PAGE SIXTEEN

295 10 2
                                    

Ouummey 016

Page 1️⃣6️⃣

___________________Tsananin so da kauna ake nuna min a kowane bangare musamman Abba da Mama da suka dauki dukkan wata soyayya suka aza min, ba dan komai ba se dan na zo a macen da basu taba samu ba, dan Mama na mugun son ƴa mace, ga shi da Allah ya tashi se yayi ta jera mata maza, wanda ganin yadda take son ya'ya mata Abba ma ke taya ta.

Yanzu kuwa da suka samu se suke ganin dole ne ma su gatanta ni, su nuna min tsananin so dan nuna godiya ga Allah.

Na taso cikin matukar kulawa, so , kauna da tattali daga iyaye na da kuma yayye na, ta kowane bangare ni yar gata ce, Duka yayye na har rufe rigen  dauka ta ake, Ya Salman da ya Najeeb ke cin girma su barwa su Ya Masdooq da ya Farooq, a tsakanin su ake shan rigima dan ya Ahmad me sanyi ne, baya fada bari yake se sun gama sun aje ni sannan ya dauka.

Aunty Luba kuwa tun suna da aka zo da ita taki komawa gidan su ta tubure ita a wajen kanwar ta zata zauna, ita ba zata bi Hajiya Yayah ba gidan su ba baby, tun ana daukar wasa har aka zo tafiya ta ringa rigima har da shidewa, se Baba yace a bar ta kawai, sanda ta gama marmari na zata dawo, se gashi kuma daga nan bata kuma komawa ba, aka tarkato mata kayan ta ta dawo gaba daya.

Ya Masdooq da ya Farouk kuwa sun fi zama gidan Hajiya Yayah dan ya Masdooq na da ɗafa, wannan yasa ba ya barin gida, shi kuma ya Farouk duk inda ya Masdooq yake nan yake zama, wannan yasa zaman su yafi a can, sedai su wuni a gidan mu da magrib Baba yazo ya ɗebe su.

A haka na tashi, cikin matukar kauna da soyayya, na taso a sakarce a shagwabe kamar kowace auta da kuka sani, Mama bata ganin laifin duk abinda zan yi, wannan yasa tsiwa da rashin kunya suka zama yan gaba gaba a cikin halaye na, tun yarinta ba ni da hakuri, in dai a ka yi min se na rama, sedai ban fiya tsokana ba.

Wannan halayen nawa yasa ba ma shiri sam da ya Salman dan ya tsani rashin kunya, sedai Mama bata bari ya hukunta ni, komai nayi a wajen ta yarinta ce.

Ina shekara bakwai su Ya Masdooq suka bar kasar zuwa Sudan yin karatun jami'a dan kuwa suna da 19years lokacin, ya Ahmad kuma yana da shekara 14 yana Jss 3 shi da Aunty Luba, ni kuma primary 3, lokacin Nene tuni ta koma Ethiopia dan an samu kwanciyar hankali, daga cewa zata je duba wasu dangin ta in zata gan su shikenan tayi zaman ta, ba yarda su Mama da su Baba ba su yi ba tace ita kam ta koma gida, sauƙin abin ta ga wani kawun ta, shikenan zaman ta ya koma can.

A shekaru na na bakwai babu inda zan shiga a lokacin baka ji an kira Aimah ba fiye da so ba adadi dan Allah ya zuba min kyau Masha Allah, ga kuma gayu da Mama ke min, tun a lokacin komai nawa unique ne, tun daga kan takalman makaranta ta zuwa school  bags dina, hatta kayan sawa na se na zaba na darje, ga shi cikin ikon Allah se haihuwa ta tazo wa Abba da wanni irin budi, harkoki suka buɗe masa ta hanyoyi daban daban, kudi kuma yace Bismillah.

Wannan ya karawa gata na armashi, komai nake so yi min ake, wani sa'in kafin ma na furta tuni an min, Aunty Luba kuwa ta zama second Mom dina, bata cin kudin break din ta ni take karawa siyan kayan kwadayi, duk kuwa da ana bani kudin break, haka kuma duk wani kayan kwadayi na yara ina da shi a ajiye ana bani kullum zan tafi school, ban da abinci da se na zabi me zan tafi da shi.

Gata iya gata ake nuna min, Hajiya Yayah ce ma me ɗan daure min fuska dan tace in ta hadu gaba daya aka sake min za'a rasa me iya tsawata min, dan kuwa Abba da Mama ba sa hanani duk abinda nake so, kome na nuna ina so to fa shi za'a yi, dan hatta girkin abinci se mama ta tambaye ni me za'a dafa, kai hatta kaya kafin a siya min se na fadi kalolin da nake so, ko kuma a je da ni na zaba.

In kuna Jin ana fadin a very spoiled child to nice, bana tunanin a duniya akwai dan da ze gwada min gata, sangarta, shagwaba da tabara.

Har ina seven years in rigima ta tashi se Mama ta goya ni nake shiru, haka kuma in na ga dama ince a dakin Abba zan kwana, haka kuma za'a yi, su sani tsakiyar su muyi baccin mu shi da Mama.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now