Ouummey 025
Page 2️⃣5️⃣
_____________________"kace I should have consider my self first?".
Farooq ya gyada kai, se kawai Masdooq ya mike ya karasa gaban console ya fara zare links din hannun rigar
"Ai shine abinda nayi, that's what I did Farooq".
Cikin mamaki Farooq yace
"I didn't get you".
"Aimah ce Ni din da kake magana, and I consider her first that's why I choose her happinesses as my first priority".
Karamin tsaki Farooq yayi tare da fadin
"Look guy, jokes aside, ni magana nake maka da gaske, You're the best choice for Aimah, you deserve her Masdooq, soyayyar da kake mata should not go in vain ka fahimce ni".
"Kai ne zaka fahimce ni Farooq, ban da wani farin ciki da ya wuce na Barbie, dariyar ta itace tawa, farin cikin ta shine nawa, walwalár ta itace key to mine haka zaman lafiyar ta means mine, akasin haka kuma shima yana nufin tashin hankali na, ko da kace my love for her shouldn't go in vain, ai be je in vain din ba, tun da gashi ya bani damar bata muradin ta, and kake cewa i deserve her, wannan a idon ka ne, in her eyes bata ga wannan dacewar ba dan haka Nima ban ganta ba".
"You're not serious, zan je nacewa Abba he should over look wannan maganar, sam bata yi ba".
"Zaka batawa kan ka lokaci dan till eternity zabin Barbie would always be mine, kaga kuwa hakan na nufin ina kan ra'ayi na".
Kallon shi kawai Farooq ke yi cikin takaicin sa da bacin rai, tare yake da Masdooq a inda ba su da kowa, ya fi kowa sanin irin tsananin so da kaunar da Masdooq have for Aimah, tun tali talin yarinta, tun kan ta san kanta har zuwa ta fara zama mace, se yanzu kuma da ta gama zama yaddaa ya kamata se wani ya dauke ta ba dan uwan shi da ya sha kwana ido biyu saboda ita ba?.
No! Ba ze yiwu ba, ba ze bari haka ta faru ba, wallahi in har yana numfashi Aimah have no husband other than Masdooq, ba kuma dan iya Masdooq kadai ze yi wannan fighting din ba, har da dan ita kan ta Aimahr, ya fi kowa sanin Masdooq da irin qualities din da yake dashi, duk matar da ta auri Masdooq ta samu rabin addinin ta, he can swear akan hakan, dan haka ba ze bari kanwar sa tayi loosing this precious gem din ba.
Da wannan tunanin Farooq ya ja wa Masdooq kakkarfan tsaki me tsayi sannan ya fita daga bedroom din yana masa banging kofar, duk da he's not in the mood amma se da Murmushi ya kwace masa, ya sani dan ran sa ya ɓaci Farooq yayi tsakin dan ya fi kowa sanin ya tsani tsaki, haka ma banging door, shi kuma shiyasa yayi dan ya bata masa rai kamar yadda ya tabbatar ran Farooq din a nace yake yanzu.
"He'll never understand".
Masdooq ya fada yana nufar toilet a hankali, duk wanda ze so masa kasancewa da Barbie barin shi kan sa ne, dan hakan burin sa ne na atleast over 17 years back, Amma kuma neman cikar muradi da burin sa ba ze sa ya tauye ta ba, she've the right ta zabi life partner din ta, she've the audacity tace tana san wannan bata ra'ayin wannan, ba kuma hakan ze sa ya kalle ta da wani duba ba bayan duban da ya saba mata, sedai yana tausayin kan sa, dan son Aimah be shige shi da wasa ba!.
Da haka yayi wanka ya fito ya saka kayan bacci, ko abinci be nema ba ya fada bed, se ya kai hannu ya lalubo wayar sa ya budo hoton ta, kyawawan fararen haƙoran ta a bude cikin yin dariya, haka hannun ta ya sha zanen lalle baki da ja.
A hankali ya shiga sauke ajiyar zuciya akai akai kamar wanda ya sha kuka, se kuma ya daga wayar ya kai saitin bakin sa ya sunbata, wadda sunbar ta fito daga can karkashin zuciyar sa ne.
Da hoton honeybun din sa a hannu bacci ya sace shi, maimakon wayar ta fadi se ya kankame ta a kirjin sa kamar Aimah din ce a wajen.
Hankali na be kwanta ba se da safe da na kira yace ba komai bane, kan sa ne yake ciwo lokacin, amma ynx all is good dan ya sha magani tun jiya kuma ciwon kan ya tafi.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...