PAGE TWENTY THREE

330 11 3
                                    

Ouummey 023

Page 2️⃣3️⃣

______________________"Nima ki daina shige min haka, ba kyau tun da ni ba mubarramin ki bane, kuma nima bana so".

Ban ma nuna masa naji ba dan ba zan dena ba, Allah ya sani in na rabe shi wata irin nutsuwa nake ji a raina da gangar jiki na, ban da na san baze yiwu ba ai ni ban ki kullum ace ina nanne cikin jikin sa ba.

Na sake rabawa a hankali na kwanta gefen sa kai na a kafadar sa, ya juyo ya dube ni irin me nace Miki din nan, se na yi takwaf takwaf da fuska

"I always find solace a tattare da kai, dan Allah sweetheart kar ka hana ni".

Na karasa hawayen da ni kai na ban san ko na Meye ba na rolling on my cheeks, da sauri ya kai palm din shi ne tsananin taushi kamar ba hannun namiji ba ya shiga wiping min tears din

"To Meye na kukan kuma?".

Se da na turo baki gaba sannan na bashi amsa da rawar murya

"Ba kai ne ba, ka daina so na irin su Ya Farooq".

Hannu yasa ya janye kai na daga kafadar sa ya juyo gaba daya muka fuskanci juna, hannaye na cikin nasa ya matse waje daya

"Se dai bana numfashi honeybun".

Dage masa gira guda nayi dan ban fahimci me yake nufi ba

"In dai kika ga na daina son ki to sedai bana numfashi Aimah, son ki da kaunar ki a cikin jini na suke, yadda ba zan iya rayuwa ba jini a jiki na ba haka ba zan iya rayuwa ba kaunar ki ba".

Dan farin ciki fadawa nayi jikin sa na sa hannu na zagaye shi tare da kankame shi cikin jiki na, tsayin lokaci kafin na sake shi dan shi dai be rike ni ba

"Kawo min abinci, I'm hungry ban ko karya ba na taho".

Ya fada idanun sa a lumshe bayan ya jingina da headrest na kujerar, da sauri na tashi nayi kitchen ina fadin

"Ai da ka fada min da tuni na dafa ma abinci, amma ji ba ka zauna da yunwa har to twelve".

Be amsa ni ba haka nima ban jira amsar ba na shige kitchen, da sauri da sauri na shiga nema masa simple abinda ze yi breakfast.

Ina shigewa ya bude idanun sa da suka canja zuwa ja ja ja, Allah ya sani baya san ina matsawa jikin sa, shi kadai ya san yanayin da yake shiga sedai na ki fahimtar sa, yanzu kuma ga shi har ina batun ya daina so na, ban da abu na ai yadda ba'a raba hanya da jini ya sani ba ze taba iya raba zuciyar shi da kauna ta ba, dan ba karamin kafuwa na yi a cikin ta ba, daina kauna ta na nufin daina numfashin sa a ban kasa.

A hankali ya furzar da wani dan huci lokacin da zuciyar sa ta jefo masa tambayar

"To in Kuma ta auri wani ba kai ba fa?" .

Ya sake jingina sosai jikin seat, ya sani se sha wahala in aka ce ya rasa ta, ba wahala kadai ba ya san rayuwar sa ce zata shiga wani hali, wanda shi kan sa ba ze iya predicting ba yanzu, se dai so ne na gaskiya na hakika yake mata, in har bata masa so na aure, in har bata masa kauna na hada rayuwa, in har wanin sa take so dan kare rayuwa tare, ta kuma tabbatar tana kaunar sa shi ma kuma yana kaunar ta, to ze iya sacrificing wannan dimbin so da kaunar da yake mata, ba dan komai ba se dan ta rayu da wanda take so, ta zauna da wanda take s o, tayi farin ciki a tare da wanda take so, dan baya mata fatan dandanar zafi da radadin dake cikin so, shi kan sa be san shi ba, be taba experiencing ba se jiya da daddare, amma har zuwa yanzu dacin sa be bar kan harshen sa ba, me yasa ita ze mata wannan fatan.

Haka ya cigaba da tunanin yadda ze fara rarrashi kan sa, ya lallabi zuciyar sa ta hakura da son mallakar Aimah, daga yadda ta kira shi tana kuka, da irin maganganun da take fada hatta akan mahaifin ta ya nuna masa ba karamin zurfi tayi ba akan son wanda ta kira Ibrahim.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now