Ouummey 020
Page 2️⃣0️⃣
____________________Haka kuwa aka yi, Baba ya kira ya Masdooq a gaba na ya bashi umarnin nemo shago me kyau da da zama business wise a siya, take kuma amsa masa.
Farin ciki ya cika ni matuka, na tafi daki da gudu cikin jin dadi na kira Abba na sanar masa, ga dinga tsokana ta da kaga ƴar Baba ni kuwa ina ta dariya baki na ya kasa rufuwa, na kira Mama take cewa ai ta ji mu da Baba, itama ta nuna farin cikin ta, the next da na kira Ibrahim ne.
Na san zaku ce ina yake ban gayye ce shi walima ko in ce partyn su Ya Masdooq ba, na gayyace shi amma se yace min in Yi hakuri baze samu zuwa ba, yana da tafiya ranar.
Ban ji dadi ba amma na taya shi da addu'a na shiga harkoki na, wayar na ta ringing amma ba'a dauka ba, miss call uku se na kyale shi da tunanin baya kusa ne, whenever ya gani ze kira ni.
Who next zan sanarwa, guess who? Aunty Luba, if not her not who?.
Aikuwa har ma tafi ni farin ciki, vedio call ta kira ni bayan ya kashe kiran da na mata, muka zauna muka dinga tsara yadda tafiyar da komai na shagon ze kasance, nan tayi sugessting wata kawar ta, tace tun suna school itama haka take da son makeup, yanzu haka she's way close to zama professional, sedai ita a gida take yi, so hiring her would be a good choice.
Aunty Luba na nata business din da Ya Salman ya bata jari, dan duk da ta gama school ya hana ta aiki yace baya so, se ya bata jari take business, tana shigo da duk wani high class textiles na mata, a gida take Business din se kuma online, amma yanzu tana kokarin bude shago itama.
Sedai kafin nan muka yanke shawarar za'a dinga kai kayan can, tun da waje ne na jama'a kuma manyan mutane insha Allah hakan ze taimaka ta kowane angle.
Da wannan muka yi sallama bayan ta kanga min camera kan fuksar baby Mimi na mata wasa da surutai kamar mara kai, ma aje wayar ina jin wani madaukakin farin ciki a raina.
Ina son Baba matuka gaya, shima kuma yana so na, ya dauke ni kamar koma fiye da Aunty Luba, dan yana kara wa Abba a kan ta sosai, amma ni kam asalin gata yake gwada min, wuyar ta ban furta ina son abu ba in ya duba yaga ba shi da wani illa gare ni ko will be of helpful wa rayuwa ta to ze min shi, dan yanzu haka shagon da nake zuwa aikin cake and snacks din nan ma shi ya samo min, me wajen yar abokin sa ce.
Ina ta wulla ƙafafuwa daga kwance a kan gado ina rayawa a raina shagon snacks and more will be the next after na make up, fatana Allah ya sa mana albarka kawai.
Ranar ban iya na koma baccin asuba da nake yi ba saboda murna, bayan na gama kiraye kiraye na da kuma murna ta na tashi zuwa kitchen, a can na tarar da Mama tana kokarin hada breakfast, na sa hannu muka yi tare, muna aikin muna hirar mu gwanin sha'awa, sedai fa kome nake yi cikin nutsuwa da takatsantsan nake yi gudun fadan ta, dan bata hesitating yi min fada da gyara in na kuskure, haka kuma bata bada fuskar da nake kawo raini, ba ma ni ba kowa ma bata bashi fuskar da ze kawo mata wargi ba.
A haka muka gama, ta bar min shirya dining ta wuce daki, tayi wanka ta canja kayan jikin ta sannan ta fito, lokacin nima na shiga nayi wanka, na saka A-shape na wani shaking material golden color, plain din ki ne amma yayi min kyau, na yi daurin Zahra Buhari da ya fitar da kyan fuska ta.
Ban Sa komai a face na ba se chapette amma nayi kyau matuka, a haka na fito falo muka zauna ina dannawa waya ta ina duba social sites dina na snacks and cake, da kuma na make up dina, na duba new orders da muka samu, da kuma yadda ake hailing make up dina na jiya.
Jin saukowar Baba yasa na aje wayar ina masa Barka da fitowa, ya amsa da fara'a na ja masa seat ya zauna.
Lokacin ne kuma Hajiya Yayah ta kira su Ya Farooq kan su karaso muyi breakfast.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
Fiction généraleSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...