PAGE THIRTY TWO

371 16 13
                                    

Ouummey 032

Page 3️⃣2️⃣

___________________Aunty Luba ma ta dinga lallashi, hadisai da ayoyi babu wanda bata ja ba amma be sa na ji zan fasa kudiri na ba, hankalin ta itama ya tashe yake da zulumi, a haka har sati uku na fara jin sauki, ranar da Aunty Luba ba ta zo da wuri ba na fadawa Ibrahim, se ya kawo min wani magani ya bawa gateman wai in ji yaron office din oga dan kar yaji wani iri, ni kuwa dama na san da tsarin, aikuwa maimakon biyu da aka ce a sha ni hudu na sha, shiyasa kafin awa daya na rikice da ciwon mata, daga nan kuma se bleeding, lokacin Aunty Luba tazo ta same ni cikin wannan halin, ta kira shi ta sanar masa hankali a tashe, shima Allah ne kawai ya kawo shi lafiya, ya kwashe mu se asibiti, a can aka sanar masa cikin ya zube kuma maganin zubar da ciki me karfi na sha haka kuma doze off, ranar ni kaina na tausayawa ya Masdooq dan kuka yayi da idanun sa, be taba sanin tsanar da nayi masa har ta kai haka ba, sedai ban dashi da ni da Aunty Luba ba wanda ya san maganar, dan ya roke ta kar ta fadawa kowa.

Kwana biyu nayi aka sallame ni, ya kwashe ni zuwa gida, Aunty Luba ta dena min magana, ta daina sake min fuska, zata dai taimaka min har nayi sati na gyagije, daga nan bata kuma zuwa ba, ban damu da bacin ran ta ba dan a gani na bayan dan uwan ta ta goya, daga nan muka koma gidan jiya, sedai yanzu ko kallo na baya yi, hade ran da yake yasa nake ganin kwarjinin sa, da yawa iskancin da nayi da na kasa ci-gaba wa, cikar wata daya da sati Ibrahim ya kira ni yana ta min masifar me nake jira ne, aikuwa na sake rikicewa, komai ya tabarbare, wannan karon har takardun kadarorin Masdooq nake salwantarwa, kudi in ya aje in yaga in zube masa ko in kona, abinci haka zan hada masa wani da wani, baya san yana duka na shiyasa ya rasa ya ce yi da ni, karon farko da ya kai karata wa Abba, Ya Salman da Ya Farooq se da suka sumar dani amma a banza, Hajiya Yayah bata taɓa tambayar me ke faruwa ba duk da tana lure da yadda yake cikin damuwa yake kuma rama, ita da Baba karkari su zaunar da shi su masa nasiha, nima in naje nasiha da hannun ka me sanda ne tsakanin mu amma ban taba kulawa ba, kwana uku da yi min dukan su Ya Farooq na dau fetur din inji na jika duka falon na dauko ashana zan kunna se ga Aunty Luba, tana kuka tana roko na amma baki, fada nake kawai gara na kashe kai na, a cikin haka Ya Masdooq ya dawo, dan yana office amma gaban sa na ta faduwa, shiyasa kawa yaji gwara ya dawo gida ya ga lafiya dan hankalin sa be kwanta ba,.

Idanun sa suka yi jajir kamar an watsa barkono, zuciyar sa na tafasa nna ganin irin kiyayyar da nake masa yaga na kunna ashanar zan jefa ya tare ni da fadin

"Na sake ki saki daya Nu'aimah Bashir".

Ina jin haka na kashe ta hannu na na yarda duka kwalin, na durkushe a wajen, duk da ni na nemi sakin amma na girgiza, wani bangaren na zuciya ta tashi hankali ne zokar, wani bangaren kuma murna nake yi, haka nake jin kamar ana danne bangaren tashin hankalin, Aunty Luba ma zubewa tayi tana kuka tana fadin

"Kin cuce mu Aimah, kin cuci kan ki, kin cuci kan ki".

Na dade a wajen sannan na tashi zuwa bedroom dan daukan kaya na tafi, daidai kofar bedroom din sa dake be rufe kofar ba naji yana fadin

"Ka sha ce min na hakura da auren Aimah, ka sha fada min me yasa ba zan bar ta ba tun da ba iya kadai ce mace ba, a wancan lokacin ban amsa ka ba, amma a yanzu ina tabbatar maka na bar Aimah, na bar Nu'aimah, har abada ni MASDOOQ na bar Aimah Farooq".

Se naji zuciya ta ta buga da karfi, nadama na neman lullube ni amma na ture ta da karfi da yaji na shige daki na ina fadin ai ni na fara barin ka, bari kuma na har abada ehe.

Da haka na kwashi kaya se gida, aikuwa na ga tashin hankali dan kwallo Abba ya dinga yi dani har waje yace ba zan zauna a gidan sa ba, dake bani da kunya se na tafi gidan Hajiya Yayah, ta min nasiha ta shigar ni daki na, Baba kuwa shima kamar ze doke ni kafin ya kyale ni, ban san ya akai ba dan ban kuma ganin Ya Masdooq ba, amma na ji ya tafi India, ban tashi shiga tashin hankali ba se da Ibrahim ya sanar da ni ba ze taba aure na ba, ya sa na kashe aure na ne dan ya rama yaudarar da nayi masa, wai na yaudara shi nayi aure shi ne ya dauki fansa, ya sa na zubar da ciki na, na kashe aure na kuma ya ci amana ta, se kuma lokacin na dawo hayyaci na har na dinga tunanin me ya hau kai na na yi duk wannan diban albarkar, amma na rasa ganewa.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now