Ouummey 017
Page 1️⃣7️⃣
__________________Aunty Luba kuwa ba ni da aminya sama da ita, duk inda muka je se na saka Ya Ibrahim ya min hoto dan na nuna mata, duk kuma abinda na gani se an siya mata, haka duk wanda naci se na rage mata, shakuwa ce sosai a tsakanin mu, haka kuma ita da ya Ibrahim kadai ke sa ni nayi abinda ban yi niyya ba ko na bar abinda basa so.
Se a wannan shekarar ne su Ya Masdooq suka zo gida, da shaidar su na kwalin degree dukan su kuma first class, Ya Masdooq is a aerospace engineer, where as Ya Farooq is an Architect, murna sosai aka yi amma ban da ni, dan kuwa dawowar su yasa rayuwa ta cikin wani yanayi.
Ina bala'in tsoron ya Farooq har fiye da ya Salman, dan kuwa ranar da suka dawo se da ya zane min jiki na tass da cajar waya, dan na bi Ya Ibrahim dangin Maman sa tun safe ba mu dawo ba se tara, aikuwa ya sa ni a daki ya zane bayan ya rufe kofa, wannan yasa aka rasa me ceto na se hayaniya da Abba da Mama ke yi kan ya bari amma be kyale ni ba se da ya ga ina numfashi da kyar.
Tun daga ranar kuwa nake bala'in tsoron sa, in har suka kwana a gidan mu ranar ba ni ba zuwa wajen Ya Ibrahim, shi kuwa ya Masdooq ba shi da hayaniya, magana ma bata dame shi ba, sedai baya hade fuska, amma fara'ar sa ta da ta ragu.
Nikam bana shiri da mutane marasa magana dan ni din magananniya ce, magana rairairai kamar Radio, haka nake in nan fara zuba, wani sa'in se an dakatar da ni.
Sedai shiga dari fita dari ya Masdooq se ya kawo min tsaraba, ice cream, chocolate, biscuit ko kuma kayan wasa, wannan yasa nake shiri da shi sama sama, rashin maganar sa ke bata min rai da shi, dan se in zauna ina bashi labari amma sedai yai ta min murmushi ko yai ta kallo na, in kuma tambaya ce se dai ya gyada min kai ko ya girgiza, se ya ga na bata fuska sannan yake magana, shima q hankali kuma can kasa, sedai Muryar sa na min dadi, fiye da duk wata murya da nake ji ta maza, kai har ma ta wasu matan, wannan yasa nake yawan takura masa yayi magana.
A zaman wata biyun da suka yi shakuwar mu da ya Ibrahim ta dan ja baya saboda ya Farooq, da kuma samun ya Masdooq da nayi, shima yana kai ni yawo, ya siya min duk abinda nake so, sedai baya magana, wannan yasa nake missing ya Ibrahim sa'i da lokaci, musamman in zan bada labari, sedai shima mun shaku da shi, ranar da zasu tafi duk da ina farin cikin tafiyar ya Farooq amma na sha kukan rabuwa da ya Masdooq.
Dake Baba ya sake nema musu masters shiyasa suka juya, wannan karon Australia suka yi, nayi kewar ya Masdooq na dan wani lokaci kafin kuma na ware na sake jonewa da ya Ibrahim, lokacin Aunty Luba tuni ta fara University tana karantar Education biology, an kuma saka ranar ta da ya Salman da ya bayyana yana kaunar ta, itama kuma babu jaq ta amince.
Wata biyar da aka saka na zuwa aka yi auren su, na sha kuka ranar da za'a kai ta, ba yadda bata yi dani ba kan mu tafi gidan tare naki, saboda sanin wane ya Salman, a gidan mu ma ya ba kaya da shi balle gidan sa.
Wannan yasa ba ko yaushe nake zuwa gidan Aunty Luba ba, sedai na dauke wayar mama mu cinye mata kati, ko kuma muyi vedio call.
Lokacin ina shekara sha hudu, tun a lokacin duk wanda ya kalle ni se ha kara, kyakkyawar matashiyar budurwa, me wani irin skin color dake fizgar hankali, attractive face da kuma tsiwa ta zuwa zubin dirin jiki na da ya fara bayyana ta kugu na ke jan hankalin jama'a kai na.
Tun a lokacin bani da burin karatu, abu uku nake matuƙar so da kauna sune makeup and fashion design, se kuma girki, ina matukar son kwalliya, kamar yadda nake son dinki, ba wai ni nayi ba, a'a naga ana yi na burge Ni, kwalliya kuwa ni din nake so naga ina yin ta, shiyasa tun ina ten years na mallaki make up kit na kai na, yanzu kuwa baka taba raba fuska ta da kwalliya, ko da kuwa zan je makaranta ne se na yi nude make up, tun ana min warning da fada har aka bar ni, girki kuwa dole nasa Mama ta saka ni catering schools kala kala, da na gama wannan in naga wata se na tubure an saka ni, shiyasa na kware sosai a fannin girki, yana daya daga cikin favorite hobbies Dina.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...