PAGE NINETEEN

309 11 6
                                    

Ouummey 019

Page 1️⃣9️⃣

___________________A gefen sa na zauna dan shi kadai ne zaune kan one sitter, na dan jingina jikin kafadar sa ina marairaice fuska

"Ya ka manta ka tafar min da waya ta dazu, ina so in yi hotuna, kuma zan making call shine nazo karba".

Sighing yayi, shi se ma yanzu ya tuna da wayar, ko da ya karba numbers din shi ya zuba ya kira dan ya samu number ta, se kuma da ya kira yaga ashe tana da number ta sa, so be bata ba ashe.

Kasa na sake yi da magana jin har lokacin ina jin kaifin idanun ya Farooq a kai na

"Yaya Please save me daga Ya Farooq, se mugun kallo yake min irin na zamu hadun nan, Allah kuma duka na ze yi".

Dagawa yayi ya saci kallon Farooq din, se kuwa ya samu har lokacin hararar ta yake, dan haka ya mike tare da kama hannu na na tashi muka shiga bedroom din sa.

Komai na dakin is milk in color, se curtains dake da ratsin coffee color, ko ina na dakin neat ga kamshi dake tashi me dadi da sanyi.

A can falo kuwa muna shigowa wani abokin ya Farooq me suna Haisam ya gyara zama

"Guy da gaske yarinyar can kanwar ku ce kamar yadda Man yace?".

"Hala baka ga kamanni ba?".

"Not at all, kawai dai ina son tabbatarwa ne dan yin kamun kafa da ku, Allah yarinyar tayi min naji ina son ta sosai, kuma auren ta zan yi in har kun amince min".

Dayan dake zaune tare da ya Farooq a three sitter yayi tsaki

"Haba guy, ya zaka min shigar sauri, Nima fa tayi min magana kawai ka riga ni yi".

Dariya raguwar suka saka suna fadin

"Kowa a nan tayi masa, amma tun da ya riga mu magana se mu mun masa solidarity ".

Magana ya Farooq ze yi se ga mu mun sake fitowa har lokacin yana rike da hannu na daya hannun sa kuma waya ta ce rike, wannan yasa duka suka yi shiru mu kuwa muka yi wajen kofa, ya bude tare da bani waje na fara fita shima ya biyo baya na.

Ya Farooq na ganin rufe kofar mu ya dubi abokan nasu

"Kanwa tace uwa daya Uba daya dan itace autar mu, haka kuma matar Masdooq ce insha Allah, so you guys should take your eyes off her".

Da mamaki duk suke kallon sa, ya watsa hannuwa a iska yana cewa

"Oh baku san Masdooq cousin dina bane ko, to we're cousins ba wai siblings ba".

Dukkan su mutuwar zaune suka yi dan basu taba sanin ba uwa daya Uba daya ne Masdooq da Farooq suke ba.

A can waje kuwa muna fita ya saki hannu na tare da miƙa min wayar, na karba ina Murmushi

"Thanks so much Yaya, ka cece ni daga wancan zakin ".

"Waye zakin?".

Dafe baki na nayi se kuma na saka dariya

"Kash nayi subutar baki, ai na manta dan biyun ka ne, amma wallahi ya Farooq is more like a lion saboda fadan shi, dan Allah kace ya rage ".

Juyawa yayi yana fadin

"Bari in isar da sakon ki tun yanzu ".

Zaro ido nayi tare da fadin

"Na shiga uku". Se kuma na kwasa da gudu na bar wajen, Ya Masdooq ya girgiza kai ya koma wajen jama'ar su.

Hotuna sosai muka sha abin mu, duk inda Aunty Luba tayi kuwa ina biye da ita kamar wata jela, Babyn ta kuwa me sunan Hajiya Yayah wato Mimi na hannu na naki bawa Kowa ita.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now