💗💗💗💗💗💗 ZAISUS LIFE WRITTERS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝 STORY WRITTEN 💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗 BY 💗💗💗💗💗💗💗💗 MRS NOOR'S NOVELS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝
WANENE ZAIN ZAYYAN?
ZAIN ZAYYAN haifaffen dan bakori ne cikin jihar katsina,asalin iyayensa 'yan bakorine, ALHAJI ZAYYAN shine mahaifinsa , Allah yayiwa mahaifinsa cikawa yanada shekara biyar aduniya,ya tashi hannun mahaifiyarsa HAJIA ZAYNAB itace mahaifiyarsa,shi kadaine 'da kwaya tal da suka mallaka a duniya,shiyasa suka dauki son duniya suka dora masa,gata da kulawa ba abinda ya rasa arayuwarsa,yayi karatun sa a England inda ya zama cikakken likita, makaranta,bayan ya gama sannan ya jona makaranta a UK,yayi business administration,inda ya gama,daga baya ne suka dawo sokoto sanadiyar yanayin aikinsa ba mutun bane mai zama wuri daya ba,bayada wani amini da ya wuce KHALID akoda yaushe suna tare, yanayin aikinsu ya zama daya hakan yasa suka gina gida suna zaune acikinsa,su biyu kadai,babu yaudara ko cutarwa atsakanin su, KHALID asalinsa mutunen sokoto ne shima nan gaba kadan zamu samu tarihin shi,zaune na hango zain cikin kananun kayansa sai latse latsen wayansa yake,daga ganinsa kasan tashin fallo idan ya taba tuntube toh tabbas da remote control ne,hajai zaynab ce take saukowa daga kan staircase din cikin wata material gown multiple colors rigan ta mata kyau sosai sai murmushi take tana saukowa ta nufi fallon,ta zauna tare da cewa yaron mama? ahankali ya juyo yace mummyna?tace hutawa kawai ake yace eh wallahi,tace yana da kyau,cen na hango wata babbar mace wadda a shekaru bazata wuce shekara talatin ba tana tafiya daya daya cikin riga da zane sai yanzu na lura da ciki ne da ita, fallon ta karaso ta gaida hajia zaynab, hajia zaynab tayi murmushi tace sannu tsohuwa, murmushi tayi ahankali nake kallanta, kallan sani nake mata,hajia zaynab naji tace gaskiya kam nusaiba cikin nan naki yayi kasa sosai,kodai kin kusa haihuwa ne? ahankali ta zauna akan center carfet din tace wallahi hajia bansani kinsan bana zuwa asibiti, ringing wayan zain tayi,yana dagawa ya fice daga fallon yana khalid kana ina ne?hajia zaynab tace haba dai, gaskiya ga duk kan alamu wannan cikin naki haihuwa ko yau ko gobe ne,zaune suke sunata firansuMisalin karfe goma na dare nakuda ta kama nusaiba,haka hajia da driver suka kaita babban asibitin da ke sokoto gawon nama UDUTH,sai addu'a hajia zaynab keyi, misalin karfe goma sha biyu na dare ta sauka,ta haifi baby girl,haka likita yazo yagayawa hajia zaynab taji dadi sosai, misalin karfe takwas na safe aka sallame su suka dawo gida,cen na hango megidanta yana kokarin rufe gate din, cikin hanzari ya karaso gunsu,hajia zaynab dake dauke da babyn ta mika masa,ya rungume ta kamkam yana murna sosai,hajia zaynab tace toh mu karasa ciki koh,haka suka karasa cikin fallon gidan suke zaune akan center carfet,hajia zaynab ce zaune akan kujera sai kallan malam shehu take yana kallan 'yarda aka haifa masa,tayi murmushi tace idan dai ka bari zain ya shigo shikenan dan na tabbatar idan ya karbeta daga hannunka saika dinga rokonsa ya baka, dukansu dariya sukayi,hajia zaynab tace toh yanzu wane suna yakamata asa mata?kaman daga sama sukaji ance LAURAT, juyowa sukayi dukansu dan ganin ko wanene?bakowa bane face ZAIN ZAYYAN, hajia zaynab ta juyo tace uhmm malam shehu mekace? yayi murmushi yace LAURAT,ta maida dubanta zuwaga maijegon tace sunan ya maki,tace tunda zain dina yace Laurat ayyi angama magana,tunda suke maganar zain tsaye yake bayan mahaifiyarsa yana kallansu,hajia zaynab tace tau shikenan bukatar ka ta biya, yayi tsalle yace yes🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺
Ya zagayo ya karbi babyn hannun malam shehu ya zauna ya zuba mata na mazurunsa yana kallanta,next week friday akayi zanen sunan LAURAT SHEHU diyar da aka haifawa MALAM SHEHU maigadin gidansu ZAIN ZAYYAN,koda yaushe babyn tana hannun Zain,da anyi mata wanka tasha mamma toh fah ya dauketa sai kuma iya tagani,aiki kawai yake fita ba tare da ita ba ko shi dan hajia zaynab ta hanane,amma daya dawo daga office toh Nanny job din zai fara, mahaifiyar lauratu da mahaifinta kuwa ga baki daya sunajin dadin yanda Zain da mahaifiyarsa ke kula da laurat,idan ba gayamaka akayi ba cewa ba HAJIA ZAYNAB bace mahaifiyarta bazaka taba yadda ba saboda ita ke mata wanka,ta kuma feeding dinta da madara a feeding bottle,shekara daya kenan da zuwan lauratu duniya,duk wani gata na duniya babu wanda bata samu ba,gun HAJIA ZAYNAB , ZAIN,malam shehu da mahaifiyarta nusaiba 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
Ko fita hajia zaynab zatayi tare da laurat take zuwa, lauratu yarinya ce fara kyakkyawa,gata da gashi,ga hanci har baka dan karamin pink lips dinta kuwa sai ka rantse lipstick ake shafa mata,amma haka suke,zaune take ajikin hajia zaynab tana wasa,sai pictures hajia zaynab ke daukanta,Zain ya shigo cikin coat dinsa black ya dawo daga aiki kenan,da sallama abakinsa ya karaso fallon, laurat tana ganinsa ta fara tsalle tana mika masa hannu ya dauketa,sai wasa yake mata yana fadin my amour yana girgiza mata kai sai dariya take ,hajia zaynab tace ayyi shikenan yanzu tunda ta ganka bazata kara yadda da kowa ba, bata rufe baki ba sai Laurat ta fashe da kuka,harda dan guntun hawayenta,zain yana kallan ta yana turo mata dan karamin bakinsa kuka take mai hade da dariya, hajia zaynab ta mika masa ita,tace tau shikenan an huta😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂
Haka zain yake kula da laurat sosai,tanada shekara biyu aka yayeta daga shan mamma dama cen bai dameta ba, dressing dinta koda yaushe daya ne riga da sket pink color ko red,colors din nan biyu sune kayanda ake saka mata tun tana jaririya,duk zain ya fita sai ya siyo mata kaya,tanada shekara biyu zain ya fara koya mata arwala,idan zaiyi arwala buta biyu yake daukowa ita daya shi daya,haka zata zubda ruwan wurin wankin fuska,har sai ya gama yaja hannunta sun shiga gida sunyi sallah tare,tana da three years bakinta ya bude sosai,komai tana fadi,tana kiran HAJIA ZAYNAB da MUMMY , mahaifiyarta kuma mamma,mahaifinta kuma abbah,zain take kira da papa,kowa gidan da sunan da take masa👄👄👄👄👄👄
Laurat yanda kukasan diyan turawa haka take,zain baya mata hausa ko daga nan zuwa cen,idan kaji tayi hausa toh mahaifiyarta ce ko mahaifinta malam shehu,duk zamanta da zain,bai hana ta zama very close da mahaifiyarta ba nusaiba,wasa wasa zain ya sakata makaranta boko ta diyan manya, uniform dinta riga da wando ne masu kyau,sai dan karamin hijabin ta,da yar karamar jakanta,tare suke fita da safe da zain ya ajeta school sannan ya wuce office,idan ya taso ma haka yake,karfe hudu za'a shirya mata zuwa islamiya,shi yake kaita kuma yake daukota, laurat yarinya ce mai hazaka da ilimin addini dana boko,sai in baka gayamata kalma ba amma zata riketa yanda kukansa robot haka take,haka ya koya mata fadan sunansa cewarsa koda wani ya tambeta sunan papa dinta tace ZAIN ZAYYAN papa,tun bata iya kiran sunan yanda yakamata ba har sunan yabi bakinta,ta iya kiran sunan sosai sai ka rantse ita ta sakamashi sunan,idan dare yayi sukayi sallah sukaci abinci zai mata lesson na boko dana arbiya,haka suke ta rayuwar su gwanin ban sha'awa,tana da shekara hudu ya mata celebrating birthday dinta taji dadi sosai,zaune suke akan sallaya da shi da ita a harabar gidan ,suna game awayansa sai dariya take abunta, khalid ne ya shigo yace dama nasani,Zain da laurat lokaci daya suka dago kansu zuwa ga khalid, tayi murmushi tace yaya ina wuni?yace lafiya lau our angel,ya school?tace fine,sanye take cikin arabian gown red, gashin kanta har gadon baya, murmushi yayi suka gaisa da zain yace wallahi ina isa majalisa banganka ba nace kana cen tare da laurat,zain yayi murmushi yace my amour ta juyo yace jeki cikin gida gun mummy,ta mika masa wayansa ta saka yan tsiton takalmanta red ,tana gudu ta shiga cikin gida,zain sai runtse runtsen idanuwa yake yana gudun kada ta fadi,saboda bayasan kukanta ko daga nan zuwa cen,jini tsit dinta yasan cewa an sauka lafiya,nan fah ya mike suka fita tare da khalid amma badan yaso rabuwa da amour dinsa ba laurat❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Zaune yake a fallo misalin karfe hudu na marece, HAJIA ZAYNAB ta fita tare da laurat amour, system ce agabansa sai latse latsen sa yake,jin kawai yayi mutun akan gadon bayansa ba tare daya juya ba yace amour do you want to kill me?tana dariya tace no,hajia zaynab ta shigo fallon tace kin barni cen ina kiranki,dariya take cikin yar karamar muryarta tace wayo namaki,hajia zaynab tace wakika yiwa wayo?tace ke mana, mahaifiyarta ce tace sannun ku da zuwa hajia,hajia zaynab tace yawwa sannu maman laurat ya gidan?tace lafiya lau,cikin hanzari laurat ta saki zain ta nufi mahaifiyarta dake zaune,tace mamma ? mahaifiyarta tace na'am,tace zansha tea, mahaifiyarta tace yanzu?hajia zaynab ta ari bakinta tace gaskiya nima zansha, laurat tana murmushi tace bakince yara kawai ke shan tea ba?zain yace waya gayamaki?tace mummy ta gayaman,ayyi jiya a dakinta na kwana, cikin dare nasha tea,tana magana tana wasa da dan yatsanta,hajia zaynab ta mike tsaye tace uhmm nidai na shiga ciki, mahaifiyarta ta dauketa suka shiga kitchen din,zain yayi murmushi ya juya yaci gaba da aikinsa😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊
MRS NOOR'S NOVELS ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...