Ouummey 038
Page 3️⃣8️⃣
_____________________Hajiya Yayah na zaune tare da Mama dake rusa mata kuka se ga muryar Luba na kwala mata kira, ta kalli Mama da ta sa hannu da sauri tana share hawayen ta kana ta tashi ta fita Mama ma ta bi bayan ta dukan su cikin zulumin abinda ze saka Luba yin irin wannan ihun kiran.
A falon sama suka hade da ita, ko kafin su bude baki su tambaye ta se kawai tayi wani dan tsalle ta fada jikin su gaba daya, ta saka hannu ta rungume su dan abin ya zo mata a daidai samun su da tayi tare.
Gaba dayan su cikin fargaba suke tambayar ta Lafiya? ta saka dariya ganin yadda duk suka tsure, se kuma hankalin su ya kwanta jin dariyar ta, hakan na nufin ba wani abu mara kyau bane ya faru.
Hajiya Yayah ce ta janye jikin ta tana fadin
"Ji min wani rashin hankali, me haka zaki zo kina abu kamar wata karamar yarinya, duk kin sa hankalin mu ya tashi?".
Batare da ta saki Mama ba ta dago tana dariya"To kuwa hankalin ku ya kwanta, wannan babban gagarumar abin farin ciki ne da ze girgiza ku, shiyasa nima na kasa danne nawa farin cikin".
"Ba mu musha daughter, har kin sa na kagu naji".
Shiru tayi ta ja baya tana kare musu kallo, kana tace cikin karamin sauti
"Nu'aimah ta haihu, dazu aka mata aiki aka ciro yara biyu, namiji da mace".
Gaba daya se suka kame, kamar babu jini a jikin su, kamar bata ji ba Hajiya Yayah tace
"Me kika ce?".
Aunty Luba ganin reaction din su se taja hannayen su zuwa kan sofa ta zaunar da su kana ta zauna a ta gaban su
"Wallahi Aimahn mu ce ta haihu Mama, nima ban san tana da ciki ba dan be taba fada min ba, se kawai zuwa nayi na tarar da su tana nakuda shi kuma duk ya rikice, abin mamaki har Sa'adah ma bata sani ba se yau din, can na baro ta cikin mamaki itama".Shiru suka yi duka kowa na assimilating zancen, basu ankara ba suka ji Mama ta fashe da matsanancin kuka, duk se hankalin su ya koma kanta, Hajiya Yayah ta shiga lallashi ita kuma Aunty Luba tana tambayar ta me ya faru, cikin kukan take cewa
"Me na aikatawa yarinyar nan Luba?, Me ya tunzura ni har haka?, Shin ita ba yar Adam bace me iya yin kuskure?, Me yasa na manta hakan, ace ta dauki ciki tsayin watanni tara tayi fama da shi amma babu kulawar uwa?, Tun kwanakin baya nake mafarke mafarke da ita amma fushin zuciya ya hana ni neman ta, yanzu da ace mutuwa tayi a wajen haihuwar shikenan sedai a zo a fada min ta mutu?, Wayyo Allah na ni Safiyya, me nayi haka?".
Hajiya Yayah ma cikin damuwa tace
"Ba iya ke kadai ce kika yi kuskure ba har da ni Safiyya, tun ranar da na kai yarinyar nan gidan ta ban kuma zuwa na duba ta ba, hasalima so daya kawai na ganta a tsayin shekara ba wata biyu na auren su shima nan gidan suka zo, Allah ya sani ban rike ta akan komai ba haka ban yi da niyya ba, na bar su ne dan su sarara, na kuma basu space din da zasu fahimci juna ne, ashe ban sani ba hakan kuskure ne babba, da ace ina zuwa duba ta da na ga cikin jikin ta, amma shi ma da laifin sa, me yasa baze fada mana tana da ciki ba, wannan ai raini ne babba".
Ita dai Aunty Luba shiru tayi musu, a ranta tace gwara ta kyale su su gane kuskuren su, musamman ma Mama dan in ta rantse ba zata yi kaffara ba hukuncin ta se ya fi na kowa jijjiga Aimah, kasancewar shakuwar su da ita ba ta wasa bace.
Se da ta ga abin nasu ba me karewa bane ana ta koke koke da nadame nadame sannan ta mike
"Ni dai zan koma asibitin dan babu komai na bukata a can, se kun taho".
"Wane irin banzar magana ce wani se mun taho, dama mun san asibitin ne da zaki fadi haka, ni jira mu muje jor, tashi Safiyya".
Tashi Mama tayi har lokacin tana sharar hawaye, Hajiya Yayah ta daga waya ta kira Baba sedai bata ce masa ga abinda ke faruwa ba ta dai ce zata asibiti dubiya, be ja ba yace a dawo lafiya.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...