ZAISUS LIFE WRITTERS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝 STORY WRITTEN 💗 BY 💗💗 MRS NOOR'S NOVELS ❤️ ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*******BIRNI*******
Bayan su siyama sun kai kayan akayi musu tarbo na musamman da zasu dawo kuma akayi musu goma na arziki yanda kukasan wadanda suka kai lefe,komai ya tafi akan tsari irin na manyan mutane,masu magana da kudi,suna dawowa,gida hajia nadiya tayi murmushi tace gaskiya kam amma ayyi suda keda biki agabansu ,daya daga cikin matan tace kedai hajia bari mai kudi yana yanda yaso, Allah dai ya kara rufamana asiri,dukansu suka amsa da ameen sannan suka hau fira ta daban,siyama na makale jikin hajia zaynab kaman wata mageKhalid yana shiga daki bandaki ya fada yayi wanka ya shirya cikin wata gizna brown,tayi kyau sosai, komai black yayi daga hula har zuwa wrist watch dinsa,tsaye yake agaban dressing mirror yana feshe jikinsa da turare murya kasa-kasa yace yakamata naje naga Aisha i miss her sosai,nan dai yacigaba da shirin nasa
Zain kuwa nan da bacci ya daukesa akan kujera anan muka kara tarar da shi yana baccinsa,kaman daga sama yayi wani dogon motsi tare da mika idanuwansa ya bude wadanda busu sauka ko ina ba sai kan agogon bangon da ke fallon,wanda ya nuna misalin karfe biyar,wani dogon tsaki yaja mtswwwww tare da mikewa tsaye ya shigewansa daki🤫🤫🤫🤫
****One week******
Sati daya kenan,akayi bikin yaron da aka haifawa khalid wanda yaci MUHAMMAD SAFWAN amma da SAFWAN zasu dinga kiransa,anyi biki na musamman tamkar bikin aure,kowa yaci yasha,daga lokacin khalid koda yaushe yana gidansu Aisha,zasu zauna a dakinta suyi fira ,suyi wasa da dariya,Koda yaushe yaje yaron yana makale ajikinsa,saidai yayi shuru yana kallansa,wayansa ce tayi ringing ahankali ya aje SAFWAN gefen gadon sannan ya saka hannu a aljihun sa ya dauko wayansa,Koda ya duba sai yaga mummy ce ke kiransa,yana daga suka gaisa tace maza ka sameni gida, yace okay,Aisha dake gefen gadon tana kallansa wani mayen murmushi ya sakammata sannan yace mummy ke kirana,tace okay tashi kaje koh?mikewa yayi tsaye ta zagayo tayi hugging nasa ya sumbaceta akan forehead nata sannan yasa kai ya fice,yana fita baj taka birki ko ina ba sai gidansu,komai bai kawo aransa ba,sai maganar FAWAD AHMAD wanda yake neman kanwarsa siyama,koda ya shiga gidan fallo ya hango hajia nadiya tsaye sai safa da marwa take ,siyama na gefe zaune kanta sunkuye akasa tana latse latse awaya, sallamar sa tasata tsayawa chak tare da juyowa,ta amsa masa sallamar sannan tace khalid ina LAURAT? gabansa ne yayi mugun faduwa cikin rashin fahimta yace kamanya mummy?tace kaman yanda kaji tambayar,yace tana gidanta mana,tace uhmm anya babu abunda yake faruwa da LAURAT ace tunda aka haihu bata kara zuwa duba jariri ba sannan ana neman wayanta akashe,nayi tunanin zatazo biki shima bikin shuru banganta ba,harda hajia zaynab taje bikin amma bataman maganar komai ba naso na tambeta amma na kasa, jikinsa yayi sanyi jin kalaman mahaifiyarsa,tuni yakai zaune saboda idan ya jima atsaye zai iya faduwa,bakomai yake tunawa ba sai karshen ganinta da yayi a hospital din da zai fita,Mummy ta katse masa tunanin sa ta hanyar nidai dan Allah kiraman ZAIN naji ko lafiya? cikin hanzari siyama tace ZAIN kuma?hajia nadiya ta juyo tana kallan ta tace eh lafiya?kai ta girgiza tace lafiya lau,zancen zuci tayi"ZAIN ?bashi bane senorita take nema ba kuwa?if i can remember clearly ta gayaman sunan saurayin ta ZAIN ZAYYAN,what is going on? mahaifiyarta ta katseta ta hanyar bakyajina ne? cikin hanzari ta d'ago kanta sama tana kallan mahaifiyarta da na mazurunta da suka tsaya chak kan na mahaifiyarta,hajia nadiya tace nace kin sameta kuwa?kai ta girgiza mata tace aaah not reachable,nan fah khalid ya kira zain amma bai daga ba,murya kasa-kasa yace inaga baya kusa bai daga wayan ba,tace uhmmm nidai gaskiya hankalina bai kwanta ba jin shuru haka
Kaman kada ta shiga theater room din nan ta fito gadai tanan, khalid yace wane theater room mummy?hajia nadiya tace ayyi itace ta karbi haihuwar Aisha lokacin da suke neman female doctor, khalid yace LAURAT?hajia nadiya tace kwarai ma kuwa,wani lumshe idanuwansa yayi tare da sunkuyar da kansa lokaci daya saboda ga baki daya yanzu sai yaga laurat batada laifi shi yakeda laifi,ga baki daya guilty concious ya kamashi,sai yaji ga baki daya ya tsani kansa,mikewa yayi tsaye yace bari naje gidan nagani,hajia nadiya tace yakamata sai ka dawo,nan ya fice daga gidan zuciyarsa tana tafarfasa kaman zata fito
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...