PAGE THIRTY

345 14 1
                                    

Ouummey 030

Page 3️⃣0️⃣

___________________Karfe takwas na dare kowa ya watse se Aunty Luba kawai da Ya Salman ze tafi da ita in yazo, tun tana lallashi na ta dadin rai har ta gaji ta zuba min ido, kuka nake yi kamar wadda aka kawo kabari ko kuwa gidan yankan kai ba wai gidan Ya Masdooq ba, Aunty Luba ta zuba min idanun ta da suka canja kala, ranta baya mata dadi ganin yadda nake kuka akan auren dan uwan ta, kar ku manta jini daya fa ba wasa ba, gashi ni kuma sakara ba na boye kin auren a gaban kowa hatta kuwa mahaifiyar sa Hajiya Yayah, can Aunty Luba ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannu na da suka sha jan lalle da baki tun last week, kuma dake ba wani aikin ruwa nake ba zanen yana nan tar kamar jiya aka yi shi

"Mun taso tare karkashin kulawar uwa daya kuma uba daya dake Little, mun nuna miki gata da so da kauna, tun bare Mama da Abba, haka kuma Baba ma ba'a barshi a baya ba, Ya Masdooq ya soki tun kina kankanuwa, a lokacin dan gidan su babu yarinya mace, su Ya Salman duka sun so ki sun kauna ce ki kuma sun yi wahala dake, ni kuwa kallon ki nake da idanu biyu, daya kanwata mafi soyuwa a rai na, na biyu ƴata abar alfahari na duk da kuwa ban ci na haife ki ba dan shekara bakwai kawai na baki, amma yarda da so da kaunar dake tsakanin mu yasa ke kan ki kan kirani Little Mom, Hajiya Yayah na kaunar ki duk da ita bata miki irin yadda mu muke miki, duk wannan so da kaunar da muka shafe shekara da shekaru muna gwada miki ace abu daya yaa gagare mu samu daga gare ki Aimah?, Ba fa rayuwar ki muka roki ki bamu ba, ba kuma wani sashe na jikin ki ba, rokon mu kawai ki kwantar da hankali ku zauna lafiya da dan uwan ki, yayanki kuma mijin ki a yau, wanda kin fi kowa sanin shi, kina cikin wanda zasu ba da shaida akan shi a karba ba tare da kokonto ba, amma hakan yana neman ya gagara, jibi yadda kike kuka kamar wadda aka saka cikin kabari tare da bakin kumurci ba wai amaryar da aka kawo gidan angon da ke son ta da kaunar ta ba, fada min, shin Ya Masdooq na da wani mugun hali mara kyau wanda mu bamu sani ba da ya hana ki karbe shi matsayin miji?".

Ban amsa ba se fama goge hawaye da nake da dayan hannu na, maganaar gaskiya babu wani hali mara kyau da Ya Masdooq ke da shi, ba shi da makusa ta bangaren halitta balle hali, kwata kwata ba shi da aibu da ze hana a zauna da shi matsayin miji, hasalima duk macen da ta same shi matsayin abokin rayuwa ta gama dace kuma ya kamata ta godewa Allah, ni kawai matsalar shine bana son shi, bana mishi so na aure, soyayya da kaunar dake tsakanin mu ta yan uwan taka ce, so na aure Ibrahim kadai nake yi wa, me yasa ba zasu gane ba!.

"Ki fada min matsalar kida auren nan Aimah, wallahi in har dalilin ki me karfi ne I'll back you, zan tsaya tare da ke yar uwa ta har se na ga an raba ki da shi, ni ban damu da shi ba, ban damu da ya yake ji ba, ke ce concern dina, ke nake bukatar ki samu kwanciyar hankali da nutsuwa, shiyasa nake son jin menene matsalar dan taya ko magance ta".

Jin wannan bayanin daga little Mom se na samu sauki har na rage kuka na zuwa kuma ya tsaya gaba daya ina sauke ajiyar zuciya, se na sa hannu nq dage lafayar da aka ja ta rufe min kai, na dubi Aunty Luba da kodaddun idanuwa na

"Baya so na little Mom, Nima bana san shi, taya ya zaman aure ze yi yiuw a haka, Ibrahim kadai nake wa son aure, kaunar mu da sweetheart kauna ce ta yan uwan taka ta jini ba wai ta soyayyar aure ba".

"Shine kawai matsalar?".

Se na daga mata kai ina jin dadin ta fahimce ni ita

"Ko kin san lokacin da akai auren mu da Ya Salman nima bana masa son aure Aimah?".

Da mamaki nake kallon ta dan ban taba sanin haka ba, irin yadda ta amsa zancen auren lokacin da aka zo mata da shi a wancan lokacin yasa kowa yake tunanin dama itama tana san Ya Salman din, daga nan kuma aka yi shirye shirye aka yi aure batare da ta bada kowace matsala ba, se ma farin cikin ta da take nunawa, ya kuma yanzu zata zo tace min wani bata son shi, kuma tayi tunanin na yadda?.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now