ZAISUS LIFE WRITTERS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝 WRITTEN
BY
MRS NOOR'S NOVELS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝Tunda ta tashi sallah subahin bata kara komawa bacci ba,aikin gidan take,ko ina tsab,ta debo ruwa,tacika komai na ruwa agidan,har karin kumallo tayi koko ne,awaje taje ta siyo kosai gun baba talatu, misalin karfe bakwai da rabi inna larai ta fito sai mika take tana hamma,ko sallah subahin batayi ba,dan haka ko maganar hanne ba'ayi wadda ko musu bazanyi ba yanzu ta gyara kwanciyarta,har kasa laure takai ta gaida inna larai,fuska a daure tace kinga ni ba wannan ba,kin dama kokon kuwa?laure tace eh nadama har kosai na siyo,inna larai tace toh yayi kyau,tasa kai ta koma dakinta,cen na hango hanne sai sharar baccinta take,komawa inna larai tayi akan tabarma tayi kwanciyar ta😁😁😁😁😁😁😁😁
Tsab laure ta shirya cikin kayan makarantar boko cikin wasu riga da wando ruwan omo,hijabin ne fari har kasa mai hannu, kafanta kuwa sandals ne duk sunbi sun tsufa duk faci ne dasu,bako safa a kafafuwanta,wata azababbiyar yunwa takeji kuma tanajin tsoron dibar kokon kada inna larai ta hanata zuwa makaranta,haka ta hakura ta dauki jakanta ta leda ta fice zuwa makaranta,tana fitowa taci karo da mahaifinta malam shehu,har kasa takai ta gaida shi, murmushi yayi yace har anfito kenan?tace eh baba,yace toh Allah ya bada sa'a sai andawo koh?ta mike tsaye tace Allah yasa abbah, sannan tasa kai ta fice abunta kanta akasa take tafiya kaman batasan taka kasa,kallo daya idan ka mata kasan kyakkyawa ce wahala ta maida ita haka🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄
❤️❤️ MRS NOOR'S NOVELS ❤️❤️
Zain kana bani mamaki wallahi,kamanya bazakaje kauye ba?akanka farau ko karau,kaga dan Allah kaje mana,cigabane fah ,duka duka 6month ne zakayi ka dawo haba Zain? khalid ne tsaye ajikin wata mercendenz Benz baka,zain na gefen shi ya nade hannayensa biyu,kansa a kasa, ajiyan zuciya yayi sannan ya dago kansa sama ya dubi khalid yace haba man village ne fah,ga sauro,ga ruwan garin ko shawu basayi bare ace suyi wanka,ko kamanta da typhoid ne? Khalid yayi murmushi yace amma kuma kada kamanta cewa taimako ne zakayi,akwai dubunka masu son irin wannan aikin busu samu ba kai kuma kasamu but you are trying to play smart, alright then good for you,zain yayi shuru yana nazari,sai cen yace alright then naji but yaushe zamu fara zuwa naga yanayin garin first? Khalid yace uhmmmm let it be tomorrow,i think it will be better,zain yace okay then,muje daf kem am kind of hungry, khalid yace okay,mota suka shiga khalid ke driving ,zain na zaune agefen mai zaman banza sai charting yake🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄Isar lauratu dede gun wata makaranta,duk dalibai suna waje sai wasa suke,ko wacce kwana da nata group mata ne da maza,duka uniform din iri daya ne dana lauratu,sai dai mazan harda hula ce dasu fara,daka gansu kasan suna cikin wahala,wani ga baki daya kayan jikinsa ko kalluwa basayi,wani kuma duk faci ne ajikin uniform din,wasun su kuwa ko wanka busuyi ba,tana isa makarantar aji ta shiga,matasa matane zaune a ajin zaune sai surutu suke,cen dayan bangaren kuwa duk layin maza ne,suma surutun suke,cen bayan layin matan kujerar karshe ta koma ta zauna ita kadai ta aje ledar littattafan ta ,ta zuba wani uban tagumi sai kallan sauran daliban take ta window daketa wasan su, tunda ta shigo yan matan da ke gabanta zaune suke mata kallan banza Lauratu kuwa babu wacce ta tankawa cikin su,ajin ba wani babba bane,dauke yake da kujerun makaranta wadanda bazasu wuce kwara ashirin ba acikin ajin,sai bakin allo dake manne ajikin ginar ajin,daga ganin makarantar kasan bazatafi shekara uku zuwa hudu da budewa ba,haka classes din nasu suke, saboda cikar ajin wasu har a kasa suke zama, shiyasa suke saurin zuwa saboda su samu wurin zama,cen na hango mairo tafe bakomai ahanunta sai wani dan karamin kwano na tuwon miya akanta da wata karamar bulala ta dogon yaro hannunta,sai wasa take da ita, uniform dinsu iri daya dana Lauratu,sai dai nata sunfi zama sababi sosai,tayi kwalliyarta mai kyau,tana shigowa ajin yan matan da ke zaune akan tabur suka koma kan kujerunsu suka zauna tsit fah gefen mata yayi shigowar mairo,tsaye take ajikin kofar ajin,sai harara take watso musu,babu wacce ta tanka mata, ahankali take tafiya duk kujerar da tabi sai ta tsaya ta kallace matan da ke zaune akujeran, bangaren mazan kuwa shuru suma sukayi suna kallan iko irin na mairo,mairo bala'in birgesu take saboda bata daukan raini ko wulakanci gun kowa kab garin babu wanda bayada labarin mairo saboda batada kirki idan aka tabata ko kawalliya dinta lauratu,dede tabur din lauratu dakai,tana murmushi tace kawalliya ?shuru taji lauratu data zuba wannan uban tagumin ga duk kan alamu tana duniyar masu tunani,dafa kafadarta tayi wadda tasa ta dago afirgice, narainarai tayi dana mazurunta tana kallan mairo wacce ke tsaye tana kallanta , murmushi tayi tace kawalliya ina kwana?mairo ta tabe baki ta zauna sannan tace me haka kuma?me aka maki ne? Hanne takai kararki ne gun inna larai?shuru lauratu tayi tana sauranta,mairo tace appp lallai watan cin uban hanne ya tsaya yau, cikin hanzari Lauratu tace Kinga fah wallahi ko daya babu,yunwa nakeji wallahi sosai,mairo tayi murmushi tace amma fah ta kuru yau,dama nasan bazaki samu cin abinci da safen nan ba kuma nasan ke kikayi karin kumallo amma saboda tsabagen tsoro irin naki yasa baki sha ba,kwanon da ke gabanta ta turamata agabanta tace ungo nidai dimamene,kici kamin malamin ya shigo.
Ahankali lauratu ta bude langar jikinta har rawa yake, dimamen tuwon dawa ne da miyar kubewa sai kamshin man shanu dake tashi,mikewa tayi tsaye ta dauki langar ta fito daga ajin,guri ta samu ta tsugunna gindin bishiya ta bude tanaci , jikinta rawa yake sosai saboda tsabagen yunwar da takeji, ba'a dauki wani dogon lokaci ba,ta gaba kab,ta nufi rijiya ta saka guga ta debo ruwan tasha sannan ta wanke hannunta,sai lokacin taji kanta daidai,ta wanke langar ta dawo ajin,har lokacin malami bai shigo ba, ta koma ta zauna ahankali mairo tace kin koshi? lauratu tayi murmushi tace eh mairo nagode,baki mairo ta tabe tace dame Kuma nifah banasan haka, lauratu tace na daina,fira suke abunsu, ajiyan zuciya lauratu tayi sannan tace mairo? ahankali mairo tace na'am laure, lauratu tace wallahi ko jiya nayi mafalkin wannan da nake baki labari,mairo tace kuma? lauratu tace Allah ,Kuma jiya yagayaman sunansa,mairo ta zaro na mazurunta tare da dafe kirji tace a mafalkin?da karfi saida duk suka jiyo suna kallanta, harara ta banka masu sannan tace kaga zuri'ar munafukai menene da kuka wani juyowa kuna kallona daku nake ne?da sauri suka juya babu wanda yace da ita alif,ta juyo tace laure da wasa kike? lauratu ta girgiza kai tace Allah dagaske nake,mairo tace me sunan nashi? lauratu tayi shuru alamun mai nazari sai cen tace ZAIN ZAYYAN,na mazurunta ta fiddo tace ZAIN ZAYYAN sunan mutun ne kuwa? lauratu tayi murmushi tace Allah ni shi yagayaman da kansa,mairo tace tab anya laure bakida mutanen boye kuwa?taya zaki fada tarkon son wanda baki taba gani ba, sunansa ma baiyi kama da sunan mutane ba,suna sai kace na sarkin aljannu 🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉🙉 sannan kiceman mutun ne, lauratu tayi murmushi tace kai mairo Allah mutun ne!!!!! Amma bantaba ganin kyakkyawar halitta irin tasa ba,mairo tace appp taya kuwa zaki ganta,kinyi gamo da aljani,shin tsaya ma wai a ina ne kuke haduwa a mafalkin? lauratu tayi murmushi tace kedai bari abun ba'a cewa komai saboda wani lambu ne na masoya,wurin zagaye yake da abubuwa daban daban kamansu bishiyar gwaiba,mangwaro,ayaba,da fulawowi masu kyau da kamshi,shuru mairo tayi ta tattara hankalinta ga baki daya zuwa gareta ga baki daya lauratu hankalin ta ya fita jikinta,magana take amma sai murmushi take tana kara lumshe idanuwanta 😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎
MRS NOOR'S NOVELS 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Novela JuvenilFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...