PAGE TWENTY ONE

330 14 26
                                    

Ouummey 21

Page 2️⃣1️⃣

______________________Abba ya kare fada with bitterness in his tone, abin ya masa zafi, fuskar sa ta nuna haka ma idanun sa.

Wani irin kallo na shiga yiwa Abba, sam ban yadda Ibrahim zeyi abinda Abba ya fada ba, taya ma ze fara, me ze sa yayi hakan bayan ya san yadda muka tsara.

Wait to ma shi Abba wa yace yaje, ai dama dole waliyyan Ibrahim suce ba aure ze yi ba, tun da dama ba zasu bari yayi aure ba yar su na da tsohon ciki, kar tashin hankali ya jawo mata wata matsalar! Na ayyana a raina.

"To amma Abba ai da baku je ba, nifa tuni mun gama tsarawa dama ba yanzu zamu yi aure ba se matar sa ya haihu, tun da kun ga ai in yayi aure yanzu da take da tsohon ciki be mata adalci ba, na san wannan ne yasa Ibrahim ya fadi haka, su ma kawunan sa haka amma ba wai dan ba zasu bari ya aure ni ba, bari ku gani, ta na haihuwa da wata biyu zasu zo neman auren".

Takaici, bakin ciki da ɓacin rai ne ya cika Abba, ya juya ya dubi Mama da fuskar ta take ba dadi alamar itama a bin ya bata mata rai.

Kafin yayi magana ta riga shi da fadin

"Nu'aimah har yanzu ke yarinya ce, annan mahaifan Ibrahim ba zasu bari ya aure ko ba, shima kuma ba shi da niyyar hakan, ban sani ba tsoro ne yasa ko kuwa soyayyar matar sa ce, amma dai tabbas baya yin ki yanzu, kiyi hakuri, na sani da zafi amma Allah ze baki wanda ya fishi".

Dariya nayi kafin kuma na bata fuska ina kallon Mama, da wannan Muryar tawa ta shagwaba da sangarta nace

"Ni dai kar ki min baki, kuma babu hakurin da zan yi dan kuwa Ibrahim ze aure ni, ji Mama har wani fada kike wai da zafi kamar irin ya taɓa faruwa da ke".

Me ya kamata Mama tayi a wannan lokacin? Ku sanar min please.

Mama ta girgiza kai kawai bata ce komai ba, na maida duba na kan Abba, baro baro nake ganin bacin ran sa amma ni ban damu ba, damuwa ta Ibrahim da aka ce wai ba ze aure ni ba

"Kar ka bata ranka Abba, let's wait for 8 months, a gaban ku Ibrahim ze zo ya nemi aure na, and please kar ku kuma cewa ze bar ni dan Allah i can loose control".

"In har kika ga kin aure shi kuwa se dai in bana raye ko kuwa kin canja wani mahaifin ba ni ba, ban taba tunanin ba ki da hankali ba nu'aimah se yau, in fada miki irin wulakancin da aka yi mana a gidan iyayen yaron nan amma ke bata haka ma kike yi ba, an wulakanta mu, an fada mana maganganu marasa dadi amma kike ikirarin auren dan su, to let me make it clear to you wallahi ba zaki taba auren Ibrahim ba".

Wani irin mikewa nayi tsaye, ina jin numfashi na na sama kamar wadda ake kokarin rabawa da numfashi na

"Wallahi se na aure shi Abba, kawai dan rashin adalci se ace ba zan auri wanda nake so yake so na ba, bayan ku kun auri wanda kuke so, to wallahi ban zan yadda ba".

Mikewa Abba yayi jikin sa na rawa yake fadin

"Ni kike fadawa haka Nu'aimah, ina fadin ba zaki aure shi ba kina se kin aure shi? To na ga yadda zaki aure shin, dan na fada miki se dai in bana raye ko ki canja wani uban".

"Allah ma yasa ina da Baba, se in koma gidan sa na san shi tun da yana so na baze ce.....".

Saukar marin da na sha a karo na farko daga hannun Abba yasa magana ta ta katse, haka kuma jina ya dauke na sakanni, yana dawowa kuwa na saki ihu da kuka, na fadi na shiga birgima a wajen, kuka nake da ihu tare da birgima janar yar shekara biyar ba sha takwas ba, Mama na zaune ta zuba tagumi tana kallo na, Abba kuwa takaici ya sa yana tsaye yana duba na cikin bacin rai, ganin abun ba na kare bane yasa ya fusata ya cisgo wayar jikin receiver, ban aune ba se jin saukar bulala na yi a jiki na, ai tuni na tashi daga birgimar da nake na fada kan Mama na kanainaiye ta ina ihu da soshe soshe, hankali tashe Mama ta shiga kare ni tana bawa Abba hakuri.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now