💝💝💝💝💝💝 ZAISUS LIFE WRITTERS
WRITTEN
BY
MRS NOOR'S NOVELS 💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗
Isarsu kasuwar sukayi siyayya,kudin inna larai kuwa gyada kawai suka siya kwano biyu,mairo kuwa acikin kudin tallanta ta hada aka hadawa inna larai cefanan ta,suna fitowa kasuwa akan hanyarsu ta komawa gida,suna tafiya suna fira,kaman daga sama suka jiyo sallamu alaikum yan mata ji mana,mairo ce ta tsaya chak tare da juyowa tana murmushi tace lafiya kuwa malam? yayi murmushi yace lafiya lau,gefe lauratu ta koma tayi tsaye tare da basu bayanta,dan saurayin yayi ajiyan zuciya mai nauyi yace nidai sunana IBRAHIM ni dan maigarin kauyen nan ne ,dan Allah ko zakiman magana da kawarki, wallahi na kamu da sonta,mairo ta zaro na mazurunta tare da cewa so?yace sosai ma kuwa yar uwa so,tace tabdi lallai kai rayuwar ka tana cikin matsala,dan ga dukkan alamu ko lahira layin yan wuta zaka tsaya, ibrahim yace kamanya kenan?mairo tace kaga malam ni badani za'ayi wannan ba ka iya zuwa ka sameta din da kanka, ibrahim yace ayyi wannan ba matsala bane,yasa kai ya nufi gun lauratu data basu baya duk a tsawwale take,tana juyo sukayi ido hudu da ibrahim gabanta ne yayi mugun faduwa,hakan yasa ta zaro na mazurunta ta nunashi da dan yatsanta tace kai ne kuma?wai kai wane irin mutun ne marar zuciya, kullun sai ka biyoni ne,ka biyoni awurin sana'a ta sannan har kasuwan ma bina kakeyi, wallahi zan gayawa abbana idan baka daina bibiyana ba,wani dogon tsaki taja mtswww tare dasa kai ta fice ko jiran mairo batayi ba, ibrahim yayi tsaye yana kallan lauratu tana tafiya cikin hanzari,tako mairo tayi ta karaso gunsa dariya ta fashe da ita,ko dariyar ma maicin rai sosai, ibrahim ga baki daya kasa daukan kansa yayi, ahankali yake kallan kansa,sanye yake cikin shadda ruwan omo,sai yan faransin da ke sanye a kafafuwansa,katse dariyar mairo yayi da wai diyar wanene ita?mairo tace appp dama cen bakasan ko diyar waye ita ba?kuma kake bibiyanta, gaskiya malam bakada sa'a arayuwanka ni kaga tafiyana,ta fice abunta ta barshi a tsaye yana cizon dan yatsansa 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Mairo kuwa sai kwalawa lauratu kira take iya muryar da Allah ya mata,laure laure laure ki jirani mana,chak lauratu ta tsaya gindin wata bishiya ta koma ta zauna,ta aje ledar da ke hannunta,mairo tana karasowa gunta itama kasa takai ta zauna,shuru tayi , lauratu ta katse shurun da wallahi ibrahim dan gidan mai anguwa ya rainawa mutane wayo ina ni ina shi,kin ganshi kuwa?mairo ta tabe baki tace kina bani mamaki lauratu,kinga yanda yan matan karkarar nan kesan ibrahim kuwa,kab garin nan fah ba wanda yayi kyawunsa ga daukar wanka,ga kudi,ga kuma sarauta,kuma wani hanzari ba gudu ba namiji tilo gun mai anguwa,babu abunda ibrahim zai nema a karkarar nan ya rasa kema kinfi kowa sani,kuma ko tantama babu idan yaje ya sami abbah kingama auren ibrahim🙄🙄🙄🙄, lauratu tayi ajiyan zuciya tace kinyi gaskiya fah kawalliya,gashi abbah ya faraman maganar aure,mairo tace kingani koh? Kuma dai kinsan duk inda zaki wahala cen inna larai zata izaki,sai ta iza hanne inda zataji dadi,bata rufe baki ba,sai jin sukayi ance ooooooh aikin da inna ta maki kenan koh laure?a firgice lauratu ta mike tsaye jikinta har karkarwa take saboda ta tsorata,mairo ta mike tsaye tana kakkabar jikinta, ahankali tace kinga munafuka wuce zuwa inda zakije inba haka ba wallahi bakinki yayi jini,hanne ta karaso gindin bishiyar tana wani marmadi da idanuwa sama da kasa, ahankali ta dubi mairo tace bakinwa zaiyi jini?mairo tace naki mana, cikin hanzari lauratu ta riko hannun mairo cikin rawar murya tace muje kinji mairo?fizge hannunta tayi daga rikon da lauratu ta masa,ta matse jikin hanne kaman ta hadiyeta,hannu hanne tasa ta bangajeta da karfi saida takai kasa,tun daga kasan take fadin kan uba, wallahi yau sai naci ubanki,hanne tace ubanwa zakici?Nan fah suka kacame da fada sai kace kaji, cikin ikon Allah mairo takai hanne kasa sai naushi take kai Mata,lauratu kuwa sai kokarin dauketa daga ruwan cikin hanne amma ina ta kasa, tuni ta fashe da kuka, cikin muryar kuka tace mairo kin kaini kin baro,kinfi kowa sanin yau sai na yabawa aya zakinta, jikin mairo yayi sanyi,ta mike tsaye sai numfashi take mayarwa,hanne kuwa kwance take rairan akasa tana kuwa sai kace wadda akayiwa mutuwa, cikin tsawa mairo tace wallahi ko kimana shuru ko naci uwarki larai,shegiya ,tasa kafa ta shureta,tsit hanne tayi ,ta hade kanta da guwawunta sai kuka take🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣
Tuni lauratu takai kasa,tana lallashin hanne,mairo ta saka takalmanta ta dauki ledar,taja hannun lauratu suka wuce abunsu, lauratu shuru tayi saboda tasan yau karyarta ta kare,mairo tace ungo nidai tare da mikawa lauratu ledar, lauratu ta karba tana kallan mairo da ko ajikinta,ko alamun tsoro babu a fuskarta, lauratu tace mairo bance abunda kikayi bai kamata ba amma kinsan halin inna larai kada ta ciwa baba mutunci saboda wannan abun,mairo ta bushe da dariya harda sarkewa,tabi take da hannu tace wallahi da yawa na nunawa inna larai cewa uwa batafi uwa ba, saboda har ita sai na mata dukan tsiya kuma ba abunda zai faru, lauratu ta tabe baki , ahaka suka isa gidansu lauratu,inna larai tana daki kwance akan gadon karanta,tana sauraren fm 92.1 ,suka shiga dakin tare da sallama,cen bakin kofa mairo ta tsaya tana gaida inna larai fuskanta a daure, jikin lauratu har rawa yake,ta nunawa inna larai duk cefanan komai ta siyo, saboda dadi ya kasheta da mari tace laure babu canji? mairo ta amsa tambayar da akwai shi amma mun hadu da hanne akan hanya tace kince a bata,inna larai tace ita hannen da kanta? mairo tace appp ita mana,inna larai tace Allah ya kyauta zata zo ta sameni,laure dauki kayan kije ki dora sanwar girkin dare, lauratu ta hada kayan ta mayar leda sannan ta fito,a tsakiyar gidan suka zauna,sukayi gyaran kayan miya da alayyahu,tunda suka fara babu wanda yacewa wani alif, mairo kuwa sai wakar dandali take rerawa abunta😂😂😂😂😂😂
Haka sukayi tuwon shinkafa da miyan allayahu ,sukayi wanke wanke da sharar gidan,zaune suke a shigifar gidan zaune akan tabarma suna firansu,hanne ce ta shigo fuskanta a daure,tana shigowa taci karo dasu zaune,harara ta banka masu,zata wuce mairo ta riko kafanta tajata da karfi saida takai kasa, lauratu saida ta lumshe idanuwanta irin yanda hanne ta fadi dipppp,da karfi hanne ta juyo zatayi magana,mairo tace appp Allah da kinyi magana sai na tona maki asiri gun inna larai da baba ,kinsan dai nasan inda kike zuwa da sunan dandali koh?atsorace hanne tace me kuma nace maki yanzu?mairo tace oho dai, wallahi ko kallan banza kika karayiwa laure sai kingane kurenki, sannan komai inna larai tace maki kice kawai hakane,kuma idan na kara zuwa naga laure tana aikin gida,shima kin shiga......sai tayi shuru ta juyo tace laure me sunan wannan abun ma da wannan dan bautar kasan ke cewa?laure tace "CASE" mairo tace yawwa shi fah,kinji dai da kunnenki koh?hanne tace eh naji,ta mike tsaye ta ficewanta cikin gida da karfi kaman wacce iska ya turo😅😅😅😅😅😅😅😅😅😅😅😅😅😅😅
MRS NOOR'S NOVELS 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...