ZAIN ZAYYAN PART 2 PAGE 55&56

914 47 0
                                    

💕💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 22, October,2018

Wasa wasa zain ya fara neman laurat,yana zaune akan sallaya yana lazimi ya gama ya hada da addu'a,ya mike tsaye har ya zauna gefen gadon,Kara mikewa yayi ahankali ya nufi durowar kayansa wani dan karamin kit ya dauko kaman na kayan kwalliya ya dawo ya zauna tsakiyar gadon ya bude kit din,wani dan  karami box ne aciki,sai wasu takardu, ahankali ya dauko box din wata 'yar Teddy ce karama pink aciki yana budewa sai abun ya fara dadin i love you yana fitarta red light,yana rawa,idan ya rufe sai komai ya tsaya,takardun kuma duk shirme ne aciki, drawings ne anyi painting dinsu ga duk kan na wasan yara ne,haka ya maida hankalinsa ga baki daya akan teddy box din yanata open nd close, lokacin ne khalid ya shigo dakin, zain ko kadan baisan da shigowar khalid, gyaran murya yayi sannan yace well-done sir,sai lokacin hankalin zain ya dawo jikinsa,yace guy, khalid yace uhmmmm mekakeyi da kayan wasan yara?zain yayi murmushi yace first gift dinda my amour ta fara bani kenan tunda tayi wayo,nata color red ne, khalid yayi murmushi yace Allah sarki,kana nan kana tunanin matar wani,zain yace babu ruwanka, Aisha fah?sai lokacin khalid ya zauna yace kai bari wallahi ni banasan ta yanzu,na kamu da san wata amma mummy ta nunaman cewa there's no way zan kyale Aisha bayan angama komai,zain yayi ajiyan zuciya yace shiyasa kaga banasan rushing in life nafisan kayi komai akan kwanciyar hankali da natsuwa, khalid yace hakane wallahi amma nasan zata cenza💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

Khalid yana gida gaban mahaifiyarsa,zaune akan center carfet tace yawwa yau saura sati biyu a fara bikinka, what's your plan?ga baki daya komai ya dagule masa, cikin murya kasa-kasa yace mummy babu yanda za'ayi a daga maganar auren nan har gaba? tayi murmushi tace nasan meyasa kake san a daga auren, khalid kanasan Aisha nasani amma halayenta ne basu maka ba,cen farko sonta ya hana kaga illarta saida ka hadu da laurat,kayi hakuri zata cenza kaji koh?yace yaji,amma tayi hakuri yanasan yaje UK yaga laurat, tayi murmushi tace uhmm khalid mezaka mata,dan Allah ka barta tayi karatunta hankalin ta kwance itama nasan tanasan ka sosai,ko bakomai yaji dadin shedunda mummy tayi nacewa laurat tana son shi amma har yanzu ya ya kasa samun natsuwa,shi dai atunaninsa indai ba aure tayi ba toh tabbas ko bayan aurensa da Aisha koda da sati daya ne sai ya aureta🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Zain na hango fallo zaune da mahaifiyarsa,makale yake ajikinta kaman wani mage,kaman daga sama yaji tace tunda yanzu ka gama karatunka,kana da aiki,kuma you are now a grown up man,meze hana kazo ka nemi HANIFA sai.........ko aya bata kai ba ya zame jikinsa daga nata,yana kallanta da dara-daran idanuwansa, murmushi tayi tace menene zain?yace mummy wacce irin magana ce  wannan,wacce HANIFA?tace HANIFA nawa kasani,'yar uwarka mana,ya kara shigewa jikinta yace mummy wallahi LAURAT nakeso,dan Allah ki gayaman inda zanje na sameta, please mummy wallahi bazan iya rayuwa da ita hanifa ba ,cikin rawar murya yake magana, ahankali ta zamesa daga jikinta ranta abace,tace kana hauka ne,wacce laurat?inhar yanzu kana tunanin ka zauna da ita toh tun wuri ka cireta aranka, yarinyar da iyayenta basuda godiya,duk irin gatan da 'yarsu ta samu daga zuwa gida shikenan bako sanarwa, wallahi idan bakasan na bata maka rai tun wuri ka cireta daga zuciyarka,idan bakasan HANIFA kuma na baka daga nan  zuwa two weeks ka nemo matar da kakeso ka aura,renin wayon  banza sannan ta mike afusace ta bar fallon,zain ya hade hannayensa biyu ya bita da kallo harta shige dakinta, lokacin hanifa ta fito daga kitchen,tana smiling ta karaso gunsa har kasa ta sunkuya tace yaya inawuni, ahankali ya dago kansa ya dubeta ,wani dogon tsaki yaja mtswww tare da ficewa daga fallon,cike da mamakinsa ta mike tsaye jikinta a sanyaye tana tunanin ko laifin me ta masa?bayan fitarsa ya shiga motarsa ya fice daga gidan,bai taba shiga tashin hankali irin wannan ba,ga baki daya baya jin kansa daidai,ba gida ya wuce ba straight blue line ya wuce gidan giya kenan,

Haka ya siyo kwalaben giya ya dawo gida,yana dawowa yaci sa'a khalid baya nan,ya shiga dakinsa ya rufe,ya zauna gefen gado kuka yake kaman wani karamin yaro,ahaka ya farashan  kwalaben giyar,duk ya dora daya abaki sai ya shanye kab sannan ya aje kwalbar, idanuwansa sun rine sunyi jawur,haka yake shan giya tamkar yana shan ruwa,sai hawaye yake zubarwa😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠😠

Gun khalid kuwa haka ya dawo gidan, jikinsa shima a sanyaye,ya shiga dakinsa ya kwanta akan lafiyayyan gadonsa yana tunanin yanda rayuwarsa zata kasance idan ya auri Aisha, yayi dayasanin bari magaba su shiga maganarsu,sai yanzu yakejin yana gab da aikata babban kuskure arayuwarsa,sai yanzu yakejin cewa babu wanda yakai shi rashin sa'ar abokiyar rayuwa,yana cikin wannan tunanin wayansa ta soma ringing,yana dubawa sai yaga senorita cikin hanzari ya tashi zaune dama video call ne ta kira shi,ya bude durowar gadon da ke gefensa ya dauko earpieces ya saka a kunne sannan yayi accepting call din,tana murmushi yana kallanta yayi murmushi yace my SENORITA tace na'am yayana,kwance take akan gado,cikin kananun kaya riga da sket pink sai gashin kanta daya zubo har gadon baya,haka suka dinga fira,sai labari take bashi dariya kawai yake sosai ya manta duk wata damuwa tashi, yanasan mata maganar zain amma tunda mummy tace mashi laurat na sanshi ya kasa gayamata saboda gudun bacin ranta,sun kai misalin karfe biyu na dare suna fira,saida ta farajin bacci sannan sukayi saida safe, khalid ya kwanta sai gizo take masa,sosai yakesonta amma ya zama dole ya cireta aransa saboda bayada way out💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘ahaka bacci b'arawo ya sacesa 🤫🤫🤫🤫

Gun zain kuwa kab saida ya shanye kwalaben giyar duka,sai maye yake shi kadai acikin daki yana karawa,sai sunan LAURAT MY AMOUR yake kira,ahaka bacci ya daukesa yana rungume da rabin bottle din giyar😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥

Wasa wasa laurat ta fara shakuwa da fawad Ahmad,Koda yaushe suna tare,ta saki jiki da shi sosai,shi kuma yana mutuwar son ta amma ya kasa gayamata,haka suke fita strolling tare,zaune suke a MacDonald,garin ana sanyi sosai harda snow🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️🌨️zaune suke akan kujera mai table a tsakiya,sai fira suke da hot coffee agabansu,senorita sanye take cikin wata hadaddiyar English gown peach color,mai dogon hannu,rigan ta zauna jikinta sosai,sai rolling dinda tayi da black veil,sai jacket dinta pink data rataye akan wuyan kujera,fawad ma cikin kananun kayansa yake,rigarsa purple wandonsa baki,sai jacket dinsa baka,shima arataye take akan wuyan kujera,akwai mutane zaune awurin amma kowa abun gabansa yake ba ruwan wani da wani,sai fira suke,suna cikin firarsu yace mata senorita tace yes,yace kinada boyfriend kuwa? Wani matsakaicin murmushi tayi sannan tace yes,tun daga nan yasan babu shi babu laurat SENORITA, yayi bakin cikin hakan sosai,dole ya hakura suka zama friends kawai,haka ya komawa siyama, soyayya suke wadda ake kira soyayya,laurat taji dadin hakan sosai,

Siyama ce zaune agaban dressing mirror kan kujera, senorita na tsaye abayanta tana gyara mata gashin kanta,tsab ta shirya cikin wata prom gown red har kasa,tayi rolling da black veil,sai heels dinta 6inches red,komai red tayi , tayi kyau na fitar hankali sai kamshi yake,laurat tayi mata pictures, sannan suka fito tare,fallo suka tarar da fawad cikin coat dinsa white,komai white yayi,yana jin saukowarsu ya mike tsaye yana fadin wawwwww ma sha Allahu, lokacin suka karasa saukowa,ya mikawa siyama hannunsa,ta dora nata akai,wani mayen kallo yake yiwa laurat wanda ya nuna har yanzu akwai sauran sonta azuciyarsa, hankalinta ga baki daya yana kan siyama,sai pictures take musu,sai lokacin sukayi four eyes da fawad,tayi murmushi tace ku tafi kada kuyi late,siyama ta rungumeta,ta rakasu har waje,yau da wata hadaddiyar Land Rover yazo white,ya budewa siyama kofa ta shigo, yayi tsaye yana kallan senorita wadda ke waving siyama,sai lokacin ta ankara  yana kallanta,tayi maza ta mayarda kofar ta rufe sannan ta dawo cikin gida ta zauna a fallo..........

💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now