💔💔💔💔💔💔 MRS NOOR'S NOVELS 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔 vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
Isar Khalid da siyama hospital din keda wuya, yayi parking ya fito har lokacin siyama na zaune a mota, ahankali ya tsaya chak yana kallanta ga baki daya hankalinta baya jikinta, dawowa yayi ya bude kofar ya sunkuyar da kansa cikin motar yace siyama? afirgice ta juyo tace na'am yaya, yace fito mana,haka ta fito jikinta a sanyaye,yana gaba tana biye da shi abaya,sai zancen zuci take"tab ni siyama ya zanyi wallahi i can't pretend anymore,yaya khalid will kill me today"haka suka karasa cikin hospital din,suna kan corridor din shiga dakin senorita,taji ankira sunanta kaman wacce ke jiran akirata,ta juya da karfi,wata baturiya ce ta kirata,siyama tace yaya jeka kawai am coming,ya juyo yace alright sai kin shigo,haka ya karasa,ita kuwa ta isa gun wacce ke kiranta suna tafiya suna firan,sai yanzu tadan samu sakaci before ya kwala mata kira,dan tasan ita zai fara kira before kowa🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
Khalid kuwa yana isa kofar dakin senorita,yayi knocking tare da tura kofar ya shiga,yana shiga yaga wayam,ya zauna gefen gadon, atunaninsa tana bandaki,yafi 30minute zaune adakin,amma ko motsin ruwa bayaji,yana mikewa tsaye aka shigo dakin,ya juyo nurse clara ce ta shigo dakin dauke da faranti mai tea cup da drugs akai,bayan sun gaisa ta tambe shi laurat?yace shima kansa ita yake jira atunaninsa tana bandaki amma yafi 30minute zaune ko motsin ruwa bayaji, nurse clara ta aje farantin akan center table dinda ke gefe tace ita kuma tunaninta yazo ya fita da ita shan iska, cikin rashin fahimta yace bai gane ba?tace ta shigo dazu amma bataga kowa adakin ba, bandakin ma bakowa,so ta dauka tare suka fita,yace what?are you kidding me? cikin harshen turanci sukayi maganar, cikin hanzari ya fice daga dakin tare da bangaje clara,haka yake bin lungu da sakon hospital din yana kiran senorita,mutanen hospital din sai kallansa suke, wasu sun dauka bayada hankali, saboda ga baki daya a hargitse yake,haka yakai guwawunsa kasa yana kuka sosai kaman wani karamin yaro 😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥
Nurse clara da sauran nurse's din mata da maza sukayo kansa,sai hakuri suke basa,haka suka daga shi zuwa offishin Dr babbansu kenan,suna zuwa suka masa bayanin komai,yace dr senorita?sukace masa eh,kuma tabbas shi ne yayi treating dinta,ya mike tsaye tare da basu umurnin cewa aduba masa each and every CCTV camera ta hospital din nan ga baki daya, sannan aka masa ID dinta,haka fah aka fara aikin neman LAURAT ruwa ajallo,duk hospital din ya dauka kowa sai mamakin hakan yake,babu wanda yaji dadin abun,aiki kawai ake gadan gadan🙋🙋🙋🙋🙋🙋
Gun siyama kuwa karkashin bishiya suka zauna tare da kawarta,suna cikin firarsu take tambyarta senorita?tace mata tana ciki batada lafiya itama,haka suka mike da sunan zata dubota, siyama kuwa tuni tasha toka kaman batasan komai ba,ganin yanda hospital din ya dauki shuru aka hana gudanar da ko wane aiki, yasa baturiyar take tambyar siyama lafiya kuwa? siyama ta tabe baki tace Allah batasani ba,haka suka isa dakin laurat wayam, suna fitowa sukaci karo da nurse clara dama cen tasan siyama nan take yiwa siyama bayanin komai,siyama tace what?nan fah itama ta hau nata kukan da tsalle tana karawa,da kyar suka lallasheta,itama inda suka kai khalid cen suka kaita, cikin magiya tace Yaya ka nema man laurat bazan iya zama bada ita ba, Dan Allah, tausayin kanwarsa ya kamasa sosai,hakan yasa ya rungumota jikinsa kamkam yana lallashinta,shima karan kansa zubarda hawaye yake🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭🤭
Laurat ce zaune akan sofa,ta dora kafa daya akan daya,wayanta ce hannunta tana kiran wata number da tayiwa saving da siyyy baby,siyama kenan,amma tana ringing ba'a picking,tayi mata kira yakai biyar amma no answer,haka ta hakura,ta shiga yanar gizo Facebook,tana shiga ta tarar da friend request daga mutane daban daban, ahankali take scrolling through request din,bata tsaya ko ina ba sai kan wanda yake dauke da "DON ZAIN"chak ta tsaya tana nanata sunan kasa-kasa, profile din ta shiga taga komai nasa United kingdom ne,ta lumshe idanuwanta tace uhmmmm bansan meyasa ba but anya wannan ba ZAIN bane?haka dai taja dan guntun tsaki ta fita yanar gizon ga baki daya ba tare da tayi accepting friend request na kowa ba🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫
Gefen su mai anguwa da iro kuwa,tuni iro ya samu sauki,har yana iya mikewa tsaye da kansa,ba tare da taimakon kowa ba,dama cen a hospital din aka masu komai, khalid ya hadasu da wani abokinsa da zai dawo Nigeria ya dawo dasu,da sassafe yasa driver yakaisu har garin nasu,horo birni kam ba'a cewa komai sai zuwan ganin iro ake,mai anguwa yana gefensa zaune sai murmushi yake,sai cewa ake iro ya zama bature saboda yayi haske yayi jiki,ya kara kyau,bayan kowa ya watse mai anguwa yace toh iro wannan kadai ya ishaka wa'azi,kaga dai yanda rayuwa take,duk wanda yayi dakyau zaiga da kyau,amma koda wasa kada naji kada kuma nagani ka gayawa kowa cewa laure ce ta maka wannan aikin,idan lokacin sani yayi kowa zai samu labarin haka,iro yace in sha Allahu baba,yace sannan yanzu ka gayaman wacece kake so duk fadin garin nan,hakan ba karamin dadi yayiwa iro ba, cikin zumudi yace laure,mai anguwa yayi wata yar bazawarar dariya yace ayyi ka makaro saidai wata kam badai laure ba,iro cikin rashin fahimta yake kallan mahaifinsa,mai anguwa yayi murmushi yace uhmm na baka nan da sati biyu,ka gayaman wacce kake so, cikin sanyin jiki iro yace tau, sannan ya fice daga dakin😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔
Gun mahaifin laure kuwa,ayyi ranar da yabar gidan mai anguwa ya koma gidansa,yana zuwa larai tana zaune a tsakiyar gidan tana wakar ta tanacin gyada,ya shiga bakinsa dauke da sallama, cikin renin hankali tace daga ina ba tare da ta d'ago kai ta dubesa ba,chak ya tsaya ya kare mata kallan tsabta sannan yace daga gidan ubanki, cikin razana ta d'ago kanta ta dafe kirji tace ubana MAMMAN?yace idan akwai wani agefe harda shi,mikewa tayi tsaye zatayo cikinsa yace kinga dakata tare da daga mata hannu yace maza ki kwashe naki da naki ki bar gidan nan,ki dauki agolar diyarki kubarman gida na sakeki saki biyu,chak ta tsaya tana kallansa,wata bazawarar dariya tayi tuni ta cire dankwalinta tasha damara,tana tsalle tana karawa tace wallahi karya kake shehu,munafuki, cikin muryar kuka tace wallahi ban saku ba,nan yabarta tsaye ya shigewansa dakinsa tare da rufe kofar dakin🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆haka fah larai ta aza hannu akai tanata kuwa tana karawa sai kiran makwabta take😲😲😲😲😲😲
MRS NOOR'S NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
Ya take ne?
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...