PAGE FOURTY SIX

525 19 3
                                    

Ouummey 046

Page 4️⃣6️⃣

______________________Ba wai dan na dena son sa ba, ba dan bana kaunar zama da shi ba, ba kuma wai dan nayi fushi da shi ko wani abu ba, a'a.

Ba zan koma zama da shi ba saboda ina son sa ina kaunar sa, shi kuma a yanzu ba ni yake so ba, ba ni yake kauna ba, wata ce daban a rai da zuciyar sa ba Aimah ba, ni na riga nayi wasa da dama ta ta yarda ta subuce min har wata ta tsinta, dan haka zan masa sadaukarwa, irin wadda yayi min lokacin da na nace se ya sake ni na komawa wancan mugun, ya sake ni din ba dan baya so na ba, ba dan baya kaunar zama da ni ba, se dan na sami farin ciki da kwanciyar hankali, to nima irin haka zan masa.

Ban manta yace min kafin dawowa rayuwar su shi da Sa'adah Are living a happy life, full of peace, love and care, shigowa ta cikin su na neman sawa su rasa waɗannan abubuwan, ba zan yarda hakan ya kasance ba saboda ina masa fatan rayuwar farin ciki, so a will shift a little ko komai ya dawo daidai a rayuwar su, Ni kuma zan cigaba da rayuwa da yara na, su kadai sun ishe ni farin ciki, bare ma ga Nene ta, ga Dr Bee'at dina g kuma my comedian Aunty A'i, insha Allah rayuwar wouldn't be boring.

Da wannan tunanin na rufe chapter Masdooq a raina, ba wai na dena tuna shi ba, ba kuma wai na dena son shi ba, sedai ina kokarin ganin ban bari soyayyar sa ta hana ni yin rayuwa ta ta yau da gobe ba.

Yau watan mu bakwai ba kwana ɗaya da zuwa Ethiopia, ma'ana gobe zamu shiga wata na bakwai cif, tun da muka zo Masdooq na kiran waya kusan kullum, sedai Nene bata picking, lokacin nima bana san tayi picking din, daga baya da yara suka fara wayo wajen there months yana kiran vedio call a sa musu waya a fuska yayi ta ganin su, nice dai Nene ta hana.

A haka yaran suka saba da shi ɗan har yanzu suna ganin fuskar sa kullum da safe da dare, sedai ni bamu taba magana ba har yau, da Nene ke hanawa yanzu kuma a karan kai na nake gudun hakan saboda na sani ganin sa ze tada min da duk wata boyayyar soyayyar sa ne da nake hakilon binnewa, ganin sa ze tada min hankali ya yi watsi da duk wani kokari na wajen ganin na hana kai na tunanin sa, shiyasa nake dodging din sa.

A shirye na fito dan yau Laraba, sanye da dogon hijab dina ash color da yayi wa fuska ta kyau, babu abinda na shafa ban da kohl wa ido na se lipgloss wa lips dina amma ba karamin kyau nayi ba.

Tun da na dawo hayyaci na shiga gyaran jiki na, fata ta da duk tayi min wani iri na maida hankali kan ta, skincare products kala kala na siyo na dinga gwada wa har na samu wanda ya karbe ni, kana na shiga zuwa spa duk sati biyu da nake yi a baya, shiyasa nan da nan na farfaɗo na dawo Aimah ta, musamman ga kwanciyar hankali har wata yar kiba nayi kadan bayan murjewar da nayi, in ka ganni ba zaka yarda na taba aure ba balle har da ya'ya.

Islamiyya na shiga tun last two months dan Kara sani, duk da nayi sauka amma akwai bukatar na san litattafai sosai, aikuwa na karu sosai haka kuma yanzu har aji aka bani da dalibai, in mun gama da su mu kuma ayi mana namu karatun.

Samari kuwa sedai in ban fita ba, amma sha Allahu zan dawo da biyu ko uku, kuma duk yadda nake fadar ni matar aure ce basa yarda, se kawai ma na dena fadar tun da ba amfani.

A compound na yadda twins suna wasa tare da jikar Aunty A'i da tazo dan na fada muku ba yarinya bace, yarinyar sunan ta Safar shekarun ta bakwai, twins kuwa yanzu suke seven months da sati biyu, magana a bakin su kamar sun shekara, haka kuma suna tatata duk da bata yi kwari ba, dan ma sun yi zire ne dan ba su yi rarrafe ba, ga girma tubarkallah kamar sun fi shekara, shiyasa ban fiya fita da su ba saboda baki, yanzu zaki ji ana ta tanka su se Nene tace in dinga barin su tun da ba sa rigima kuma suna cin abinci dan tun 5 months Nene ta fara basu abinci, tace ita ba ta ganewa wani goyon kawai ba da ba za'a koyawa da cin abinci ba, nima kuma se na ji dadin haka tun da rashin tsotson su ya taimaka wajen kara murmurewa ta.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now