PAGE SIX

195 10 0
                                    

Ouummey 006

Page 6️⃣

__________________Dariya na fashe da ita bayan fitar su, na dade ina kyakyatawa kamar ba ni ce cikin damuwa ba kafin na samu na tsagaita, sedai da na tuno irin yadda Sa'adah ta fita a fusace hankali a tashe se in sake fashewa da dariya, ba su s an duk burga ba ce nayi musu, ko daya a abinda na fada ba wanda ya faru, ban ma san yaya aka yi ya karbi matar sa ba, na dai san se da suka shekara tana zaman jiran sa kafin ya hakura da guje gujen da yake yi ya karbe ta, shima a bakin Mama nake ji da take fada cikin gore goren ta na nayi asarar miji.

Yar ta kuwa, ban da Sa'adah bata da kai ai be kamata ta yadda da ni ba, duk da Mama mahaifiya ta ce amma shi kuma ai kanwar mahaifiyar sa ce shakikiya, dan haka saka sunan Safiyya wa yar ta princess ba shi da alaka da ni, dan ko Barka kunya da gudun maganganun mutane basu bar ni na zo ba.

Su wai a tunanin su da zasu fadawa Aimah ciwo ne ta zuba musu ido, lallai har yau da sauran Sa'adah a sanin wacece ni, dan ma tayi Sa'a tazo a lokacin da ruwa ya daki babban zakara.

Da wannan nishadin na karya, kar kuyi mamaki dan nace nishadi, ni din a da kafin duk wani tashin hankali ya kutso rayuwa ta me tsokana ce, faran faran da saukin sabo, da dan karan surutu da iyayi, tun bayan faruwar komai kuwa se duk wannan halin nawa yayi sanyi, shiyasa yanzu nake jin dadi abina.

To fa, aka ce wai ba fada da malam ba daren, yau kam na jigatu dan abincin ranar da ake dan yafata min shiru har bayan Isha kafin a kawo min na dare, wato dai na yi na abincin rana na.

Haka na jawo na shiga ci zuciya ta ba dadi, nan da nan na tashi da dan abincin dama ba wani na azo a gani bane, a wajen na cigaba da zama na kasa tashi na wanke hannu, tunanin yadda zan yi kan lamarin abincin nan nake dan bana jin zan iya hakuri da jurewa tafiya a haka, dole se nayi wani abu.

Amma wani abu kamar me kenan?, Me gidan dai tun zuwa na gidan yau kwana uku da yini daya ban taba sa shi a idanu na ba se dai na ji motsin shigar sa da fitar sa, Hajiya Yayah?, No Hajiya Yayah is not a good option Dan ban manta nasihar ta ba a ranar da ta rakoni, wadda ta karkare da yabon Sa'adah da fadin sun shaidi kyawawan halayen ta, na san ko na fada ba yarda za'a yi ba, watakila ma ace ina neman ta da tashin hankali tun da ni nayi kaurin suna.

Ban da su kuma wa nake da shi a yanzu?, Yayye na sun sallama ni, Mama kuwa tun kafin na bar gidan muka fara da ita dan ban manta dukan da ta min ba ranar da aka daura auren, BA NI DA KOWA yanzu kenan dan zan kaiwa kuka na!.

A hankali na ja majina ina kokarin tsaida zubar hawayen da ban san da su ba se da na ji damshin su, lallai a rayuwa duk dan da yace ba za'a fada masa ba yana tare da wahala da tarin kalubale dan kuwa rayuwar sa ba zata yi albarka ba balle ayi zancen kwanciyar hankali, ni din nan babban darasi ce da misali me girma ga ire ire na masu taurin kai, kafiya, tsayayya da kuma rashin hakuri.

Da kyar na tsayar da hawayen na share su daga kunci na kana na tashi na wanke hannu na koma na zauna, tagumi hannu bibbiyu a kunci na ina tunano rayuwa ta ta baya cikin tsananin begen da ma ana juya hannun agogo ya koma baya.

******Sa'adah*****

Gyara dining din da suka gama cin abinci tayi ta wanke komai ta mayar inda ya kamata kana ta shiga dakin ta dan yin sabon wanka kafin ta tadda sanyin ran ta.

Tana shirya wa tana tunanin maganganun da suka yi da Zee yar uwar ta, irin rarrashi da ban bakin da ta mata wanda ta san ba dan shi ba da tuni ba wannan zancen ake ba.

"Kar ki sake ki bawa duk wani banzan kalaman ta damar yin tasiri a ran ki, komai da ta fada karya ne, burga ce zata miki irin ta ta dan ai dama kin san ta, ban da yanzu ma bata bari a fada mata tayi shiru, shine halin ya motsa take neman bata miki rai ta hana ki kwanciyar hankali da mijin ki, tana bakin cikin ko kallo bata ishe shi ba, da ita da shara duk daya dan ai kin ce be taba nuna ya san da ita a gidan ba, se ma kayan ta da Hajiya Yayah ta hado shi fa su ne ya bawa yar aiki ta kai mata, ko ba haka ba ne?".

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now