PAGE FOURTY FIVE

484 18 0
                                    

Ouummey 045

PAGE 4️⃣5️⃣

BONANZA BONANZA BONANZA!!!

Ina kuke ma'abota so da kaunar littattafan ouummey?, Albishirin ku!, To ga dama ta Samu!!!.

Kamar yadda kuka sani paid books din ouummey guda uku ne,

ANJANE ₦400
RASHIN HAIHUWA ₦500
YAR DAMFARA ₦500

Dukan su sun kammala a document, sedai a maimakon ku biya ₦1,400 dan samun su, yanzu zaku biya ₦1000 ne kacal ku same su duka ukun!!!.

Wannan bonanza is valid to month ending kamar yadda masoya suka yi pleading a mayar, a hanzarta a sharbi rahusa, wannan duk kauna ce daga ouummey zuwa gare ku masoya❤️.

Ga me bukata, should chat my up through 09013101854,
Ouummey 📚✍️.

___________________Madaidaicin gidan Nene suka sauka, daki uku ne, Nene na cikin daya, dayan kuma me aikin ta se daya da ba kowa, shi ta saka a ka gyarawa Aimah, aka saka ƙatuwar katifa family, aka lailaye ta da sanin gado me kyau da daukar ido, dakin se tashin kamshi yake yi ta ko ina.

A nan aka sauke ni da yara na, kwanan mu biyu da zuwa Nene ta kira Masdooq kan sunan yaran dan ita kam ba zata iya fadin wani cutie da handsome ba, rasa sunan da ze fada yayi se kawai yace mata

"Aiman da Airah".

Daga haka Nene ta kashe wayar ta ba tare da ta bashi damar tambaya ta ko yaran ba.

Kwanan mu uku da zuwa na fara zuwa asibiti, wanda tun da na shiga dakin da aka sauke mu se yau din ne na fito, kulewa nake a daki abu na na saka yaran a gaba ina tunani, wani sa'in ni kaina ba zan iya cewa ga tunanin da nake yi ba, kawai my mind was always absent daga wajen, Nene da me aikin ta babba Aunty A'i ke kula da yaran, wani ikon Allah su bana damuwa dan sun dauke su, kawai dai in an gama gyara su a dawo min da kaya na, shikenan.

Se a kwanakin nan yaran suka samu kulawar da ta dace, wanka da ruwan zafi zuwa gashin cibi, se gashi hatta da baccin su se da ya canja, dama ga su ba rigima ba se su wuni suna bacci, ni kuma in ta sa su a gaba in yi ta kallo da tunani.

Yau muka shirya fita zuwa asibitin da Nene take ganin ya cancanta, tun muna Nigeria Dr yayi mata bayanin ina bukatar therapist, shine yau zamu je.

Tun da muka shiga mota kai na na kasa, bana kallan kowa kamar yadda tun da na zo kasar bana magana, daga uhm se uhmuhm, har muka kai asibitin wanda drivern Nene ne ya tuko mu, muna zuwa ba bata lokaci aka yi attending mana dan muna da appointment da Nene ta karba tun jiya.

Tare muka shiga office din da Nene, tana rike da yaran duka biyu, ta tasa ni gaba ita tana bi na a baya.

Ban daga kai na kalli ko ina ba a office din balle Drn, na zauna kan kujera bayan Nene ta min izini, itama ta zauna a kusa da ni suka shiga gaisawa da likitan, ya amsa da faram faram da alama be da damuwa, daga kuma jin muryar sa ba wani babba bane.

Suka gama maganganun su sa Nene da ba wani fahimta nayi ba dan na fada tunanin da ya zame min jiki, ashe yana ta kiran sunana ban sani ba, se da Nene ta taɓa ni sannan na kalle ta, se ta nuna min shi tana fadin

"Ana miki magana".

Se lokacin na dago na kalli bangaren da Nene ta nuna min, yana zaune kan kujerar da ke motsawa da shi a hankali, matashi ne da ba ma ze kai shekarun Ya Masdooq ba, sedai be kai shi kyau ba amma yana da nasa daidai misali, daga zaune da yake zaka san ba wani dogo bane, sedai yana da fara'a sosai dake kara masa kyau.

"Kanwa ta".

Se na fara juye juye a office din dan neman kanwar sa da naji ya faɗa, ya takaita min confusion dina da fadin

BA KOWANE SO BANE.......Where stories live. Discover now