Ouummey 049
Page 4️⃣9️⃣
_____________________Har na bude baki zan yi magana se kuma na fasa, internally nake fadawa kaina _'ke Aiman, daidaita kan ki da nutsuwar ki mana, kin manta waye a gaban ki ne?, Me kike tunanin ze miki da zaki rude haka?, Wa ya sani ma ko maganar yara ze miki ke kuma kika tafi wani tunanin da da zai ji se ya kwasa miki mari_'.
Se na shiga daidaita kai na, na haxihe firgici na da rudewar ganin sa, kana na danne tsallen murna da zumudin ganin sa da zuciya ta ke yi na gyara tsayuwa ta tare da nema bakin bed na zauna
"Ina kwana baban princess?".
Na gaida shi can kasa fuska ta ba yabo ba fallasa, be amsa ba se da ya tako shima ya zauna gefe na har kafafun mu na gugar na juna, na dago na dan kalle shi kana na mai da kai kasa kamar wadda ta ke gaban suruki.
Gaba daya ji nake kamar ina tare da stranger ne ba wai Ya Masdooq sweetheart dina ba, ya kafe ni da ido yana nazari na, ganin ba shi da niyyar tafiya se nace
"Nenen na falo, twins kuma na wajen Aunty A'i a daya dakin ".
A sannan ne ya ka da baki yace
"Na ga Nene sanda na shigo amma ba wajen ta na zo ba, twins ma ba wajen su na zo ba shiyasa ban neme su ba, I'm here to see my wife, hug her and kiss her, am here to Express how badly I miss my wife".
Cikin mamaki na dago ina bin shi da kallo, matar sa fa yace yazo gani, to ko dai sun yi da Sa'adahn zata zo nan ne shine ya biyo daga wata tafiyar?, Amma kuma ta zo nan tayi me?.
Take wata zuciyar ta bani amsa da _'Kakar mijin ta ce fa, maybe zata zo gaishe ta ne'_.
Da wannan tunanin na dago kai na dube shi cikin tabbatarwa
"Amma kuma ai bata zo ba, maybe kun yi sabani ko se zuwa anjima zata karaso".
Na bashi amsa zuciya ta na min daci, sedai ban bar abin ya dore ba na kore shi sanin ai nima na ce ba zan koma masa ba, then kishin na meye.
Ya Masdooq ya kalle ni tare da sakin tattausan murmushi yana rayawa a ran shi wato dai wautar autanci ba ze taba barin Aimah ba.
Ban ankara ba se ji nayi yasa hannu ya fizgo ni jikin sa, na ware idanu na akan fuskar shi shima se ya ware min nasa, ya subhanallah ai da sauri na rufe nawa kirji na na dokawa, ya sunkuyo da fuskar sa kan tawa ya hade goshin mu waje daya, haka dogon hancin sa na gogar nawa
"Wace matar ce muka yi sabani bayan ta gaba na, watan ta bakwai fa a kasar nan yanzu, to ina ta je da zan jira ta har ta karaso?".
Duk yadda kasalalliyar muryar sa ta kassara min jiki haka na bude baki nace
"Wai kana nufin ni?, Ko dai wata matar gare ka ban sani ba?".
Cikin sigar rada ya rage Muryar sa
"Babu mace da zata yadda ta auri mijin nace, dan haka ke din dai nake nufi Barbie".
A raunacen da ya kashe min laka na janye jiki na na ja baya na zubawa fuskar sa ido, yayi mulmul abin sa ya kara kyau, kwarjini da haiba, ga sajen shi da ya zagaye kyakkyawar fuskar sa da yana cikin abinda nake so a tare da shi
"Abin mamaki, ko da dai ba lallai ya zama na mamaki ba, ban taba zaton after all that happened zaka dube ni a matsayin kanwa ba, sedai yau ka karya ta hasashe na, na gode sosai".
Da rashin fahimta ya kalle ni se kuma ya furta da bakin sa
"Ban fahimci zancen ki ba".
Se da na sake kwarara kai na sannan na iya cewa
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...