Ouummey 002
Page 2️⃣
_______________ Kallan dakin nake yi fuskata dauke da wani yanayi mara fassaruwa, dakin baki ne me ɗauke da ciki da falo, falon karami ne sosai dan one and two sitters kawai ya dauka, se karamin fridge dake gefe.
A hankali na taka na zauna kan kujerun, wanda alamu ya nuna ana gyara dakin koyaushe dan a tsaftace yake babu ƙazanta.
Na dade zaune a wajen kafin nan tashi zuwa bedroom din, nan din ma karami ne dan kuwa gadon kwanciyar mutum daya ne baze ci mutum biyu ba, shima nan din a gyare yake sedai babu bedsheet a kai, na wuce toilet shima na duba, shima dai ba laifi duk da be min yadda nake so ba amma dai ba ƙazanta.
Ban fara karambanin wankewa ba na koma falo na zauna tun da ban san matsayi na ba a gidan, nan din kamar wajen zaman wucin gadi ne kafin me gidan ya dawo ya san yadda zeyi da ni kamar yadda Hajiya Yayah tace.
Zama nayi na zuba tagumi ina tunanin rayuwa, a yadda na budi ido na taso ban taba tunanin rayuwa ta zata juye irin haka ba, ban taba tunanin akwai wata ƙaddara da zata ratso tayi tafiyar yaji da gata na da jin dadi na ba, se gashi tashi daya komai da kowa ya watse, abin da na fi karfi a baya yanzu ya fi karfi na, rayuwar da nake ganin wasu a ciki na tausaya musu se ga shi nima na tsinci kaina a ciki dumu dumu.
Ban san kuka nake ba se da na ji digar sassanyan ruwan hawaye na kan hannu na dake aje kan cinya ta, ban iya na daga hannu na share ba saboda hayaniyar da naji na tashi a compound.
Kamar munafuka haka na tashi na daga curtains din dakin ta bangaren compound, a lokacin ne na fahimci me ke faruwa dan kuwa SA'ADAH ce wasu mata biyu dan ban gama shedawa ba suka riko, irin kukan da take yi seda ya sa naji wani dam a raina, haka kumq kirji na ya shiga dukan uku uku.
A falo suka zaunar da ita kan sofa suka zagaye ta suna bata hakuri ita kuma se kuka kawai take yi, da kyar ta iya bude bakin ta ta fara magana muryar ta na fitar da sautin kuka haka kuma tana rawa
"Me yasa sai ni? Me nayi wa Hajiya Yayah me zafi da ta yanke min wannan zazzafan hukuncin? Aunty A'i me yasa duk kusancin ka da mutum da kaunar da ze nuna maka wataran se ya fifita nasa a kan ka duk min girman zunubin nasan?, Ina nan nan gidan yarinyar nan ta tozarta Ya Masdooq, a gaban kowa ta zabi wani ta bar shi, a kan ta wane irin wulakancin da tozarci ne ban fuskan ta ba Aunty, na sha wahala matuka da Masdooq kafin ya manta da ita, na yi kuka har idanuna suna neman samun matsala kafin na samu Masdooq ya dube ni, iya iyawa ta kuma faranta ran Hajiya Yayah nake, da dukkan zuciya ta nake kaunar ta kamar uwa ba wai uwar miji ba, saboda ta nuna min gata, ta tsaya min a lokacin da ba wanda ze iya, amma me yasa yau kuma take neman rusa fadin ciki na, shin me na mata na ba daidai ba, a ina na kuskure, dan Allah Aunty ku tambayar min ita zan gyara wallahi, zan kuma kiyaye maimaita hakan amma dan Allah su rufa min asiri su raba auren nan, wallahi ba zan iya jurewa ba, ban da karfin zuciyar da zan ga Masdooq na juya baya gare Ni, zuciya ta bugawa zata yi, innalillahi wa inna ilaihi rajiun".
Sa'adah ta shiga jujjuya kai tana kuka me cin rai, ni dai ina daga daki ina sauraren su, kirji na yayi min nauyi haka kuma ina jin kunyar daga ko curtains ne na kalle su, a lokacin ne naji Muryar ta me sanyin nan ma'abociyar nutsuwa da kamala, muryar ƴar uwa daya tilo da na dauka jigo ga rayuwa ta, yar uwar dake iya hana cikin ta abu ta bani, yar uwar da ta tsani ganin damuwa a kan fuska ta balle aje ga hawaye, se dai a yau ba'a gare ni ne ta kasance me share hawayen ba, ga KISHIYA TA ne ta zamo me lallashin, tausasawa tare da shawarwarin ta masu dimbin fa'ida da a baya na kasa bude ido na kalle su balle nayi tunani har na gano girman fa'idar su har se da na kai kaina na baro.
"Dago nan ki dube ni SA'ADAH, kar na kuma jin ko da wasa kin ce Hajiya Yayah bata ɗauke ki ƴa ba, kar na kuma jin ko da kuskure kin ce wai Hajiya Yayah na kokarin rusa fadin cikin ki, da dukkan zuciya ta nake sanar da ke Hajiya Yayah ta dauke ki fiye da ƴa, tana kuma kallon ki da dukkan so da kaunar da uwa zata yiwa ƴar ta, sedai a rayuwa kowane bawa da irin tasa ƙaddarar, haka kumq jarrabawar mu baze taba zama daya ba kamar yadda muka banbanta ta fuskar halaye da ra'ayoyi, ina so ki sa a ranki ba Hajiya Yayah bace ta nemawa mijin ki aure, Allah ne ya ƙaddara ƙaddarar su a sarke take da ta juna, bana kuma son ki saka hakan a ranki balle ya dame ki, ke din macece me daraja me kuma kima, ba'a iya idanun mu mu yan uwan ki ba har da idanun mijin ki, mijin ki na son ki soyayya me tsafta, hakan kuma ya samo asali ne daga kyawawan halayen ki da ya fuskan ta, tarbiyyar ki da nutsuwar ki tare da biyayya sun sama miki gurbi me matukar girma da zurfi a rayuwar Masdooq, ba zan so kiyi sakarci ko sakacin da zaki rasa su ba. Bari in fada Miki, duk yadda kika dauki rayuwa haka zata zo miki Sa'adah, dan haka ina so ki sa a ran ki karin auren mijin ki ba komai bane ba, ba kuma dan baya san ki bane, haka kuma ba dan kin gaza ba, sedan ƙaddarar shi kenan haka kema taki kenan, ki kuma sa a ran ki karin auren shi baze taba rayuwar ki da shi ba ta kowace fuska, ki cigaba da kyautata masa, ki cigaba da faranta masa da dukkan iyawar ki, kar ki sake Kice zaki tashi hankalin sa saboda haka, abinda mu mata mu ka kasa fahimta shine, daga lokacin da kika rika bori da tashin hankali kan namiji ya kara aure, daga lokacin kika fara zubar da damar ki, dan tun yana lallashin ki yana ta taki har se ya gundura ya fita harkar ki, amma in kika nuna baki damu ba, kika danne kika shanye wannan dacin wallahi shi kan sa namijin shakkar ki ze dinga yi, dan be san me kika boye a ran ki ba, kullum tunani da zullumin sa shine me zaki yi ko me zaki ce, hakan kuma ƙarin kima ze jawo Miki, dan duk yadda yake son amaryar ko yake dokin ya zaki ba za bata damar taka ki ko raina ki ba.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...