azabar wahalarwa, in ya tashi ji nake kamar ba zan rayu ba, ga gefen ciki na da ban isa na mike tsaye ba se in ji kamar an daure min gefen wajen.

Tun ina kokarin kautar da kai har na hakura na mika wuya cewa ulcer ce ta kama ni, ulcern kuma irin me karfin nan, sedai yanzu ma ban yi kokarin sanar da wani ba, na cigaba da rayuwa a haka da dadi ba dadi, da lafiya da babu, ina dai yin addu'a a ruwa in sha.

******

Kamar kullum yau ma haka ta tashi a firgice, jikin ta duk ya jike da zufa, se zare ido take yi kamar zata gan ta a gaban ta.

A hankali ta kai hannu ta gyara gashin ta da ya barbaje sanadin kwanciyar da tayi, ta daure gashin waje guda kana ta aje hannun ta a sanyayen.

Sati biyar kenan da fara wannan mafarkin nata, safe, rana da dare in dai zata kwanta se tayi mafarkin ta , cikin different conditions, se dai ko daya babu yanayi me dadi ko kyau, musamman ma na yau, shiyas aya firgita matuka.

Tana cikin ran ta kullum, a ko da yaushe tunanin ta na kawo mata farmaki, sedai tana korar shi da karfi dan bata san duk wani abu da ze tuna mata da ita, sedai bata san me yasa ba yanzu take wannan mafarkin da ita, ta sani bata sa damuwar ta a ranta ba balle tace, to ko dai tana cikin wani hali ne a can din?.

Se kuma da sauri ta girgiza kan ta tana Kore tunanin, ta fi kowa sanin ina ne take, guri ne da ta tabbatar za'a kula da ita irin kular ma da ita fushi baze bari tayi mata ba, ta tabbatar ba ze cutar da ita ba ko da kuwa ba ze karbe ta da wuri ba, dan haka batun tana cikin wani hali ma be taso ba.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now