PAGE FIFTY TWO

386 16 4
                                    

Ouummey 052

Page 5️⃣2️⃣

______________________Ban canja kaya na ba dan babu bukatar hakan, yaran kawai na canja wa zuwa wasu daban, shima ya canja shigar da zuwa Ethiopian male attire, in kuka gan shi ba zaku taba cewa he belongs to Nigeria ba, yayi kyau matuka sosai.

Har daki naje nayi wa Nene sallama, na zata zata hana ko tayi ta tuhume tuhume se kuma naji tace se mun dawo, na sha jinin jiki na daga ganin yadda take cin goron ta hankali kwance, ba ko yaushe take ci ba shiyasa ba wanda ze gane ma se ya gan ta tana ci din.

Jiki a sanyaye na juya zuwa dakin Aunty A'i itama na mata se mun dawo, ita har bakin kofar falo ta rako mu tana a dawo lafiya sannan ta koma.

Motar Nene ce ya dauka, ni ban ma san sanda ya sa a ka wanke masa ita ba dan a aje take, da alama ya shirya wa fitar tun jiya.

Safar na baya, ni ina gaba kusa da shi rike da Airah, shi yake driving yana rike da Aiman.

Shiru babu wata hira tsakanin mu dan ni gari nake kallo ta window, shi kuma yana bin wakar "baby calm down" da ya kunna take tashi a motar kasa kasa, da hannu daya yake tuki dan dayan na rike da Aiman da tun farko na ce ya kawo na rike su gaba daya yaki, sa'i da lokaci yana dagowa ya kalle ni da ban ma san yana yi ba.

Tunani kawai nake yi na me ze faru in muka rabu?, Ze kwashi yarana ya kai wa matar sa, ni kuma a bar ni gaban Nene in cigaba da zama, ko kuwa ze bar min su.

A haka muka kai wani katon wajen shakatawa da ni ban ma taba sanin akwai shi ba, yayi parking a parking lot sannan ya dube ni yadda nake Len gurin ta window

"Zamu iya shiga?".

Na juyo na kalle shi se na gyada kai na bude door din side dina na fita, hannu na daya dauke da Airah, dayan kuma karamar handbag dina, Safar ma ta fito haka shima yayi locking motar sannan ya zagayo inda nake, hannu ya kai ze karbi handbag din na dube shi da tunanin me ze yi, se ya dage min gira yana sake neman karba, se na sake masa kawai, ya karba tare da gyara mata riko sannan ya nuna min hanya da ido.

Zuciya ta ba dadi na fara takawa zuwa cikin wajen, a jere muke haka ya daidaita takun sa daidai da nawa, duk da ma shi ba shi da sauri a tafiya balle garaje, komai na sa a nutse yake yin sa, Safar kuma na gaban mu.

Lokacin da muka shiga cikin park din sosai na bude ido ina kallo, gurin ya tsari matuka gaya, yayi kyau beyond tunani na, kayan wasa na yara ga sunan birjik, kai har ma da na manyan, ga kuma can gefe wani hadadden garden me cike da niima, kai hatta kamshin wajen na daban ne, a sanyaye kuma me kwantar da hankali, kamshin tsirrai na sake kara masa dadin shaka.

Wajen wasan yaran muka nufa, ya kira daya daga cikin masu kula da yaran suka yi magana, ban taba sanin ya iya Yaren su ba se ranar, suna gama magana ya karbi Airah daga hannu na yana mata wasa, ya kira wata mace me sanye da uniform irin nasa ta karbi Aiman, suka fito da wani karamin na'ura Ya Masdooq yayi scanning hannun sa a kai nima nayi suma suka yi se kuma suka bashi karamin plastic card, kana suka wuce da yaran har da Safar.

"Muje".

Wani kallon rashin fahimta na masa

"Muje ina?, Ina kuma zasu kai min yara na?".

"Nutsu mana, kin san dai ai ba zan cutar da su ba ko?".

Shiru na masa ina kallon sa a kage, so kawai na ke ya yi min bayanin ma'anar bada yara na da yayi

"Su ne masu kula da yaran a wajen wasan su, haka kuma in iyaye na da wani excuse din zasu basu yaran su kula musu da su zuwa mean time din da zasu zama available, za'a yi scanning fingerprint din su saboda tsaro haka kuma cameras na nan lungu da sako ta ko ina a wajen da ake iya ganin kome ke faruwa, su wadannan din in mutum ze bar yara a hannun su yana yin requesting tun kafin yazo kamar yadda nayi, company din su ke assigning din su ga duk wanda yayi requesting, so ki kwantar da hankalin ki, yaran ki ba bata zasu yi ba kuma ba abinda ze same su, now let's go ".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now