ZAIN ZAYYAN PART 1 PAGE 19 &20

1.2K 69 0
                                    

Dama kinsan hausawa kance "abun sawa adaki yafi daki wuya"tayi murmushi tace "in ba mugun damu ba meya kawo fura a zane"murmushi yayi yace lallai kin cika bahaushiya laure, murmushi tayi tace yaya khalid kenan,ayyi wannan bakomai bane,yace tau naji meyasa bakyasan hada ido da abokina ne?ta lumshe idanuwanta sannan tace bakomai,kawai nafi samun natsuwa idan ina tare dakai, yayi murmushi yace kin tabbata?tace sosai ma yaya,yace meyasa tau?tace banida yaya banida kanwa nikai nake kaga dole naso na samu yaya ko kanwa,yace hakane sha kuruminki am always there for you,tace really?yace yeah, tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace amma kash nan da wata shida zaka komawanka, khalid yayi murmushi yace kada kidamu i will visit you time to time, musamman idan zaki rubuta jamb dinki,zan kai ki birni kiyi registration ko bakya so? murmushi tayi tace inaso mana,yace.tau kada kidamu,zaune suke akan sallaya,cen gefe na hango taron samari da budare,suna wasan dandali,sai kidin kalanku ake masu suna rawa,suna waka,cen gefe na hango zain tsaye agefe tare da mairo,sai murmushi yake saboda wannan ne karo na farko daya taba ganin wasar dandali a fili,sai dai ya kalla a film din hausa,sai wulgi yake dana mazurunsa dama da hauni,yana neman khalid da laure, ahankali yace mairo?ta juyo tace na'am yace ina khalid, mairo tace uhmmmm ta duba dama da hauni bata gansa ba tace uhmmmm yana tare da laure, zain yayi ajiyan zuciya mai nauyi yace LAURAT, mairo tace eh,yace uhmmmm wai meyasa yakesan zama da ita ne? mairo tace uhmmmm bashi nake mamaki ba,ina mamakin yanda laure ta saki jiki da shine saboda tunda nake tare da laure bata taba tsayuwa da wani da'namiji ba ,ko kallo busu isheta ba,amma abun mamaki cikin kwana biyu ta sake da yaya khalid, zain yayi ajiyan zuciya mai nauyi yace uhmmmm KHALID kenan, mairo tace yawwa yanada aure kuwa? zain yace aaah bayada shi amma yanada matar da zai aura, mairo ta juyo tana kallan zain dana mazurunta tace dagaske?yace eh mana, mairo ta tabe baki tace Allah ya kyauta, sukaci gaba da kallan samarin da yan  matan da ke rawa, khalid da laure kuwa fira tayi dadi sai dariya suke , labari kawai khalid yake bata cikin harshen turanci,shi kuwa sai kallanta yake,a karamin birgesa take ba,gata karama amma sai ka rantse wata babbar macece idan kaji kalamanta, khalid yace shekarunki nawa?tana wasa da dan yatsanta tace uhmmm shekarana goma sha biyu,ido ya zaro yace be serious mana tace uhmmmm am 19years old,yace wawww anya kinyi su? tayi murmushi tace uhmm 20years fah zan shiga by may yanzu that's in the next three months,yace waww big girl kenan

Laure tayi murmushi tace yes ,yace Allah ya nuna mana,kin taba birthday?tace tab kaji yaya khalid bantaba ba,yace kin kusa kenan?tace aaah wazeman?yace ni mana, tayi murmushi tace uhmm ba wani,suna cikin firarsu,kaman daga sama sukaji ance sannun ku da aiki, ahankali khalid ya juyo yana murmushi yace my oga?zain yace uhmmmm ayyi kai ne oga, mairo ta dawo gefen laure tace hajia an tashi dandalin tashi muje koh?ko yanzu zain baiga fuskanta ba hijab ne taja har zuwa goshinta, ahankali ta daga kai tana murmushi tace uhmm angama?sunyi saurin gamawa yau, mairo tace ya za'ayi ki sani tunda kina nan kin maida yaya khalid abokinki,kin kyaleni, khalid ya mike tsaye yace oooh kishi kike ne? mairo ta tabe baki tace nidai nasan yanzu andaina sona,laure ta mike tsaye tare da dauke sallayar,ta linkafeta sannan suka jera suna tafiya, Zain sai kallansu yake,tana gaba tare da mairo,suna biye dasu abaya,suna kan hanyarsu mairo ta hango hanne,da sauri tasa hannu ta bangaje laure gefe,sai a hannun zain ta fadi, khalid ya juyo da karfi zai rikota sai yaganta ajikin zain, mairo tace yaya khalid ba tare da ta juyo ba,ya juyo yace na'am,tace ga hanne cen, ahankali yake kallanta tana tafiya tare da wani saurayi,yace itace hanne? mairo tace itace ba daga dandali ta fito ba daga dakinsa ta fito, khalid ya kara juyowa har lokacin zain yana rungume da laurat,ransa yaji yayi mugun baci, mairo sai gayamasa take amma hankalinsa ga baki daya baya kanta,gun lauratu kuwa hijabin ya hana zain yaga face dinta amma ahankali yake kallan dan karamin bakinta wanda ya kasance pink sai ka rantse ta shafa lip gloss,wani mugun motsi tayi wanda yasa zain da sauri ya dagata jikinsa,tsaye tayi agefe tare da sa hannu ta kara jan hijabin ta rufe fuskanta, cikin hanzari ta nufi gunsu khalid,tana isa tace mairo muje , mairo ta juyo tace bakiji ciwo ba,yi hakuri kawalliya hanne nagani shiyasa, laure tace kada kidamu muje, khalid yace yakamata ku isa gida yanzu, sukayi masu saida safe suka fice abunsu sauri sauri gudu gudu, shuru khalid yayi bai cewa zain alif ba,zain ma haka,haka suka taka zuwa gida, Koda sukaje ba wuta,zain ya tada masu generator, sannan suka shigewansu daki,babu wanda ya shiga fallon , sukayi wanka suka kwanta,duk khalid ya runtsa sai yaga laure da zain suna masa gizo,hakan yasa ya kasa runtsawa,aransa kuwa cewa yayi"meyasa nake kishin laure ne? Ina fatan ban fara sonta ba? meyasa nake jin zuciyata tana tafasa? tambayoyin da yake yiwa kansa kenan,sai juyi yake dama da hauni,

Zain kuwa bai taba jin dadi kaman na yau ba,bai taba samun natsuwa ba kaman yau,babu abunda yake masa kizo sai pink lips dinta banda smiling babu abunda yake,bakin cikinsa daya rashin ganin fuskarta da baiyi ba,amma bai taba ganin halitta kyakkyawa irin Laure ba,sai smiling yake,haka bacci yayi awon gaba da shi,yayi bacci yau cikin natsuwa da kwanciyar hankali, khalid kuwa kasa runtsawa yayi sai nisa yake yana karawa😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥

Kwance na hango Aisha cikin kananun kaya riga da sket,sket dinta mai wando ne aciki , iyakacinsa kneels dinta,sai wata yar karamar riga wadda ko al'aurar ta bata rufe ba,sai gashin kanta wanda tayi parking da ribbon pink kalar kayan jikinta a tsakiyar kai,sai kiran number take wadda tayiwa saving da sweetie,amma wayan not reachable,zaune ta tashi taci gaba da kiran number amma number bata shiga, safeeya ce ta fito cikin kayan bacci riga ce iyakacinta hips dinta blue,mai hannun shimi,sai yar karamar hularda ke kanta,ga duk kan alamu tayi bacci ta farka,sai hamma take,cen ta hango Aisha zaune tana latse latse awaya, ajiyan zuciya tayi sannan tace you are still awake? Aisha ta dago kanta tace yes dear, safeeya tace what's wrong? Aisha tace tun dazu nake kiran number khalid but not reachable, safeeya tace text him,am sure idan yayi receiving text din zai kiraki may b he too is trying to call you,nan take ta tura masa text kaman haka"hellow darling please call me when you receive this"ta tura kuma text din ya nuna mata yayi deliver,ta mike tsaye suka wuce daki tare da safeeya.........

Khalid na kwance har misalin karfe 3 na dare bai runtsa ba sai juyi yake,yana cikin hakan yaji wayansa tayi ringing ma'ana text ya shigo,yana dubawa sai yaga text daga wurin safeeya wadda yayiwa saving da wifey,zaune ya tashi,yayi mata replying text kaman haka"hey sofy how u? nd how's everything?the network is bad that's why i have been calling you but your number is not reachable,i miss you,ya tura mata text din,tare da jingina gadon bayansa da pillow kansa a sama yana kallan sillin,amma kash ya kasa runtsawa koda da second daya ne......

Gun laure kuwa,suna isa mairo ta wuce gida,ita kuma ta shiga gida,tuni inna larai tayi bacci,abbah kuma bai dawo ba sai sati na sama yana birni wurin aikinsa,laure ta shiga dakinta ta rufe tayi kwanciyar ta,itama kasa baccin tayi,sai tunanin ZAIN take, murmushi tayi tace uhmmm ooooh ni laure anya bansamu tabuwar hankali ba,ko wane namiji kallan kamanun ZAIN nake masa, wannan bakon ma haka,uhmm Allah gani gareka,banida wani gata sai naka,ka hadani da wannan bawan naka dan isarka da mallakarka, sannan tayi addu'a tayi kwanciyar ta da  tunanin ZAIN a zuciyarta,hanne kuwa ta jima bata dawo gida ba,tana shigowa taje ta dinga kwankwasawa laure kofa,cikin bacci takejin kwankwasar haka ta tashi da bacci a idanuwanta ta bude kofar dakin,hanne tace jeki rufe kofar gidan,laure tace tau,ta koma daki ta saka hijab dinta dama shi kadai ta cire,ta nufi kofar gidan,tana tsaye zata rufe  kofar taji anturota waje an banko kofar gidan da karfi,an saka sakata an rufe,zugum tayi saboda tasan ko ta kwankwasa ba wanda zai bude,ga garin tsit kowa ya shige,haka take zubarda hawaye zafafa,sai kallan dama da hauninta take, cikin hanzari ta nufi gidansu mairo tayita knocking ,amma taji shuru,tsaye tayi tana kuka,ta jima a kofar gidansu amma ba wanda ya bude,tayi zugum tana zubarda hawaye,ahaka ta koma kofar gidansu,ta cumuimuye guri daya kaman wata mage,kaman wata mayya,sai kuka take sosai kaman ranta zai fita 😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥

Bacci takeji sosai amma ta kasa saboda ga baki daya a tsorace take, ahaka bacci yayi halinsa ya saceta,kanta ajikin bango kofar gidan tana bacci,amma still hawaye take zubarwa 😥😥😥😥😥

Hanne kuwa tana aikata hakan,ta bushe da dariyar mugunta tace bakiga komai ba farawa ce,taya za'ayi ace duk karkarar nan ba wanda yayi kyawunki,da farin jinin ki, sannan kike tunanin zan barki ki huta, wallahi karya ne,duk yadda zanyi kibar garin nan sai nayi, matsiyaciya kawai,kowa sai yabonki yake,sai kace ke kadai ce  mace tagari,tsaki taja kaman zata cire harshenta,sannan ta shigewanta daki tayi kwanciyar ta hankali kwance,inna larai kuwa sai hansari take bata masan wainar da ake toyawa ba,amma ko tasani ba abunda zatayi hasalima sai dai ta goyi bayan yar'ta saboda itama kanta tana neman hanyar da zatasa laure tabar garin amma ta kasa,duk wurin malamin da taje amsa daya ce suke bata"ta rike ibada sosai dan haka komai za'ayi bazai kamata ba"babu wurin bokan da bataje ba amma amsar daya ce sai dai wasu suyita cin kudinta,ta gaji ta bari ,taci gaba da muzguna mata ta wannan hanyar🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄

MRS NOOR'S NOVELS 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now