Ouummey 055
Page 5️⃣5️⃣
Last page
____________________Iya dubawa ta na rasa wa zan nufa da wannan batun dan haka na hakura na kawo ido na saka masa, sedai na fara janye masa, ba kamar baya da in ya taba nu nake biye masa ba, yanzu da ya kawo hannu nake gocewa, in kuwa ya rike ni na dinga neman zame wa kenan.
To tsakani da Allah kan zan cigaba da yadda yana gwama min lissafi yana bari na cikin wani hali, saboda shi ya san yana da wata matar da ze iya zuwa ta magance masa damuwar sa, to ni ma kam na dena yarda.
Wannan janye masan da na fara yana damun sa, duk da be fito fili ya nuna ba amma in na kwace daga jikin sa fuskar sa na nuna damuwa, ban kuma taba nuna na gani ba, so nake yi ya gaji ya magantu da kan sa, daga nan ni kuma se in amayar da abinda ke raina.
Kun san lamari irin na shaidan, wannan halin da Ya Masdooq ke gwada min se yake tunzura zuciya ta, yana sa min sake sake cewa ai dama Ya Masdooq baya so na yanzu, tausayi na da neman ganin ya farantawa iyayen mu yasa ya dage ya dawo dani, ba wai dan kauna ba.
So daya dai matar sa yake yi wa, ita yake kauna shiyasa a idanu na har rawar jiki yake yi in ze koma mata, ranar da nayi wannan tunanin wuni nayi ina kuka, kuma dake ranar ya bar gida na se ban samu me rarrashi ba, na yi kuka iya kuka har idanu na suka kumbura, zazzaɓi ya rufe ni me hade da ciwon kai, na kwana da shi na tashi, be sake ni ba se da rana da na daure na sha maganin da na tsana.
Wannan ɗan zazzabin da kuka banzan tunanin da na kakabawa raina yasa har faɗawa nayi a kwanakin.
Ranar da ya dawo gida na kuwa ba wani tarba ta daban, ba wannan murna da rawar jikin da nake yi, duk gaba daya se ya sha jinin jikin sa, damuwar yanayi na yasa fara'ar da ya shigo da ita ta bace.
Na dago na kalle shi lokacin da yake tambaya ta me ke damuna, ban san me zance masa ba, damuwar yadda ka ɗauke ni ba mace ba zan ce ko kuwa cewa zan yi damuwar rashin soyayyar ka gare ni?, Se kawai na kada kai nace ba komai.
"Kin ga yadda kika rame kuwa a kwanaki biyu kadai Barbie? Kuma kice min ba abinda yake damun ki kiyi tunanin zan yarda?".
Bana san ya matsa min da tambayoyi se nace
"Nayi zazzaɓi da ciwon kai ne jiya da shekaranjiya, seda na sha magani sannan na samu sauki".
Ya na kokarin rungume ni a jikin sa yace
"An so very sorry, kin yi rashin lafiya har kin tashi ban sani ba, kiyi hakuri, but please ba fata nake ba amma duk sanda kika ji ki ba daidai ba ki sanar min ko da kuwa ba a gidan nan nake ba, lafiyar ki sama yake da komai kin ji ko?".
Zame wa na shiga yi dan bana san wannan nanike min din da yake, tun da baya buƙata ta a matsayin mayar sa then why the teasing
"Insha Allah, ban kira ka bane kar na katse muku nutsuwar ku ko na shiga lokacin ku".
Irin yadda words din suka min ɗaci a harshe Allah ne kaɗai ya sani, amma ya zan yi tun da wanda nake yi dan shi be san ina yi ba.
Ranar duka ban bari ya taba ni da wani niyya ba, kissing ɗin da ya maida kamar wani farilla na ki yarda, hatta rungumar da yake min in zamu yi bacci yau duk na hana hakan, yana sake miko hannu a karo na uku dan ja na jikin sa na ture hannun nace
"Pleaaaasseee".
Ban san me ya gani ba da ya kyale ni sedai ya matso dab dani har muna shakar numfashi juna, hakan kuma yana affecting dina, se na juya masa baya a hankali kuma na matsa can ɗaya edge din gadon, ina jin idanun sa a jiki na shaidar kallo na ne yake yi, sai dai ya zan yi, be bar ni da wani zabin ba bayan wannan.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...