PAGE THIRTY NINE

510 17 1
                                    

Ouummey 039

Page 3️⃣9️⃣

____________________Suna nan zaune likita ya shigo yace musu ba'a san hayaniya, is either suyi shiru ko su fito waje, haka suka tsuke bakin su dan kam kowa baya san fita ya bar dakin.

Se da magrib tukuna mazan suka tafi sallah, matan kuma suka yi a daki, se kuma a wajen nurse din dazu suka ari pray mat dan Aunty Luba bata hado da shi ba, su Ya Salman na dawowa da suka ji haka Ya Najeeb ya bawa Aunty Luba key din motar sa yace taje akwai pray mat biyu da ya aje a ciki saboda sallan juma'a ta dauko su, haka kuwa aka yi, ta maida wa nurse tata ta mata godiya.

Aunty Luba ce ta koma gida saboda yara da se da Hajiya Yayah ta tuna mata ta bar su a school ko daukar su ba'a je ba, Allah ma yasa se six o'clock ake tashi, tana zuwa kuwa ta tarar driver ya aje su gidan Maman Ilham, ta shiga ta musu godiya ta kwaso su, tayi girki ta musu wanka ta canja musu kaya ta sake kwasar su zuwa hospital.

Se karfe tara Hajiya Yayah ta kora su, da kyar Aunty Luba ta hakura dan cewa tayi ita zata kwana a wajen ta, shi kam me gayya me aiki yana jin su yayi fumfurun fus abin sa, be ce a zauna ba be ce kar a zauna ba hasalima be nuna ya ji su ba.

Aka gama Ya Salman ya tarkata Aunty Luba da yara suka wuce, ya Najeeb da Aunty lateefa, Ya Farooq da Aunty saddiqa, Ya Ahmad dama be karaso ba saboda ba'a garin yake aiki ba.

Ɗaki ya rage daga Hajiya Yayah se Mama da Ya Masdooq, Hajiya Yayah ta dago zata yi magana kenan kira ya shigo wayar ta, ta daga ta duba se ta saki murmushi ta daga tare da yin sallama, aka amsa mata daga can tare da tambayar ta inda take, ta bada amsa da asibiti.

Mama ta kalle ta da tambayar ta waye, ƙasa ƙasa tace mata Baba ne.

"Wai waye a asibitin da kika kai dare har haka a can, ko kuwa kin manta da ni ne?".

"Ina ni ina mantawa da wannan dattijon arzikin, sirikar ka kuma yar ka ce Allah ya sauke lafiya".

Dan shiru yayi se kuma yace

"Sa'adah na da ciki ne dama?".

Hajiya Yayah ta girgiza kai kamar yana ganin ta

"Ba ita ba, dayar yar uwar ta ta ce".

Unbelievably Baba yace

"Kina nufin Nu'aimah ce ta haihu?".

Seda ta saki mutmushin da yaji shi ta cikin wayar
"ita dai Baban Aimah, yau Allah yayi ka samu jikoki daga gare ta".

Dake a da can takan kira shi da baban Aimah saboda kaunar dake tsakanin su.

Se Baba ya kara rike wayar da kyau

"Jikoki?, Biyu ne kenan ko uku ta haifa?".

"Biyu ne, aboki da mata".

"Kai Masha Allah, Masha Allah, alhamdulillah, wane asibiti ne, ya sunan sa?".

Baba ya tambaya cikin shauki, ba bata lokaci Hajiya Yayah ta sanar masa, yace gashi nan zuwa.

Tana aje wayar ta dubi Masdooq da ya jingina da jikin gadon ya lumshe idanun sa,

"Ya kamata kaje gida kayi wanka ka huta, kaga yau ka dawo daga tafiya akwai gajiya ga kuma Sa'adah, Safiyya zata zauna da Nu'aimah".

A hankali ya bude idanun sa sanin da shi take tun da babu wani namiji a dakin se shi, da gaske a gajiye yake, Sa'adah kuma ya manta da ita wallahi se yanzu da Hajiya Yayah ta ambaci sunan ta, amma duk da haka ba inda ze je ya kwana bayan matar sa da ƴaƴan sa na kwance a nan wajen daban, base iya ba dan ko ya tafi ma hankalin sa ba kwantawa ze yi ba, Hutu kuma ba ze taba samuwa ba kwanciyar hankali ba.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now