ZAIN ZAYYAN PART ONE PAGE 1 & 2

5.6K 199 1
                                    

MRS NOOR'S 💕 NOOR'S NOVEL 💕💕💕💕💕💕💕 CHAPTER ONE
    
                ZAISUS LIFE WRITTERS
              WRITTEN
                            BY
MRS NOOR'S NOVELS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝

Haba KHALID meyasa kakesan 'yar mace ta raina maka hankali ne,gaba dayan AISHA guda nawa ce?kaga Dan Allah kada ka bataman rai,am not in the mood for this childish act of yours okay? So please 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔 Khalid dake kwance akan sofa da sauri ya tashi zaune yana kallan zain wanda ga baki daya attention dinsa nakan television wrestling ne suke kallo a mbc action, girgiza kai Khalid yayi sannan ya mike tsaye ya saka takalmansa ya fice ransa a bace, murmushi Zain yayi sannan yace zancen banza,ni wallahi har yanzu ba'a yi wannan macen da zata hanani bacci ba ko ta bataman rai ba,dan guntun tsaki yaja tare da maida hankalinsa yaci gaba da kallansa🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄

Haba dan Allah AISHA forgive him wallahi yayi nadama,kinfi kowa sanin cewa Khalid is different from his friend nesa ba kusa ba,kindai san wallahi da zain ne saidai ki nutse a ruwa amma wallahi bazai baki hakuri ba,wait a minute wannan shine son da kike masa,haba esha com on forgive him mana,babbar kawarta ce safeeya ke mata magana akan ta yafewa khalid, murmushi Aisha tayi sannan tace naji bakomai ya wuce but safeeya he really hurts me Allah, safeeya ta dora hannunta akan nata sannan tace i know but remember how much he loves you so kiyi hakuri kawai, Aisha tace okay besty thank you, safeeya tace nagode nima,kema kanki kinasan jin voice dinsa kawai ego ne ke hanaku sauraren juna,but you guy's are deeply in love with each other so try to understand each other more okay? Aisha tace okay tare da mikewa tsaye ta fice daga dakin tana smiling 😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

❤️❤️ MRS NOOR'S NOVELS ❤️ ❤️
Dauke take da faranti akanta,bakomai aciki sai gwangwanin tumatur karami dana peak milk,daga ganinta kasan daga wurin talla ta fito,sanye take cikin riga da zane banban sai wani bakin gyale akan kafadarta,sauri take sosai kaman wacce aka biyo,kayan jikinta sunyi jawal jawal,tayi baki sai warin zufa take, daidai kofar wani gida mai ginin bulo wanda daga ganin gidan kasan suna cikin rufin asiri ne kawai iya gwargwado,tun daga shigifar gidan ta jiwo muryar inna larai tana fadin, tsinannar yarinyar nan har yanzu bata dawo ba,tanacen ta tsaya tana fira da samarinta,sai sun gama lalatar da ita sannan ta dawo tana wani kame-kame kaman ta kwarai,wani dan guntun tsaki taja mtswww, Allah dai......bata kai ayaba yarinyar ta shigo tare da sallama,inna larai dake zaune akan tabarma tana tsintar gumi ta dago kanta sama,wata harara ta bankawa yarinyar da ke tsaye da farantin akanta sai kace wadda aka dasa,inna larai tace toh dan ubanki bazaki ajeman faranti ba,ki bani kudina, ahankali yarinyar ta sauke farantin daga kanta,ta durkusa gefen inna larai,tace ina wuni?inna larai kuwa cikin zafin nama tace da ban wuni ba zaki ganni?nidai bani kudina,ta fadi haka tare da miko mata tafin hannunta wanda yake abude, cikin rawar jiki ta dorawa inna larai yar leda fara,inna larai ta banye ledar ta kirga kudin tsab, sannan tayi murmushi tace yawwa ko ke fah?da ace haka kike kullun ayyi da bazamu dinga fada ba ,maza kije kiyi wanka, abincin ki yana kicin,kici kizo na aikeki cefanan gobe, jikinta ba kwari ta mike ta shige dakin,ta cire kayan jikinta,ta dauro zane ta fito,ruwa ta diba ta shiga bandaki tayi wanka, ba'a dauki wani dogon lokaci ba ta fito,tayi arwala sannan ta shige dakinta,ta zauna kan katifar da ke dakin,ta shafa vaseline,ta shafa powder da kwalli, kwalliya dai tayi amma ba wata doguwar kwalliya bace,Amma tayi kyau ba karya,Ghana most go dinta ta bude ta dauko wasu riga da sket ,na atamfa da red hijab,tsab ta shirya abunta,tayi sallah sannan taci abincinta shinkafa da wake ne da yaji(garau-garau)tasha ruwa ,ta kwanta saboda ta gaji sosai 😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥

Kaman daga sama ta jiyo inna larai tana kwala mata kira,LAURATU LAURATU a firgice ta mike ta fito cikin hanzari,sai hamma take tana karawa,wani shegen kallo inna larai ta mata sannan tace kinga nifah banasan sakarcin banza,maza kizo kiyoman cefane kamin a kulle kasuwan, LAURATU tace tau inna,ta saka takalmanta yan faransi ta nufi gun inna larai dake tsaye ajikin bango tana mata kallan ukku saura kwata,har kasa LAURATU ta durkusa tana sauraren aiken inna larai,tace ki siyoman kwanon gyada biyu,da kayan miya ,ki siyoman magi,mangyada,manja da albasa,sai ki siyoman alayyahu,naira dubu ce ta bawa lauratu, ahankali lauratu tabi dubun dana mazurunta,cikin rawar murya tace inna dubu ce fah kika bani?inna larai tace eh dubun ce na baki sai akayi yaya?lauratu tace kikace kwanon gyada biyu,dasu kayan miya duk a dubu dayan zanyo wannan cefanan?inna larai tace toh lallai yarinya ta balaga,wato har kinsan kudin basa isarki cefane,nasani ayyi dan dai kinsan ba makauniya bace ni,dan haka tunda kinada samari birjit idan kika fita kyasan yanda zakiyi,amma wallahi kada ki dawo gidan nan bada cefanan ba,mikewa lauratu tayi tana kara yiwa naira dubun hannunta kallo saboda batasan inda zataje ba,batasan yanda zatayi ba,kanta a kasa take tafiya daidai shigifar gidan tayi kaura da wata yar matashiya kaman ita,da karfi matashiyar ta bangajeta saida ta fadi kasa, narainarai tayi dana mazurunta tana kallan wadda ta bangajeta,cikin zafin nama take fadin ke wai wacce irin jahila ce?kina tafiya amma bakya kallan gabanki,yanzu mutun ya kasheki ace ya kashe mutun koh?lauratu dake a kasa sai kallanta take, cikin sanyin jiki tace dan Allah kiyi hakuri HANNE wallahi banganki ba,wani dogon tsaki taja mtswww sannan ta ficewanta cikin gida,tana wani tastas da chewing gum kaman
wata banza🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Bayan fitar lauratu akan hanyarta taci karo da kawarta MAIRO tana murmushi tace kawalliya ina zuwa haka?lauratu ta tabe baki tace kasuwa zanje mairo,mairo tace mezaki siyo ne?lauratu ta lissafa mata komai kaman yanda inna larai ta gayamata,mairo tace iyyeeee kinyi ciniki kenan a wurin talla,kice yau zakuci dadi? murmushi lauratu tayi sannan tace tau kinsan ko da nawa zanyi duk wannan cefanen?mairo tace indai inna larai ce nasan bazata wuce baki jika biyu da wazobiya biyu ba(500)ido lauratu ta fiddo tace aaaah jaka biyar ce(1000)mairo ta tabe baki tace kinga nima kasuwar zamuje,idan kudin suka rage zamu siya mata komai saboda nasan halin inna larai sosai, murmushi tayi tace Allah sarki kawalliya nagode,mairo dake sanye da banban ajikinta sai mayafinta baki karami wanda aka dora akan kafada, kyakkyawa ce itama kanta, tafiya suke suna fira,mairo sai labarin samarinta take bawa lauratu, lauratu kuwa banda murmushi da tabe baki babu abinda take😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏

❤️❤️MRS NOOR'S NOVELS ❤️ ❤️
KHALID ne na hango yaci ado cikin shadda fara,wadda tasha dinkin yan zaria daga wuya har hannu,yayi kyau sosai tamkar wani ango,sai kamshi yake abunsa,har lokacin zain zaune yake a fallo akan sofa yana kallan wrestling sai kuwa yake yana karawa, khalid yana fitowa yace guy ni zan fita,zain ya juyo yana kallan khalid murmushi yayi yace ina zuwa haka kasha shadda sai kace wani ango? KHALID yayi murmushi yace i don't know,nidai na fita see you later,zain yace nidai nasan cen zakaje,kawai malam kanasan yarinya yar mitsiltsila ra maida kai tamkar remote,sai yanda tayi dakai, khalid yace yanzu dai kai akeji mahaukaci ya fada rijiya,kai yasa ya fice daga gidan....
Wayan zain ce ke ringing yana dubawa sai yaga number ba suna,dan guntun tsaki yaja mtsww yace wallahi yarinyar nan mayyace, rejecting din call din yayi ya saka wayan silent ya koma ya kwanta da control remote hannunsa sai cenza channels yake dama da hauni😏😏😏😏😏😏
Mrs noors novels

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now