PAGE THIRTY FIVE

469 18 1
                                    

Ouummey 035

Page 3️⃣5️⃣

___________________"Shin ban hane ki kawo min batun ko da Abinda Ya shafe ta bane Luba?".

Bata share hawayen ba take bashi amsa, duk da dukan da gaban ta ke yi amma bata fasa ba, baze yiwu a cigaba da wannan abin ba, sam babu adalci a lamarin nan, ko da kuwa bata kyauta ba amma ai bata cancanci haka ba, da soyayya da jawo wa a jika ne zata gyara, amma abinda suka yi ai kara tabarbara lamari ze yi.

"Idan da gaske ba kwa san jin ko da batun da ya shafe ta ne se ku tsaga jikin ku ku cire jinin ta da yake yawo a jijiyoyin ku, haba mana baban Mimi, wannan abin naku babu adalci, sam wallahi".

Tsananin mamaki da al'ajabi yasa Ya Salman kasa cewa komai, se kallon ta da yake yi kamar wata sabuwar halitta, abu ne da be taɓa faruwa ba cikin tsawon zaman auren su, kai tsawon rayuwar su ma tun suna gida, Luba me biyayya ce, bata da tsayayya balle rashin kunya, shiyasa yanzu abin ya girgiza shi.

Duk da ganin yadda maganar ta ta dake shi be sa ta fasa ba, dan ta kudiri niyyar Insha Allah se ta kawo karshen wanann rashin adalcin da suke wa yarinya karama, kuma in har tayi nasara a kan sa kamar tayi ne akan sauran, dan Kasancewar sa babba yasaa duk sauran maganar sa suke ji bayan ta Mama.

"Ku duba fa, Aimah yarinya ce karama, ko ba komai ai ta cancanci a mata uzuri dan akwai kuruciya a tattare da ita lokacin, aside that ga gata da sangartar autanci da kuma kasancewar ta tilon ya mace cikin maza hudu, kuma ko da su Mama su ka kasance iyayen mu ai yan adam ne, ajizai ne masu iya yin kuskure, dan haka ma su Mama ba su tsallake ba, sun yi nasu ajizancin a kan tarbiyyar Aimah, wajen kokarin gwada mata kauna da soyayya se suka zarme idanun su suka kulle, sukai mata raino akasin wanda suka mana, dan haka har da wannan ajizancin nasu cikin kasancewa dalilin ƙaddarar Aimah, so be kamata ace ita kadai zata yi taking blame din ba, mu ma da namu laifin, dan haka se mu tsaya mu hadu gaba daya mu gyara, ba wai mu wofintar da ita ba, yau da ace Abba ze dawo rayuwa ya ga yadda kuka wulakanta rayuwar ƴar sa mace tilo kuna tunanin ze yi farin ciki da ku, ko ze yi alfahari da ku? In kuna tunanin haka ne to kun yi kuskure, muna rokon ƴaƴa maza a farko ne dan su tsaya wa kannen su a rayuwa, wajen tarbiyya, wajen kula da dabi'u da halayya, da kuma tallafar su a wajen da sukai rauni, in har basu kasance masu aikata haka ba kenan meye marabar su da mata, masu gajeren tunani, marasa dogon tsinkaye da kuma yanke hukunci cikin fushi?, Tabbas babu wani banbanci, dan Allah baban Mimi ku sake tunani, dan Allah".

Ta karashe tana rushewa da kuka, ta dade tana auna irin yanayin da ze iya kasance Aimah ke ciki a yanzu, sedai duk yadda ta auna se taga kamar be kai yadda take ba, tun ranar da taje tausar Sa'adah shekara daya ba wata biyu baya, ta shiga ta fito batare da neman Aimah ba duk da sanin tana cikin gidan, haka kuma ta tabbatar taji ta zuciyar ta ke cikin rashin dadi, ko da Sa'adah ta kasance yar uwar ta me irin matsayin Aimah a musulunce amma a zuciyar ta matsayin nasu varies, in ta rantse ba zata yi kaffara ba tana jin Aimah a ran ta fiye da Masdooq, dan bayan kasancewa jini daya a kwai shakuwar shekaru goma sha shida tsakanin su, ta ya to ba zata damu ba, taya hankalin ta ze kwanta?, Ba zata iya ba, ba zata cigaba da jurewa ba, dole zata yi fighting, for Aimah's sake, and Insha Allah she'll win it.

"Ban san yaushe kika fara ketara umarni na ba, amma na yafe miki, ina kuma rokon Allah ya yafe miki".

Daga haka Ya Salman ya bar table din, har ransa maganganun ta sun taba shi, sosai ba kadan ba amma ba ya san ya nuna mata, shi kan sa hankalin sa ya dade da komawa gare ta, tsoro da fargabar rasa mahaifiyar su da kuma fushin da be gama hucewa daga kirjin su ba ya tunzura su suka yi abinda suka yi, yanzu kuma kunya ce ta sa yake jin nauyin su neme ta, se kuma sanin waye Masdooq, ko da fushi ya sani ze kula da ita, ba zata tozarta a hannun sa ba.

****Masdooq****

Yau kwanan sa biyu da zuwa kasar France, aiki ne ya kawo shi kuma tun ranar da suka zo suka shiga meeting kan batun da ya tara su, jiya ma sun yi, yau kuma suna hutawa ne.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now