PAGE FOURTY SEVEN

434 19 2
                                    

Ouummey 047

Page 4️⃣7️⃣

_____________________Karfe biyar muke tashi a makarantar, sedai yau ganin hadari sosai ya tufke ga iska ana yi yasa dole aka sallame su da wuri saboda yan nesa, dan ruwan nan in ya balle ba'a san ranar tsayawar sa kasancewar muna karshen watan July ne.

Mu ma yau bamu zauna an mana jari na duk muka yi sallama aka watse, sauri nake yi na kai gida saboda kar ruwan ya dake ni, ina son in ga ana ruwa sosai sedai bani da damar shiga yanzu zazzaɓi ya rufe ni.

Addu'a ta bata karbu ba dan ko zagayawa ban yi ba ruwan ya kece da karfin sa, wata irin ajiyar zuciya na sauke lokacin da sanyin ruwan ya ratsa hijab dina zuwa cikin riga ta ya sauka a fata ta.

Se kawai na rage saurin da nake yi na kankame jaka ta dan kar ruwan ya shiga ya taba min litattafai, kafin in kai gida na jike sharkaf ina ta diga kamar wata kaya, ban shiga falon a haka ba dan zan lalata musu rug, se na tsaya daga kofa na shiga kwalawa Aunty A'i kira, karfin ruwan ya sa bata ji da wuri ba dan duk suna bedroom din su, da sauri ta fito tana kallo na cikin damuwa

"Me yasa zaki taho a ruwan nan bayan kin san ruwa baya miki ta dadi Aimah?".

Baki na rawa na saki murmushin karfin hali

"Wallahi a hanya ne ya tare ni Aunty A'i, ko kafin na nemi gurin fakewa na jike shiyasa kawai na karaso".

Da sauri Aunty A'i ta juya tana fadin

"Ina zuwa".

Daki na ta shiga ta dauko min kaya, doguwar rigar wani yadi ne me kauri se hula da rigar sanyi har da karin karamin bargo.

"Shiyasa nake son ki Aunty na, bari na maza na canja".

Se da na bude kayan daga nannadewar da ta musu naga har da undies, na sake sakin murmushi na shiga canja kayan a cikin corridor din, ina gamawa na lulluba bargo na na kwashi kayan zuwa daki na.

Se da na kai toilet na saka kayan cikin washing machine, undies din kuma na wanke na shanya sannan na fita zuwa kan bed na kara jan babban duvet na kara, dumin da ya shiga ratsa ni maimakon sanyin da na fito daga ciki yasa nan da nan bacci yayi gaba dani.

Ranar kwana aka yi ana ruwa, be dauke ba se karfe goma saura, mu dai muna gida mun hade cikin kayan sanyi, yau riga da wando na saka na sanyi pusha pink, twins ma na sanye da nasu se dai su baby pink ne, Nene ce bata saka ba tace ita ta saba abinta, Aunty A'i ma rigar sanyi kadai ta sa, ban biye ta ba na sawa Safar na ta irin namu, ita kuma dark pink.

Mun yi kyau sosai gwanin sha'awa, muna zaune muna karyawa a falon cikin farin ciki, hular kai na me kyau ta teddy me gashi sosai na dan tura baya kadan ina cewa

"Maganar gaskiya Aunty A'i you're a good chef, ban da Hajiya Yayah ko Mama se ta sallama miki a bangaren kitchen".

Dariya suka yi gaba daya, Nene na cigaba da tsotsar kashin hannun ta tace

"A'i sa mata waigi kar ta fadi dan santi ne take yi, to ba ma dole tayi santi ba ta ji girki me suna girki, su suna nan suna fama da feleke, taji farfesu cike da daddawa ina ba zata yi santi ba".

Murmushi nayi kawai na cigaba d acik abu na dan ba da wasa nake ba yayi min dadi, muna gama wa na mike na wanke hannu na, twins da ke gefen Nene custard ne ta ke basu se cookies, hankali kwance kuwa suke cin abin su, na zuba musu ido cike da sha'awa da jin dadin wai duka wadannan nawa ne, Allah Al Hakeem.

Seda ta gama ba su na gyara wajen dan ban bar wa Aunty A'i aiki ita kadai, muna gama wa Nene ta jawo Radio din ta ta kunna labarai, ni kuwa se na kishingida tare da ɗaukan waya ta na shiga wps, jerin litattafan da Sadiya ta tura min ne jiya, kallon su nake da son zabar wanda zan fara da shi, daga karshe dai se na fara da Ba ni da laifi dan ba ga be kai su yawa ba, haka kuma sunan ya dauki hankali na.

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now