Ouummey 013
Page 1️⃣3️⃣
_____________________Tun da ya shigo dakin yake bin ta da kallo jikin sa a sanyaye, ya rasa ma me zece, ya rasa tunanin me ze yi, se kawai ya karasa gaban ta ya zauna looking at how helpless she's lying on the bed.
Me ya jawo mata ciwon ulcer, shine kawai abinda yake san ji yanzu, sedai ba shi da wanda ze tambaya, ita da ze tuhuma din kuma gata kwance bata ma san inda kan ta yake ba.
Is it rashin son sa da kaunar sa ya sa a wannan karon kuma ta yanke yiwa kan ta horon yunwa? Ko kuwa me ne ne?
Shi dai ya san gidan sa ba rashin ci ba rashin sha, abinci kan yayi rabi ma ya karo wasu, he has the believe that abinci is the first priority and the first need na dan Adam, so baya wasa da siyan kayan abinci wa gidan sa da gidan iyayen sa, Sometimes har fada Hajiya Yayah ke yi tace abincin su be kare ba ya yi wani abu da kudin, amma no shi yafi san kullum yaji shiru babu wani korafi kan rashin wadatuwar abinci.
And not only food yake kawowa, healthy diet yake providing ma iyalin sa dan kuwa nama se ya kawo kala uku ban da kifi, su kwai, su veggies su fruits duk se ya siya every month, ya kare ko be kare ba be fasa siya.
Amma ace wai tana kwance a gadon asibitin nan ne saboda cutar yunwa, wane irin abin kunya ne hakan gare shi, me mutane zasu kalle shi in suka ji wannan maganar.
Haka ya gama tunanin sa be samu makama ba, a karshe ya barwa kan sa yin bincike dan gano komai, ko da ya duba wrist watch din sa is ten minutes after 6, se ya tashi ya nufi kofa, har ya bude ya juyo ya kalle ta yana tuno likitan yace se after five hours sannan possibly zata iya farkawa, so se ya fita tare da rufe kofar.
Nurse station yaje ya samo guda daya ya bata kudi kan ta zauna masa da ita kafin yaje gida ya dawo.
Ko da ya koma Sa'adah bata dawo ba, se princess da Hindu, suka gaishe shi princess ta ɗane shi, ya daga ta cikin farin ciki yana mata wasa kamar yadda suka saba, sedai be dade ba ya sauke ta yace ze yi alwala ya fito.
Ko da ya fito hindu na sake mopping floor din falo, ta masa adawa lafiya haka ma princess ya amsa su, har ya kama handle din kofar falo se kuma ya dawo ya zauna kan one sitter, ya kalli princess yace taje dakin sa ta dau phone din sa tayi game.
Se da ta shige sannan ya kalli Hindu dake kwasar kayan gyaran dan barin falon kamar yadda Madam din ta ta umarce ta ta dinga yi duk Masdooq din ya shigo falo, sedai baya kai ga fita ba ya tsayar da ita tare da cewa ta dawo.
Kan carpet ta tsugunna daga opposite him
"I'll ask you, and I want everything daze fito bakin ki ya zama actual truth, not otherwise, in Kuma kika min karya I'll punish you before sending you back to your parents, kin ji me nace?".
Jiki na rawa hindu ta amsa dan tun da take da shi magana bata taɓa hada su ba bayan gaiuwa, shima daga lafiya be kara kallon ya, ga kuma maida ita gida da yake magana, ina zata so komawa gida bayan a nan rayuwar ya dauko hanyar gyaruwa da daukaka ta sanadin ilimin da suke bata batare da duba da ita din wacce ba saboda tsabar karamci.
"Aimah na fitowa ta ci abinci tare da Maman princess ne ko kuwa diba take ta tafi daki?".
"A'a.. a'ah, Aunty ce ke zuba mata ta bani na kai mata, wataran kuma ta kaji mata da kan ta".
Cikin mamakin jin wai Sa'adah ke zuba mata abinci ya dubi hindu sosai
"Okay bata fitowa ta diba da kan ta kenan, ko kuwa ta taba fitowa ne Maman princess ta mata wani abu, ko zagi haka ko makamancin s".
"A'a yallabai, bata fitowa ne gaba daya, dan tafi wata uku bata fito ba ma daga dakin".
Jinjina kai yayi
YOU ARE READING
BA KOWANE SO BANE.......
General FictionSo da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda n...