PAGE SEVEN

213 18 0
                                    

Ouummey 007

Page 7️⃣

_____________________Karo na biyu kenan ko nace na uku, Mama na ta fadi hakan lokacin da take dukana, haka Hajiya Yayah ta fada min haka da tana min nasiha, yanzu gashi shima ya bayyana.

Lallai dolen dole ma haka ne, na sani a da ina da taurin kai da kafiya, tsiwa, da rashin kunya in an tabo ni, haka kuma ban fiya hakuri ba, se dai ban da su ban san wasu halaye nawa marasa kyau ba dan bana neman tsokana kawai dai in an taba ni bana bari ne, haka ina da saurin sabo, kawaye na kuma na fadin ba ni da rowa dan abu na be rufe min ido ba, ta daya bangaren ina da tausayi, dan kusan almajira layin mu duka se da na sa aka sa musu kwano a gidan mu, daga baya da nake sana'a take kai min kuwa rabin samu na a gidan marayu da kan almajirai yake karewa, amma ban sani ba ko ina da wani hali mara kyau ne da ni ban fahimta ba, sedai koma yayane yanzu na yadda, halaye na basu da kyau sam tun da har baki uku suka fada.

"Kwana bibbiyun yayi Hubby".

Kalaman ta suka maido ni hayyaci na, na kuma fahimci ana batun rabon kwana ne, lamarin da ya sake sa gaba na ya yanke ya fadi, ban sani ba ko tsoro ne ya sa hakan ko kuwa fargaba, ba na ce ba.

"To shikenan, Allah ya bamu zaman lafiya baki daya, me girki zata dafa da kowa a lokacin kwanan ta, kina iya tafiya".

Zumbur na mike sanin da ni yake, ban tsaya komai ba kuma nayi falon da nake, hankali na baya tare da su balle wata soyayyar da suka fara a falon ta dame ni.

Kan kujera na fada jagwab, se na sami kaina da addu'a da fatan Allah ya sa ba da ni za'a fara zagayen kwanan ba yau, se kuma naji dariya ta kwace min lokacin da zuciya ta ta fada min babu abinda ze kawo shi daki na, ko da ace da gaske ya raba kwanan sedai ya tafi dakin sa ya kwanta, to mutumin da na lura ma san baya san kallan fuska ta me ze kawo shi kusa da ni.

Da wannan tunanin hankali na ya kwanta tas na tashi na canja kaya na zuwa na bacci na kwanta bayan na kara feshe dakin da room fresheners.

Addu'o'i na nayi na bacci na rufe idanu na cikin neman bacci, sedan cikin ikon Allah shiru yaki zuwa, har kusan awa uku ina kwance se juyi nake,daga karshe dai na shiga karatun suratul Kahf a raina idanuna a rufe kamar me bacci.

Wajejen karfe sha daya na dare naji an Turi kofar daki na, na dan firgita amma se na sake lafewa zuciya ta na bugu a kai a kai, ban ji an shigo bedroom din ba tsayin lokaci se na sadada a hankali zuwa window na daga curtains din hannu na na rawa, se kuwa na sauke idanu na a kan shi, yana tsaye yana karewa dakin kallo kafin kuma ya karasa kan doguwar sofar dake nan ya zauna, a hankali na ga ya cusa yatsun sa cikin sumar kan sa yana hargitsawa.

Tsayin lokaci yana a haka kafin yayi addu'a ya gicciye ya kwanta, kujerar tayi masa kadan sosai dan kuwa dogo ne Masha Allah, ni kaina da na fi Sa'adah tsayi kaina be karasa kafadar sa ba da kadan, ita kuwa a damtsen hannun sa kan ta yake.

A sanyaye na saki curtains din na koma kan bed na zauna, daga ganin yadda ya kwanta ba se an fada min ba yazo kwana ne, wato dai rabon kwanan da ni aka fara, wanda na sani dama haka ya kamata se dai yanayin yadda auren yake ya sa naji bana san hakan.

A zaunen ina tunani se bugawar karfe ɗaya na dare naji, dole na koma na kwanta, wani abin mamaki kuma ko minti biyar ban yi ba bacci yayi gaba da ni.

Kiran sallar farko ya farkar da ni kamar yadda na saba tashi kullum, na zauna har baccin ya dan saki idanuna kafin na tashi zuwa toilet nayi alwala na fito, dankwali na shimfida tare da sa daya daga hijabs dina biyu da aka sakomin a kaya na wanda da shi nake sallah na tayar da nafila kamar yadda nake yi kullum.

Addu'o'i kuwa cikin sallah ta har ba zan iya kayyade adadin da nake roko ba, mafi maimaituwar addu'a ta itace Allah ya kawo sassauci a zuciyar iyaye na, ya sake reuniting tsakanin mu ya kuma yafe min saba musu da nayi tun farko, se kuma Allah ya tashi kafadun Mama ya bata lafiya.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now