ZAIN ZAYYAN PART1 PAGE 49&50

1.4K 67 2
                                    

💕💕💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

Bangaren khalid da zain kuwa haka zain yake takurawa khalid akan yaje yaga ibrahim d'an mai anguwa amma ina yace shi ba inda zashi,haka zain ya hakura da zancen,akaci gaba da aikin da ya kawosu,wasa wasa aka gama gina hospital din,aka sa masa abubuwan aiki sosai,harda ma'aikata aka dauko mata da maza,aka saka magunguna,zain, khalid da mai anguwa da sauran mukarrabansa ne zaune a fada,mai anguwa sai godiya yake kara yiwa su zain da khalid yana sa musu albarka,kowa wurin sai ameen suke cewa,gyaran murya mai anguwa yayi yace toh gashi angama komai amma ba'a sawa asibitin suna ba,zain yayi saurin daga kansa sama yace rankashidade gobe za'a kawo sunan sai a laka,mai anguwa yace Allah sarki gaskiya da naso ace sunan asibitin ya kasance dauke da sunan lauratu, khalid yayi murmushi yace gaskiya haka ya dace ba matsala rankashidade za'ayi,

Washe gari misalin karfe goma na safe aka kawo sign board din sunan asibitin,kaman yanda suke a fada jiya haka suke tsaye gaban asibitin aka laka sign board din,rufe yake da farin kyalle saida aka gama saka shi sannan zain ya bude sign board din , ahankali khalid yake karantawa na mazurunsa a waje"LAURAT AMOUR HOSPITAL"da address din da komai,mai anguwa yayi shuru yana kallan sign board din ahankali,cen sai yace toh kai zan(Zain) menene arubuce?zain yayi murmushi yace rankashidade sunan lauratu ne arubuce,gabaki daya sunji dadin hakan sosai,haka suka koma fada sunata firan abun,tunda suka baro wurin khalid ya kasa ko wani dogon motsi🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫

Bayan sun koma gida, sukayi wanka suka shirya ga baki dayansu cikin kananun kaya riga da wando blue, komai iri daya ne,mairo ta kawo musu abinci shinkafa da miya sukaci,tana zaune a fallo suna fira,suna gama firan tace ita zata wuce, khalid yace kamata tayi ta zagaya dasu garin mana, saboda yanzu wata uku kawai suka rage masu,haka akayi kuwa,mairo tana gaba suna biye da ita abaya,duk inda suke da tambaya, khalid zai mata tambayar cikin harshen turanci,wata amsar ta bashi cikin harshen hausa wata kuwa turanci,haka suka zagaye garin da yake garin karamin gari ne kowa yasan kowa,duk inda suka wuce sai kallan su ake,sai nuna mairo suke, mairo kuwa harara kawai take binsu da ita,wasu dasun ganta sai su cenza hanya,zain duk yana kulle da hakan,saida suka dawo suka koma karkashin bishiyar da suke zama before lokacin da laure tana nan,zain yace mairo meyasa ake tsoronki?kaman daga sama taji tambayar,ta juyo tana murmushi tace ya akayi ka gane?sai yace wasu dasun ganki sai su dinga kame kame,wasu kuma sai su cenza hanya,mairo tace tab kasan bana raga musu saboda kawalliya dita laure, yayi murmushi yace yana kyau haka, khalid dai babu uhmmm bare hmmm, shuru yayi yana kallan su,shi ga baki daya yayi kewan laurat yau,jin kasan yake kaman bashi ba,sai kokarin son ya tuna WACECCE LAURAT AMOUR ?haka suka sha firansu mairo da zain, khalid sai dai kawai yayi smiling shikenan,bayan sun raka mairo gida suka fice zuwa gida,suna zaune a sitting room, khalid yana kwance rungume da wayansa sai kallan wani hoto yake, ahankali na cusa kaina dan naga hoton wacece?ina dubawa sai naga laurat cikin arabian dress black,tayi rolling sai ka rantse wata balarabiya ce,tayi kyau harta gaji,zain yana gefe sai kokarin hada details din aikin yake akan computer sa, khalid ya saukar da nauyayyen numfashin sa sannan yace zain?ba tare da ya juyo ba yace yes, khalid yace wacece menene ma'anar abinda ka rubuta akan sign board din hospital ?sai lokacin ya dago kansa ya dubi khalid yayi murmushi yace kana nufin har ka manta da MY AMOUR? khalid yace your amour kuma?budurwa ka taba yine bare nasan sunan?zain yayi murmushi yace amma ka bani mamaki,zaka manta yar chuchu dinda aka haifa gidanmu some years back,wadda kake kira da angel,sai lokacin khalid ya tashi zaune yace ooooooh Allah sarki wallahi har na mantata,wai har yanzu tana ranka?zain yace har gobe kuwa ba mamaki yanzu tayi aure ta manta dani ga baki daya, khalid yace uhmmmm meze hana kaje nemanta,Anya zata iya mantawa dakai?zain yayi murmushi yace ina zanje nemanta tunda bansan 'yan wane gari bane,ko mahaifinta naji labarin ance yana sokoto yana aiki amma bansan inda yake aiki ba, khalid yace ba damuwa idan muka koma zamuyi maganar,zain yayi murmushi yace alright then amma ayyi bazan iya manta amour ba, shiyasa kaga lokacin da naji sunan lauratu naso naga face dinta amma ina bansamu gani ba!!!!! khalid yace baka taba ganin laurat bane?zain yace koda wasa kuwa, cikin zumudi yace ga.......bai iyar da maganar sa ba,aransa yace "Kai bazan gayamaka ba yanzu saboda bakasan cewa she's with me ba sai mun koma tukunna"Zain yace ina? khalid yayi murmushi yace ina nufin gata gaka lokacin kaceman baka ganta ba?zain yace Allah bansan taba, khalid yace Allah sarki, anyway no problem 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now