PAGE TWENTY EIGHT

298 9 2
                                    

Ouummey 028

Page2️⃣8️⃣

___________________Sabida tsabar  rudewa da tashin hankali gaba daya se na manta Masdooq sunan sweetheart ne, se na tafi yawon tunanin waye Masdooq, a ina Abba ya san shi har yake yabon shi haka har kuma ya iya daukar ƴa guda ya bashi.

Da na kasa tunowa se na shiga tambayar Abba, shi da Mama se suka kalle ni cikin mamaki kafin Abba ya sanar da ni Masdooq dai nawa, dan Hajiya Yayah da Baba.

A lokacin ne na shiga asalin tashin hankali, kawai tunani na yadda zamu yi zaman aure da sweetheart, mutumin da nake matuƙar so da kauna a matsayin Wa na, kallan wanda muke CIKI ƊAYA nake masa, kallan wanda muka zauna mahaifa daya muka sha mama daya, ta ina zan fara rayuwar aure da shi, inaaaa, hakan ba ze yiwu ba, ba zan yadda ba kuma ba ze taba Kasancewa ba.

"Naji na yarda ka aura min duk wanda kake so, gurgu ko makaho kai ko almajiri ne na yarda, amma dan girman iyayen ka Abba kar ka haɗa ni zaman aure da Ya Masdooq, wallahi ba zan iya ba, yayana ne fa, Abba kallan wanda muka fito ciki daya nake masa wallahi, dan Allah Abba ka dube ni ka dubi makoma ta".

Na fada cikin gunjin kuka, ni yanzu na yadda ya aura min kowaye, ko ba Ibrahim ba ne, amma ban da Ya Masdooq, ban da shi, ba kuma dan na tsane shi ba, se dan ba zan iya ba.

"Wannan shine iya zabin da zan iya miki, gatan da zan iya miki kenan a gidan duniya, dan haka kiyi hakuri ki maida komai ba komai ba, Masdooq yayan ki ne, amma ba wanda kuke ciki daya ba, dan haka babu inda aure ya haramta a tsakanin ku, so ki tashi kije ki sake tunani, ya sanki kin san shi, zan iya cewa kina cikin wanda suka masa makurar sani, dan haka bana tunanin zaku sami matsala Insha Allah ".

Daga haka Abba ya tashi ya shige bedroom din sa, leaving me helplessly crying a falon, Mama ta zo zata kama ni amma naki, na kwace hannu na na tashi ina layi da burarin kuka na fice, dan ai da hadin bakin ta aka yi komai, ba yadda za'a yi ace Abba yayi lamari irin haka bata sani ba, shine ta rufe ni bata gaya min ba tun da wuri in nemo mafita, se yanzu da abu ya kwabe zata ce zata wani rike ni.

Ina shiga bedroom dina na saka lock na zube nan bakin kofar na cigaba da kuka, birgima kuwa ba kalar wadda ban yi ba, murya ta kam se da ta fashe ranar saboda ihu.

Hankalin Mama ya tashi ta taho bakin kofar ta shiga bugawa tana kiran sunana da fadin in bude sedai ko saurar ta ban yi ba, daga baya da ta takura min se na shiga yi mata rashin kunya da tsiwa

"Ni ki kyale ni, kawai zaki zo ki wani takura min da kiraye kiraye bayan da hadin bakin ki aka cuce ni, da sanin ki aka zalunci rayuwa ta, dan kawai an haife ni, ai dai da aka haife ni ba halitta ta aka yi ba, kuma kuma ai ba auren dole aka yi muku ba, amma dake ni an tsane ni shine za a aura min wanda bana so, to wallahi bana yi, ba zan yi auren ba, se dai ku gaji ku sa ya sake ni, babu inda zani ehe...yiiiiiii".

Rashin kunya sosai na shiga zubawa Mama, amma hakan be sa tayi fushi ta bar wajen kofar ba, lallashi na take yi na bude ta shiga, ita tsoron ta Allah tsoron ta kar na cutar da kai na.

Ranar wuni guda nayi ina abu daya, ba ci ba sha se kuka, se da aka yi magrib na ji da gaske ciki na neman hadewa yake da bayana saboda yunwa, ga yan hanji na da nake jin sun tattare waje ɗaya sannan na shiga toilet na sha ruwa me dumi, wai ni Aimah ce da shan ruwan toilet, saboda na ɗorawa raina wahala, wai kar na bude kofa Mama ta shigo.

Daga nan se na bude fridge na kwashi snacks, inda Allah ya taimake ni kenan dan ina ajiyar su, naci na sha da drinks, na dasa sabon kuka da ihu, ban yi shiru ba se da wani munafukin bacci ya sadado ya dauke ni, ranar ko sallar Asr, magrib da Isha ban yi ba.

Washegari da safe na dasa sabo, sedai ganin kamar ba'a damu ba yasa na shiga fashe fashe, duk wani kayan glass na dakin se da na fashe shi, mirror, perfumes da show glasses komai se da na fasa, asarar da nayi bata kanan kudi bace.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now