PAGE TWENTY SEVEN

307 14 9
                                    

Ouummey 027

Page 2️⃣7️⃣

__________________Ni kuwa tuni na bawa Abba daddumar sa na nufi motar da sauri, bangaren driver ba bude ina kiran sunan shi, se na ja baya da sauri ganin ya Farooq, na fara zare ido dan na san se yayi min bala'i amma ga mamaki na se ya sake min mutmushin da yasa kamannin mu suka fito, rashin sabo ya sa da sauri na shiga gaishe shi, ya amsa min se na ja baya ina kallon daya side din da Ya Masdooq ya fito.

Ina son in je wajen shi amma ina tsoron ya Farooq, se na juya zan koma wajen Abba se kuwa ya kira ni

"Barbie".

Na kalle shi se ya min alamar na zo, da kuwa sauri na nayi wajen shi, ina zuwa tun kan na gaishe shi ya katse ni da fadin

"Kin yi kyau".
Se na samu kai na da lumshe ido cikin farin ciki da jin dadi, ban san me yasa ba in dai ya yabo ado na se in dinga ganin kyan adon fiye da baya ko da kuwa na san nayi kyan.

Tare muka jera zuwa wajen Abba batare da na iya gaishe shin ba, muna zuwa Masdooq ya tsaya gefen Abba bayan ya duka har kasa ya gaida shi, ya sa na tsaya gefen Abba bangaren hagu ya ciro wayar sa ya bawa Ya Farooq yace yayi mana photo, aikuwa ya mana masu kyau biyu, Abba na matsawa na matsa jikin Ya Masdooq na bawa Ya Farooq waya ta cikin dari dari nace ya mana pics, na zata ze zage ni yace na raina shi se naga kawai ya karba bakin sa dauke da mutmushi yayi mana har biyar se ya miko min.

Da zasu tafi se na karbi wayar Ya Masdooq nace zan tura pic din da aka mana da Abba se yace nima in tura masa wanda aka yi mana mu biyu da kuma photos dina masu yawa, na amsa shi na karba na koma cikin gida su kuma suka tafi masallaci.

Ina zaune a falo ina turawa se ga sallamar Aunty Luba, na tashi na rungume ta ina ihu se kuma na karbe Mimi dake hannun ta, kuka zauna muka bude sabon fejin hira tare da Mama da ta fito.

Ranar kin yin girki nayi nace nayi gayu, suna ta tsokana ta se Aunty Luba ce tayi, ana saukowa masallaci se ga Abba da tawagar ƴaƴan sa maza, abin mamaki se gashi suna kiran na taso muzo muyi photo, abin daure kai duk hoton da za'a yi se an yi da ni da Ya Masdooq, kuma a tsakiya ake samu, a'a a jima kadan mana, ba se ga Baba da Hajiya Yayah ba, haka ka yi ta dauke dauken pic, dake dama dabi'a tace se ga shi ban ko gaji ba, ana gamawa da iyaye suka shige suka bar mu muna tayi, mune har garden.

Kuma ko da na riƙe ya Masdooq be kalle ni yada yake yi da ba, se ma sake riko ni jikin sa da yayi muka yi ta pics, har da wanda ya duko yayi pecking goshi na, style kala kala, kuma jiki na be taba cakuduwa da na wani namiji ba ko da ba Ya Masdooq din be irin na ranar.

Ko da aka gama pic nan muka yi zaman mu a garden leaving su Mama a cikin gida, ana gama abinci me aikin mu da ta su Hajiya Yayah da aka taho da ita su suka dinga bi suna rabawa, nan cikin garden din muka ci abincin, ba mu fito ba se da aka kira Asr, mazan suka tafi masallaci, mu matan muka yi ciki.

Ni, Aunty Luba da matar ya Najeeb Aunty Labiba muka yi sallah a daki na, Hajiya Yayah kuma na dakin Mama, su Abba sun fita suma.

A dakin muka yi zaman mu bayan mun yi sallah, gaban mu cike da snacks da juices muna ta hira, suma mazan suna bangaren mazan gidan sun baje a parlo suma snacks da juices kala kala a gaban su a wadace.

Gathering din be tashi ba se after magrib, suna dawowa daga sallah Ya Salman ya dauki Aunty Luba suka tafi, Baba dama su suka fara wucewa da Hajiya Yayah, se Ya Najeeb da Aunty Labiba, Ya Ahmad kuwa dama tun Asr ya koma school, dan yana da exam Saturday morning.

Ya saura ni da Mama da Ya Masdooq, shi kam yace se yayi dinner ze tafi, aikuwa yana dawowa daga Isha tare muka yi dinner dashi da su Abba a falon Abba dan nan muke dinner kullum, sedai In bazan yi tare da su ba in bana jin cin abinci da wuri.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now