Saida akayi isha sannan khalid ya a shigo gidan, lauratu na kwance akan sofa da remote hannunta har bacci ya dauketa, murmushi yayi ya tsaya bayan sofar da take kwance yana kallanta,bai taba mata kallan tsabta ba sai yau, ahankali yake kallanta tun daga gashin kanta idanuwansa busu tsaya ko ina ba sai kan gadon fulaninta,wanda ya kasance rigan mai anine ce amma bata sakasu ba,hakan yasa rigan take nuna fararen gadon fulaninta tsab, murmushi yayi tare da lumshe idanuwansa da sauri ya dauke kansa daga gareta,ya nufi dinning,kula uku ce akai,karamar ya dauka yace uhmmmm tace wannan na baba ne bara nakai masa na dawo,ya fice daga cikin fallon yakaiwa baba abincinsa sai godiya yake masa, khalid ya dawo cikin gidan yasaka key,tare da kashe wutar mai haske ya kunna dim light red, sannan ya isa fallon ya zauna gefen kujerar da take kwance, ahankali ya karbi remote din hannunta wanda yasata yin mugun motsi,chak ya tsaya yana kallanta,ganin yanda take juye juye akan gadon yasa da sauri ya aje remote din ya dawo ya durkusa agabanta tare da tara hannayensa biyu,kaman yasan haka za'ayi,sai kan hannunsa ta fado,ya dauketa kaman wata baby, yakaita daki ya kwantar da ita akan lafiyayyan gadonta,tare da jawo silky bed sheet pink ya rufeta,ya kashe wutar dakin ya fito tare da jawo kofar dakin ya rufe, downstairs ya dawo ya nufi dinning hall,ya jawo kujera ya zauna, yayi serving kansa tuwon shinkafa da vegetable soups sai kamshi ke tashi,haka yaci abincinsa badan yaso haka ba,yau kadai da yaci abinci tare da ita har yayi kewanta yanzu,yaci abincinsa ya wanke hannunsa yasha ruwa ya dawo fallo ya zauna,yana zama wayansa tayi ringing yana dubawa sai yaga mumcy, mahaifiyarsa ce ke kiransa, smiling yayi sannan ya daga wayan tare da cewa hello my beautiful mum,dayan bangaren cikin muryar fada tace duk abinda kake ka barshi ka sameni agida yanzu kaji koh khalid?bata tsaya taji feedback dinsa ba ta kashe wayan,ajiyan zuciya yayi mai nauyi yace uhmmmm waya kaiwa hajia karata ne ba mamaki Aisha ce,yaja wani dogon tsaki ya shiga dakinsa ya saka jallabiya baka,ya fito,yana fitowa yace baba zanje gida hajia kesan ganina dan Allah ka kula da laurat,yace bakomai khalid sai ka dawo Allah ya tsare,ya fice abunsa,yana driving yana tunanin laurat,sai smiling yake abunsa,daidai gun wani katafaren gida yayi horn aka wangame masa gate din gidan ya karasa ciki sai parking space cen gefe ya hango motan Aisha a fake,kai ya girgiza yace nasan sai ita wallahi, sannan ya gyara fakin dinsa ya fito yana zuwa yayi knocking aka bude masa,yana shigowa wacce ta bude tace sannu da zuwa yaya tare da dan sunkuyawa,yace yawwa ina hajia ne?tace tana sama,ya haura sama cikin hanzari,yayi knocking kofar fallon sannan ya tura ya shiga,cen ya hango mahaifiyarsa HAJIA FATIMA cikin atamfa riga da zane,ta dora kafa daya akan daya da remote hannunta tana kallan aljazeera,sallama yayi ta amsa ba tare da ta juyo zuwa kansa ba,gefenta ya zauna yace ya hajiata,waya kawo karanane?tace ooooh wato kasan ma kayi laifi ,yace nasani mana,ina ganin kiranki nasan antashi, tayi murmushi tace halinka daya da mahaifinka,dama bakomai bane,i want know what is going on between you and Aisha?tazo taceman kwana biyu ta kasa gane kanka,yanzu haka she's inside together with SIYAMA i don't know what is going on, gayaman menene? khalid yayi murmushi yace you are my mum,so ina tunanin kinfi kowa sanin halina, sannan idan ban gayamaki ba then wazan gayawa,jin kalaman khalid yasa tasan da wani abu,ta shafa gefen fuskarsa tace gayaman koma menene,i know you very well, yayi gyaran murya, sannan yace kinsan naje wani kauye tare da zain,tace eh nasani,yace toh i met a lady called LAURATU,ya kwashe komai tun daga ranar haduwarsa da laurat zuwa yanzu da yake gabanta...............
Yace mum this is what is happening,amma kinsan i love Aisha sosai, murmushi tayi tace khalid you did the right thing amma zaman lauratu agidan daga kai sai ita yanada matsala sosai, saboda na uku dinku shaidan ne,banga laifin ka ba saboda rai ka ceta,nd am happy baka gayawa kowa ba saboda bakowa zai fahimci goal dinka ba,Amma idan bazaka damu ba mai zai hana ka maida lauratu nan gidan tare dani,kaga you are free to meet her duk lokacin da kakeso,Amma kasan yanzu mutane ake kiwo ba dabbobi ba, yayi shuru yana sauraren mahaifiyarsa,ganin yanda mood dinsa ya cenza nan take yasa ta dafa kafadarsa tace do this for the future sake ,this is Nigeria not United kingdom, yayi murmushi yace alright then mummy duk yanda kikace haka za'ayi no problem thank you,ni zan koma?tace aaaah khalid haba kodai you are interested in this girl ne,ban taba ganin mood dinka ya cenza ba kaman yau,ya kirkiro murmushi na karfin hali yace Allah mum am okay bakomai,nima nafisan haka,ya mike tsaye tace idan kaje ka kirani zanyi magana da ita?ko kuma gobe zanzo dakaina naganta,yace alright mum,har zai wuce tace bazaka shiga kaga Aisha ba?yace noo sauri nake ita kadai ce aciki gida, mahaifiyarsa tayi murmushi tace tau saida safe, sukayi saida safe ya fice abunsa, zuciyarsa tana tafarfasa sai jin yake kaman za'a rabashi da laurat ne har abada,ahaka ya shiga mota yana kukan zuci😥😥😥😥😥😥
Bayan fitarsa mahaifiyarsa tayi murmushi tace uhmm lallai akwai matsala babba, saboda ba karamin abu bane zaisa khalid ya shiga damuwa ba, what's so special about this girl? Ko shekara basuyi da haduwa ba ta dauke masa hankali,ga wadda sukayi 10years tare amma ta kasa controlling dinsa,koma wacece na tabbatar macece saboda duk wacce ta sace zuciyar khalid cikin yan kwana ki ba karamar arziki bace,zanje dakaina naganta, tayi murmushi taci gaba da kallanta😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
Khalid yana isa gida yayi parking ya jima zaune a mota yana tunanin yanda za'a rabashi da laurat,bayasan tayi nesa da shi,jinta yake tamkar wani bangare na jikinsa💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔gun laurat kuwa misalin karfe 10 ta falka daga baccinta, tayi mika tare da saukowa akan gadon, bandaki ta nufa tayi wanka ta shirya tsab cikin wasu lafiyayyun kayan bacci,riga ce doguwa har kasa marar nauyi pink,Mai hannun vest,sai ta saman wadda ta kasan mai dogon hannu,rigar ta mata kyau sosai,ta dauki novel dinda take karatu dazu bayan magrib ta fito,tana fitowa ta nufi dinning hall, plate din khalid ta gani wanda yaci abinci, tayi murmushi tace yaya khalid yaci abincinsa kenan,ta zauna itama taci nata saida ta koshi,ta kwashe komai takai kitchen,ta kashe wutar kitchen din ta dawo fallo ta zauna,tvn akashe ta dauki novel dinta tacigaba da karatunta sai smiling take abunta,kofar aka bude khalid ne ya shigo ,hankalinta ga baki daya yana kan novel din batasan da shigowar sa ba, yayi tsaye abayanta yana kallanta,kaman wacce aka ce ta juyo, ahankali ta dago kanta sama ido biyu sukayi da khalid smiling ya mata tare da jan dan dogon hancinta tace wassshhhhh ta maida kanta kasa tana murmushi tace ina kaje ne? gefenta ya zauna tare da aje car key akan center table yace naje wurin hajia ne, tayi murmushi tace suna lafiya?yace lafiya lau ,tace nagayamaki gobe zata zo? cikin nishadi tace dagaske?yace sosai ma,tace kace gobe zamuyi babbar bakuwa,abinda Aisha bata taba yi masa ba, Aisha ko firar yan gidansu bataso tafisan suyita firan soyayya, zancen da yake da zuciyarsa kenan, lauratu ta katsesa da wane time zatazo?yace in the afternoon,tace Allah ya kawota lafiya,yace ameen angel, mekike karatu?ta juya masa littafin yace AUREN DOLE kuma?tace eh the novel is very interesting yace koh?tace eh ko na karanta kaji?yace tau ina sauraren ki,haka ta dinga karanta masa littafin cikin zazzakar muryarta mai dadin sauraro,sai smiling yake,ga baki daya attention dinsa nakanta ba kan littafin ba😍😍😍😍😍😍😍😍😍
Misalin karfe goma sha biyu lauratu tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace yaya khalid yace na'am?tace bacci nakeji, yayi murmushi yace alright jeki kwanta gobe ma ida,tace okay,ta mike tsaye tace masa saida safe,sai yanzu ya kula da kayanda ke jikinta,wani mayen kallo ya mata,shima karan kansa yasan lauratu ba karamin haduwa tayi ba,haka ta haura sama ta shigewanta daki ta rufo kofar da key,tayi addu'a sannan tayi kwanciyar ta, khalid kuwa tuni yakai kwance akan sofa,kansa a sama yana tunanin kalaman hajiyarsa,sai juyi yake saboda ya kasa samun natsuwa 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
MRS NOOR'S NOVEL 👸 👸👸👸👸👸👸👸👸👸👸👸
👄👄👄👄👄👄👄👄👄
Mamanhanna2018❤️❤️❤️❤️❤️❤️

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...