Ouummey 048
Page 4️⃣8️⃣
__________________Tun da ta fara maganar yake sauraren ta da dukkan nutsuwa da zuciyar sa, abin ya dake shi matuka, blood cancer fa ga Sa'adah, and after that wai her days q limited, a lokacin da likitan ke sanar da shi haka ya ga Bala'i dan kuwa masifa ya shiga zubawa yaba fadin in shine da ran ta ya kashe ta yanzu mana, haka kuma yaki tsayawa ya saurari ragowar bayanin likitan dan in ya fadi wasu adadin ranaku ga Sa'adah din zuciyar sa na iya bugawa.
A hankali ya matse hannayen ta cikin nasa
"Me yasa kike cire princess daga jerin ƴaƴa na bayan ita ce babba a cikin su?".
"Kar mu yaudara junan mu Masdooq, na sani dole princess ta amsa sunan ƴa gare ka tun dai ai kai baban ta ne, amma fa ba mahaifi ba".
Da sauri ya dago idanun sa da suka rine na damuwa, rashin bacci da rashin kwanciyar hankali
"Kar ki fara haka Sa'adah, ni dake kadai muka san wannan, me yasa ba zamu binne ba kamar yadda muka yi planning years back?".
"Ba ze boyu ba Masdooq, zancen duniya ba ya taba buya, ko da kuwa ace cikin kasa muka shiga muka yi maganar muka birne tabbas watarana wani ze hako. Ni da kai mun sani princess ba yar cikin mu bace, ba ma ni da mahaifar da zan yi conceiving balle na haihu, mun karbe ta ne a asibiti a India after mutuwar iyayen ta wanda suka kasance Africans aka kuma nemi dangin su aka rasa, hakan ba ze tava canja wa ba Masdooq, princess will forever be our daughter but not biological daughter, ina kuma shawartar ka da mu sanar da magabatan mu ko dan abinda ka iya zuwa yazo nan gaba, babban abin farin ciki na shine na shayar da ita, na dandana motherly feeling, Allah ya Ara min wannan damar, and ya bani wata ta yi mata tarbiyya, duk da ban sani ba ko tafiyar mu zata yi nisa tare amma ki ba komai hakan ma I'm grateful, forever grateful ya Allah, and you Masdooq, bana tunanin rayuwa would have been beautiful with another Man not you, and ina godiya ga Allah for this also".
Kasa ma sake ce mata komai yayi a lokacin, se kawai ya janyo ta jikin sa ya rungume yana sakin ajiyar zuciya a kai a kai, itama ta rungume shi tana hawaye, babu worst feeling kamar sanin kana dauke da deadly cuta, and the worstest kuma sanin kwanakin ka a irge su ke, ban da karfin imani, tawakalli da komawa ga Allah babu abinda ya hana zuciyar Sa'adah bugawa , amma kamar yadda ta fada ne ta godewa Allah ta kuma karbi ƙaddara, fatan ta in ta tashi tafiya Allah ya bata me sauki ya kuma sa ta cika da imani.
Kamar kuma kar a san da ciwon, shikenan se jiki ya rikice, bata taɓa wuni lafiya kalau, ban da tarin magungunan da take sha kullum, ga karin jini da a tsukin se da aka mata so biyu, ba komai ne ya rikita jikin ba se fargaba da damuwa da suka mata yawa, daga karshe dai dole ya dauke ta suka bar kasar da sunan ya tafi yin wani aiki.
Princess a gidan Hajiya Yayah ya bar ta dan can Mama ta koma da zama saboda gudun barin ta ita kadai a gida damuwa yayi mata illa dan ba kadan ba ta saka lamarin Aimah a ran ta.
Sun yi yawo sosai, farko India suka je ta ga Dr, aka yi the needful aka sallame ta bayan ta kwanta a asibitin for two months, daga nan suka wuce Dubai suka yi a month, Japan suka yi two weeks, France suka yi two months, Russia suka yi one week se a karshe suka wuce Saudiyya suka yi umara, basu dawo ba se ana saura sati daya sallah dan a can suka yi azumin su gaba daya.
Alhamdulillah lafiya ta samu yadda ma ba su yi zato ba, haka kuma da suka je Saudiyya ta gan ta gaban ka'abah se ya saki duk wani abu dake ranta a lokacin, tayi kuka sosai a jikin ka'abah na duk wani damuwar ta, ta godewa Allah duka ni'imomin sa gare ta kana ta nemi yafiyar zunubai da kura kuran ta, daga nan ta ji sauki sosai a ranta, haka kuma ta kudure neman yafiyar Aimah bisa zaluncin da ta mata, in har ta yafe mata bata jin tana da sauran damuwa, dan ban da Aimah zata iya rantse wa bata taɓa cutar da wani tana sane ba, da gaske tana da sanyin hali, nutsuwa da fahimta, sedai kishi yasa ta bari shaidan yayi wasa da hankalin ta wanda Allah ya fargar da ita da wuri.
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...